Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 25 of 81

NA
*AUTAR MANYA*

_Albishirinku iyayen yara dama yaran baki ɗaya, shin ko kinsan shararriyar tashar nan ta youtube mai suna *Abdur-rahman* ta shirya tsaf domin baku gudunmawa wajan tayaku bitar karatun ƴaƴanku cikin sauƙi?, Kai dai/ kedai maza garzaya wannan shararriyar channel ɗin domin ki dannawa yaranki dansu karu da zazzaƙar ƙira'ar da *Abdur-rahma* ke gudanarwa wajan bitar karatun alkur'ani mai girma acikinta daman sauran littattafan addinin islama kada ki manta da danna *SUBSCRIBE* tare da ƙararrawar sanarwa mungode_
https://youtu.be/PFTnz8JGFfQ

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*35&36*

Seda ta juyo domin nufar hanyar kicin sannan ta lura Cak ta tsaya ganin namiji zaune akan tabarma wanda yaketa zubawa mama surutu ita kuma maman tana biye masa mitstsike idanunta tai domin ta kuma tantance waye acikin danginsu sedai kuma duk hasashenta tagaza gane kowa ye shi sabida wannan shi daga gani É—an gayune kuma yana da kuÉ—i, to ina mama tasami wannan guy É—in? sanin babu mai bata amsa ga kuma mama sam taga hankalinta baya kanta hakama shiÉ—in yasa taja kafafunta zuwa gaban murhun da mama ke kokarin sauke tukunyar dambun daga kanshi.
Tundaga fitowarta har dauraye fuskarta har zuwa gaban mama data nufa duk Aliyu yana kallonta ta witsiyar idanunshi sedai miskilin ko arzikin ɗagowa ya dubi wace bata samu ba sema ƙasa dayay da kanshi sosai sabida mugun ganin dayaywa cikakkun kirjinta.
"Ke! Bebi waike kam wacce irin sakarai ce baki ganin baki agidan kika fito a haka?" taji muryar mama cikin kunnenta tana mata faɗa, turo baki tai gaba tare da saurin kwance zaninta taja ta rufe Vest ɗin jikinta, wanda adai dai wannan lokacin Ali ya sauke wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciyata wadda inda kana kusa dashi zaka iya ganewa.
Shiko usman kallon Bebi yake a nutse yasan ƴan biyu tabbas wannan ba ɗaya daga cikinsu bace, kafin suji muryarshi yana cewa "Kai masha Allah mama wannan ma ƙanwar tawace ni dai bansanta ba su hassana na sani amman itace yayarsu ko?". yafaɗa yana sakin murmushi tare da kallon screen ɗin wayarshi sabida baison ganin Bebi a haka.
Dariya mama ta saki kaÉ—an tare da cewa.
"Bebi ce ai ba yayarsu bace kuma bama ita kebinsu ba akwai wannan namijin kawai dai ita haka yanayinta yake". tafaÉ—a tana makawa Bebi harara akan ta koma cikin É—aki amman Bebi tai biris sema kokarin kai hannunta kan tukunyar dambun gabanta take.
"Ayya Allah sarki Allah ya tayaki riko mama kina kokari gaskiya". Murmushi mama tayi.
"To yaya za'ai hakan ma mungode Allah su shida mahaifinsu ya rasu yabarmin su abayanta ma akwai mata biyu". mama ta faÉ—a idanunta yana É—an kawo ruwa wanda babu wanda ya kula da hakan.
Cikin sauri Aliyu ya É—ago idanunshi yana kallon mama wanda hakan yay dai dai da tashin Bebi tsaye itama domin taje kicin ta É—auko kwano a zuba mata dambun juyawar dazatai suka haÉ—o ido dashi,.
Cak! ta tsaya jikinta yana faman mazari sabida haÉ—a idanunta datai dawani haÉ—aÉ—É—an cikakken namiji wanda tsananin tsoronsa wanda bata san daliliba yay mata dirar mikiya, cikin rawar jiki tai cikin É—aki aguje! batare data shiga kicin É—in datai niyya ba sabida wani irin kallo dataga yana aika mata dashi mai shiga jiki.
Zuciyarta tana wani irin tsalle kamar zata fito waje ta faÉ—a saman katifa tana haki sam yunwar ta fita aranta haka tai ringingine hannunta dafe da saitin zuciyarta.
Damma inda Allah yaso babu wanda ya lura da wannan dramar daga mama har usman hankalinsu bai kai wajan ba.
Shiko wani irin murmushi ya saki na gefen baki, wanda duk hasashena nagaza gane nako meye, tare da zube hannayenshi cikin pocket ɗinshi kana ya taka har gaban mama wadda take kokarin juye dambun a cikin kular tsugunne yay agabanta irin na ƴan ƙwallon ƙafa, duk kamshin mayen turarenshi ya cika cikin gidan.
"Allah yay mishi rahama, kekuma Allah ya baki ikon kulada amanar da Allah ya baki amin".
Ya faɗin hakan tare da miƙewa tsaye ɓat! suka nemeshi suka rasa agidan sejin ƙarar bude kofar shi kurum sukai alamun ya fita.
Mama ce ta dubi usman tare dacewa "kuma shima cikinku guda?".dariya yay "Eh mana wallahi kanina ne shike bimin haka muke fama dashi tuzuru ne amman next week zamuyi bikinshi ai zakuje dai". yafaÉ—a yana dariya.
"Ikon Allah amman sam bakwa kama kota farce gashi kuma shi baida son magana nagani".mama tafaÉ—a tana zuba dambun cikin kular gabanta sabida ya kammala.
"Eh bama kama shida abba yake kama mukuma da ammi, kinga yafimu kyau haka ake faɗi sedai shi baƙine ai, kuma shi kaɗaine fa bakin duk gidanmu, wannan da kike gani seyay kwana baiwa kowa magana ba, me azumin magana ake faɗa miki". yafaɗa yana miƙewa tsaye tare da karasowa gabanta ze amshi dambun yana mata godiya.
Sosai mama tai mamakin wai cikinsu É—aya da usman amman sam hali ko kama baizo É—aya ba, dan tana hango kamewa tare da kwarjini wajan Aliyun wanda take ganin irin mazan nan ne marasa É—aukar raini tare da rashin son magana amman shikam usman daga gani yana da saukin kai tare da wasa da dariya, mika masa tai tana amsa sallamar dayake mata koda wasa kuma bata kuma bincikar sa akan jin wani labarin ba sabida tana ganin hakan ba girmanta bane sannan kuma ba huruminta bane ba.
Usman kamar ze ari baki haka yakewa mama godiya harseda mama ta dakatar dashi haka sannan ya fita ita kuma ta nufi soro ta rufe gidan É—an ragowar dambun data rage ta juyo a kwano ta nufi É—aki dashi dantabawa wannan acicin.
"Ai seki tashi kici gashi nan jikar mayun wata tunda kedai kunnen ƙashine dake kin fita kin nunawa maza nono kinji dadi ko?!nace kinji daɗi tunda duk irin kallon danake miki akan ki koma ki suturta jikinki kin kasa fahimta ko arfa na kalla agidan nan wadda batakai rabin shekarunki ba tasan minake nufi bare kuma ke".mama tafaɗa cikin jin zafin Bebin tare da nufar wajan kwanciyarta.
Amai makon Bebi ta mike taci dambun Sema sake dunƙulewa waje ɗaya tai acikin hijabin data ja ta rufa dashi tana mayar da numfashi sama sama, kamar mai cutar asma! tana rufe idanunta hasken ƙwayar idanunshi take gani yana aika mata da harara wadda ta gaza gane ta mecece?kirjinta suya yake mata wata zazzafar ƙwallace taji tana mata kai komo a saman kwarmin idanuwanta cike da mamaki ta saka hannu ta shareta.
"Nidai ka barni haka wallahi tsoro kake bani".tafaÉ—i hakan a fili tana rufe idanunta ruf ga wani mayen kamshin daya biyota har É—akin wanda take da tabbacin nasane.
Ahaka wahalallen bacci ya kwashe bebi batare data É—auki dambun taci ba.

Usman yana fita waje yaga wayam rike kular dambun yay katamau jikinshi yana karkarwa ya nufi hanyar fita daga layin amman ya jawa Aliyu, Allah ya isa tafi kwando dubu inda yasan wannan rashin mutuncin ze mishi wallahi da baze barshi ya fita ba,da taimakon turch light É—in wayarshi ya sami hanya har zuwa inda sukai parking.
Azuciye ya bude murfin motarshi ya shiga tare da kunnawa batare daya dubi Aliyu ba, wanda idanunshi yake bisa kan screen É—in wayarshi yana danne dannenshi.
Revars yay tare da É—aukar hanyar shi yana aikawa masa da harara!...............
11/14/21, 3:07 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.