Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 27 of 81
Shiko Aliyu tundaga step É—in bene yake rage kayan jikinshi sabida matukar gajiyar dayay, wadda bayajin zata barshima ya iya tsayawa cin abinci yafi bukatar ya soma gasa jikinshi da ruwan É—umi tukunna kafin komai ya gudana.
Bakinshi dauke da sallama ya nufi cikin babban falon nashi wanda yaci gyara mai kyau har wani turare aka zuba irin na Æ´an maiduguri babu abinda ke tashi cikin falon nashi se tsabar kamshi mai kashe jiki.
Mamaki yay gani ƙwan falon a kunne amman seya basar sabida, yana tunanin sister ɗinshi amina wadda take gyara mishi wajanshi ko ita ce data kammala gyaran ta manta bata kashe ƙwan falon ba, sabida amina kaɗai ya yarjewa tashigo tai masa gyara amman ƴan biyu ya hutashshesu ganinsu yake kamar babu wata uwar dazasu mashi se tsabar shirme da shiririta.
Shirt ɗin jikinshi ya ɓalle ya ajeta saman seater falon sannan ya zame trouxer ɗinshi tunda daman yabar jacket ɗin daya ɗorota samansu acan motar usman.
Dagashi se single and boxer ya nufi hanyar bedroom ɗinshi yana ɗan miƙa kaɗan sabida mugun gajiyar dayaci karfinshi.
Hohoho! Umma ta iya ɗura, sabida ta afka khadija cikin uku bala'i!!! sabida tunda ta soma ɗura mata maganin mata masu ƙarfi tare da gyara na mussaman kasancewar gabatowar bikinsu yasa takejinta acikin wani irin feeling condition wanda kusan kullum setayi zazzaɓi mai zafi tare da ciwon mara mai ɗan karen azaba wanda bai barinta tai katabus dan hatta schoolma ta daina zuwa, kana ganinta kasan tana samun gyara mai kyau domin taɗan ciko ta goge ta murje tai fresh babu abinda yanzu khadija ke bukata kamar namiji cikin dare har kuka! take idan jarabarta ta mikarta sedai inda zata godewa Allah dayasa ita ɗin bata fito cikin jerin mata mabiya mazaba, hasalima yawan tara maza baya cikin tsarinta tun tasowarta ita dai barta da ɗaukar kai da iyayi da yanga tare da ɗan banzan kishin tsiya mussaman akan gwarzon nata Aliyu wanda tun wajan sallar isha'i tagama hadewa cikin tsadaddun kayan kanti masu matse jiki tai ɓarin manyan turarurruka masu kama jiki, wanda ummanta ta bata abinci da abinsha ta kawo masa amatsayin nata na tarbarsa wanda cikin dabarar da umman tai mata tafaki idanun ammi harta samu damar hayewa saman nashi, wanda ita kanta tasan a tsananin dokar ammi bazata barta ta keɓance dashi a part ɗinshi ba, shiyasa ta faki idon kowa tayo nan ɗin, tunda ta shigo taji kamshin turarensa wanda yake kame cikin kujerun falon shiya haifar mata da kasala mai zafi tare dajin wani mugun feeling!.
Tun shigowarshi idanunta yake kafe akansa wadda itan take kwance saman Threeseater tai ringine hannunta dafe da mararta ganin surar jikinshi bakaramin firgitata yayba wanda har wani zullo zuciyarta ke mata wajan angizata zuwa gareshi, lumshe idanuwanta tai tare da dirowa gadan gadan ta nufi wajanshi.
Cikin zalama ta É—ora hannunta a tsakiyar west É—inshi take kuma tasoma murza wajan kaÉ—an kaÉ—an tana lumshe idanunta tana furzar da huci, kamar wata mahaukaciya ta É—ora kanta agadon bayanshi tana shakar kamshinsa.
Yana kokarin murÉ—a handle É—in kofar yaji É—umin hannu a kwankwasonsa cike da dakiya ya cigaba da bude kofar batare daya juyoba.
Tsananin mamakine ya kamashi lokacin dayaji kwanciyar kan mutum agadon bayanshi bai jiyoba ya zira jikinshi zuwa cikin katafaren É—akin nashi.
Mamakine ya kasheshi lokacin dayaji anjawoshi da ƙarfi zuwa gaban kofar amman dayake namijin duniya ne ko gezau sema jin datai kamar tajawo dutse!
Kuka take a wannan karon tana murza kanta gadon bayanshi.
"Plsssss yayahhhhhhh dan Allah ka jiyoooooooo ina bukata yayaaaaaaaa"
Takai maganar da wani irin rawar murya.
"Kutumar uba! yaja wata ashar wadda bata saba fita a bakinshi ba, cike da zallar mugunta ya juyo da ita yana kare mata kallo idanunta lumshe suke ruff kamar ƴar maye, cike da mugunta ya tureta yana watsa mata wani firgitaccen kallo amman dayake hanakalin nata yay nisa batajin kira yasa take kara ƙoƙarin kai kanta gareshi.
"Idan kika yarda wannan ƙazamin jikin naki ya kuma raɓar jikina wallahi!".
Bai karasaba sedai yaja ƙwafa! tare da matse yatsunshi.
"Shasha sakarar banza".
YafaÉ—a yana bude kofar bathroom É—inshi ya faÉ—a.
Sosai ya shiga wani irin firgici wannan wani irin masiface yarinya zatai masa fyaÉ—e har cikin É—akinshi lalllai tarbiyar yanxu ta kama uban É—akinta, to wannanma fa agidansu take inaga Æ´an waje kuma se abinda hali yay.
Tabbas yanajin ze kara saka idanu akan kannenshi fiye da'da dukda yasan su basu isa sunyi ba se Allah.
Acikin matukar tashin hankali yay wanka yana aiyana rashin kamun kai na khadija, wanda lokacin daya fito bai ganta aÉ—akin nashi ba.
Babu yadda zeyi da mahaifanshi amman bada ban hakaba da bayajin ze iya auran khadija sabida baisan maza nawa tabi a waje ba, wata sassanyar tsanartace yaji ta ƙara tabin jikinsa da zuciyarshi baki ɗaya.
Dan haka bai sami sukunin cin abinci ba ruwa kawai yaketa É—aÉ—akawa cikinsa haryay nafila ya haye saman bed yana faman serching cikin ransa.
Itako khadija wannan tsawar daya daka mata ita ta dawo da ita hayyacinta aguje ta sauka ƙasa inda Allah ya sota babu kowa a falon farko dan haka kanta tsaye part ɗinsu ta wuce, aguje umma tana mata magana amman ina kuka kawai take bathroom ta wuce taita sakarwa kanta ruwa har komai ya lafa mata sannan ta haye kan gado tai lamo kamar wata marar lafiya.
Da tsananin damuwa ya kwana har zuwa wayewar gari rannan nashi a haɗe yake tamau kamar an aiko mishi da saƙon rasuwa.................
Tunda asubar farko Bebi ta mike kanta tsaye bandaki ta nufa domin ta gyara jikinta kamar yadda mama ta koyar da ita.............
*ƘARAMARSU* ✊
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_Albishirinku iyayen yara dama yaran baki ɗaya, shin ko kinsan shararriyar tashar nan ta youtube mai suna *Abdur-rahman* ta shirya tsaf domin baku gudunmawa wajan tayaku bitar karatun ƴaƴanku cikin sauƙi?, Kai dai/ kedai maza garzaya wannan shararriyar channel ɗin domin ki dannawa yaranki dansu karu da zazzaƙar ƙira'ar da *Abdur-rahma* ke gudanarwa wajan bitar karatun alkur'ani mai girma acikinta daman sauran littattafan addinin islama kada ki manta da danna *SUBSCRIBE* tare da ƙararrawar sanarwa mungode_
https://youtu.be/PFTnz8JGFfQ
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
            Â
            *41&42*
Sosai ta gyara jikinta tas ta wanke ko ina sannan ta fito waje tai alwala ta shiga cikin É—aki lokacin duk su mama suma sun tayar da sallah kasancewar ita batayi tana fashi yasa ta bude sif É—insu ta kaya ta dauki wanda zata saka tare da pant da tsummanta taÉ—an ja gefe ta shirya kanta, suna idarwa su mama suka fita waje domin haÉ—a sanwar dambu ita ko kwanciyarta tai tana karatun azkar É—inta na asubahi wanda ta haddace shi daka.
Æangaren ALIYU rannan baÆ™iƙƙirin ya kwana dashi koda asubahi ma daya tashi watsa ruwa kawai yay tare da nufar masallacinsu wanda ke cikin harabar gidan.
Ana idarwa ya fito sabida yana son yay sammakon office domin akwai abubuwa masu yawa dake gabanshi.
"Hy mr man barka da asubahi' Yaji muryar usman wanda shima kusan atare suka fito daga masallacin, ɗan dakatawa yay har usman ɗin ya karaso sannan suka jera ciki sabida daman ƙa'idarsu ce duk safiya sesunje gaisar da mahaifansu.
Ahanya usman yake bashi labarin rainin hankalin da zee tai mishi domin ko daya koma jiya tare da dambun nan ya tarar tai barci koda ya tasheta seta saka masa kuka! wai damme tana baccinta mai dadi ze tada ita da ƙyar ya lallaɓata ta koma baccin batare dataci dambun nanba, amman tace yau da safe zata ɗumama taci ya saka mata a frij.
Yaƙarasa gayawa Ali yana dariya, shikam Ali murmushi kurum yay sabida damuwar dake cin ranshi daman ai shima usman ɗin ya saka kanshine amman shikam bayajin ze tsaya mace ta dinga bashi order irin haka.
Sallama sukai cikin babban falon abbansu wanda suka tarar da sauran ƴan uwansu azaune kowanne gabanshi ɗauke da medium cup wanda aka shaƙeshi da ta'tacciyar zuma mai kyau wadda suke shanta aduk wayewar asubahi wannan al'adar mahaifinsu ce tun suna ƙanana yake musu hakan kuma gashi har girmansu basu dainaba domin hatta su ya abbakar dasuke manya suma sesunzo shan zuma kullum ta Allah.
Gaisawa sukai dasu abba sannan suka gaisa da ammi da ya abbakar, usman ne ya miƙa hannunshi ya ɗauki zumar gaban Amina ƙanwarasu wadda take gaishesu cikin respect, shiko Aliyu mikewa yay tare da kallon usman.
"Nifa zanje nai shirin office dan Allah karka mana delay kaga motana har yau tana garage, pls ka shirya da wuri".
Da kallo ammi ta bisa.
"Kai bazaka sha zumar ba kenan É—azuma nahau samanka yadda najera maka abincin nan haka nasaka su hassana suka kwasomin shi baka ko taba shiba".
ÆŠan shafa kanshi yayi tare da kallonta kaÉ—an.
"Ammi banji kai komai bakina yanzu da sassafan nan, sauri nakeyi kinga yau ko morning training ma banje ba sabida nai latti".
Abbane ya cafe maganar.
"To bara a haÉ—a maka break seka tafi dashi office É—in ko? ai baka tafi haka ba".
Cikin sauri usman ya amshi maganar.
"Dan Ammi kubarshi akwai masu dambu wallahi Æ´an gayu kawai ma siya muci".
Hararar da Aliyu ya watsawa usman ita tasaka usman É—in babu shiri yaja bakinshi yayi gum.
Ammi dariya abba dariya ya abbakar dariya su amina da Æ´an biyu ko suna son yin dariyar amman suna tsoro.
Fuww ya wuce samanshi yabarsu anan, seda ya tafi sannan ya abbakar ya dubi usman.
"Kaima kasan wancan miskilin baze iya cin abincin waje ba tsokanace kurum irin taka".
Hirarsu suka ɗan taɓa kaɗan sannan sukaiwa iyayen nasu sallama kowanne ya nufi yin abinda ke gabanshi, ƴan biyu shirin schl amina shirin office, suma su usman nufar part ɗinsu sukai domin suyi shirin fita office.
Ammi da abba kaÉ—ai ne a falon suna kallon labarai a tashar CNN.
Cikin kuzari da zafin nama yagama shirya kanshi cikin fari ƙal ɗin yadin tisue baƙar hular zanna tare da bakin takalmi mai rufaffan sama, se baƙin agogon rolex daya ɗaura a tsintsiyar hannunshi, fitinannun turarukanshi masu azababban ƙamshi yaywa jikinshi ɓarinsu.
Da hanzari ya ɗauki jakar laptop ɗinshi tare da tarkacen wayoyinshi, bai saka komai acikinshi ba ya kullo ƙofar bedroom ɗinshi tare da saukowa zuwa ƙasa yana zuba uban kamshi, bakaramin kyau wannan shigar tai mishiba ta ƙara masa ƙwarjini da haiba tare da tsantsar kyau irin na asalin yaren hausa fulani.
Still ya kuma samun iyayen nashi a falo hankalinsu yana kan TV sabida labaran da suke kallo na safiya.
Ƙarasawa yay gabansu tare da tsugunnawa har kasa yana gaya musu cewar xe tafi office.
Ammice ta dubeshi.
"Aliyu! wai miyasa kakeson jamin magana ne agun mutan gidannan kullum ɗauka suke ninake ɗaure maka gindi hatta mahaifinka gayanan duk sangartar dayake maka amman wataran idan idanunshi ya rufe seyace nike shagwaɓaka".
Ta numfasa sannan ta cigaba da magana.
"Jiya ka dawo daga legos amman ka gaza zuwa ka gaishe dasu yanxu ma haka fita xakai amman bazaka iya zagayen gaishe da mutan cikin gidan nan ba ko?"
Kansa yana kasa yana wasa da carfet É—in falon da hannunshi guda, bai tankawa ammi ba kuma baya tunanin harta gama faÉ—an ze iya tankawa sabida baisan meze ce mata akan hakan ba.
"Ba magana ake maka ba wai babana! É—azunnan Alhaji babba yagama yimin faÉ—a akan yadda kazo bakaje ka gaishe dasu ba, kaga nifa bana son abinda ze dinga kawon matsala da Æ´an uwana".
Cewar abba kenan wanda hankalinshi ke kan tvn gabanshi.
"Ayi hakuri xan gyara insha Allahu".
YafaÉ—i hakan yana jin ransa na suya shifa abubuwan gidan nasu sam sun soma fitar mishi daga kanshi
Mikewa yay yana kuma yi musu sallama batare daya nufi inda ammi ke nausar dashiba.
"Daman nasan wannan shegen taurin kan nashi wallahi bazeje É—in ba yadai faÉ—i hakan ne danya amsa maganar tawa, ya Allah ya Allah ya yayewa wannan yaro wannan kafiya da taurin kai amin".
Cewar ammi tana kallon abba wanda yay kamar baijita ba.
Aparking space ya tsaya suna gaisawa dasu fahad da sauran ƙannenshi waɗanda suke cousins kafin ya ɗauko wayarshi acikin aljihun wandon farin yadin jikinshi yana kokarin niman layin usman sema gashi nan ya fito cikin shigar black suite wadda tai mishi kyau babu laifi.
Batare da ɓata lokaciba usman yaywa motar key suka shige tare da nufar bakin gate.
"Ni wallahi daga yau bazan kuma dropping É—inka ba, nagaji da wannan takurar haka kurum da aurena fitar office a wannan duku, dukun".
Usman ya faÉ—a yana É—agawa masu gadi hannu lokacin yana kokarin fita daga gate É—in gidan.
Har suka hau kwalta yanawa Ali sababi wanda shi sam baima É—ago ba bare usman yasaka ran ze tankashi sema bude datar shi dayay ya shiga face book, abinshi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.