Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 81
"To babu komai rahane insha Allahu semu gwada can ɗin, sedai kuma dole mu sami abin hawan dake kai musu kayan abincin, zan dinga dambu da wake da shinkafa, amman dai Bebi banda ita sabida makaranta".tafaɗa cikin gamsuwa da maganar rahane tare dajin daɗin hakan takuma tabbatar da cewa baban nazir ze kula da ƴan biyu sosai sabida gudun wata ɓaraka.
"To shikenan nagode bara na ƙarasa idan yaso ranar asabar seku fara kinga yau laraba sabida su koda yaushe suna aikine har ladi". ta muskuta zata miƙe"To babu komai amman yanzu dai vara na baki wayata ki sakamin lambar baban nazir sabida idan sunzo su nemeshi koya kikaga?".tafaɗa tare da janyo wayar ta mika mata ita kuma ta karɓa ta saka mata tare dayi mata sallama ta fita.
Har soro ta bita tana mata godiya...........
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
            *15*
Har soro mama ta bita tana zabga mata godiya, juyowa rahane tayi tare dayin murmushi "Haba maman ƴan biyu irin wannan godiya haka kamar wadda naiwa babbar kyauta, ai komai da kikaga mutum yana yi tofa yiwa kansane".tafaɗa tana saɓa mayafinta a saman kanta, tare da tura labulan buhun soron sannan suka kuma sallama a karo na biyu rahane ta fita, mama cikin gida ta dawo, ta shiga kicin domin ta ɗora musu abincin rana ganin azahar ta kawo kai.
Shahid ne yayi sallama bayansa su ihsan ne kamar haɗin baki, mama ce ta leƙo da kanta daga cikin kicin ɗin tana musu barka da dawowa seda ta ɗora sanwar dafa dukan, shinkafa, sannan ta fito tsakar gida duk tagama haɗa uwar zufa ajikin nata, shahid wanda ya cire kayansa na makaranta yana shirin fita mama ta kirawo tana mai neman wajan zama a saman tabarmar tsakar gidan, dawowa yayi da baya.
"Gani mama".yafaÉ—a yana tsugunnawa a gabanta..
"Yawwa shahid wajan maman farida mai adashi zan turaka wannan dubu goman tawa danake haÉ—awa Bebi kuÉ—in magani zata bani".
Da kallo ya bita yana nazarinta.
"Mama dan Allah mezaki dasu? wata matsalarce ta faru?".
YafaÉ—a a nutse tare dayin tsam da ransa yana sauraranta dan yaji mezata ce masa.
"A,a shahid wata damace Allah ya kawo mana.........",tass! ta kwashe komai ta gaya masa sannan ta ɗora da,"Shine daman nakeson kazo kaje kasuwar jan guza anan komai xefi mana sauƙi amman ya kagani?".tafaɗa tana tsira masa ido dan taji ta bakinsa.
Sunkuyar da kansa yayi ƙasa tare da saka hannu ya share hawayen dayake zubo masa.
Sannan ya É—ago yana kallonta still wani ruwan hawayen bai daina zubo masa ba, sosai mama takebin shahid cikin zuciyarta da tarin tambayoyin dalilin hawayen nasa, amman setai shuru ta zuba masa idanu tana kallonsa.
"Mama Allah ubangiji ya bamu nasara, acikin wannan sana'a dazamu fara, mama! haƙiƙa hawaye baze bar zubarmin ba harse naga lokacin dani kaina zan xame miki Garkuwa, insha Allahu mama senai miki abinda zakiyi alfahari dani, kullum ina takaicin ganin ɗan kowa ya kama hanyar makaranta da safe, amman ni ƙanwata da yayyena sedai su ɗora bokiti aka sutafi tallah! ya rabbi ka kawo mana ɗaukinka dukda hakan ma muna godiya gareka".
Yafaɗa yana miƙewa tare da kallonta.
"Bara naje na karbo na dawo".
Bata iya bashi amsa ba, harya juya ya kama hanyar wajen sabida yadda yaron nata ya karyar mata da zuciyarta, tabbas ko yanxu tana alfahari da shahid kai bama shi kaÉ—ai ba dukkan Æ´aÆ´an da Allah ya bata tana alfahari dasu fatanta a kullum Allah ya raya matasu cikin amincinsa Amin.
Su ihsan sallah sukai suka É—an kwanta baccin gajiya tana cikin wanke shinkafa shahid ya shigo a tsaye ya tsaya tare da cewa."Mama kawai lissafamin nai sauri naje kinga garin akwai hadari sosai".
Hannunta ta wanke tare da nufar kicin ta zuba shinkafar sannan ta kuma dawowa.
"Kadai bari kaci abinci ko?".
TafaÉ—a tana zama, akan tabarmar datake wajan.
"A,a mama nidai nafison naje na dawo tukunna".
Lissafa masa komai tayi cikin nutsuwa sannan tai masa fatan alkairi ya kama hanyarsa ta tafiya, ita kuma ta miƙe tayi kicin danta duba sanwa.
_SharaÉ—a Æ´ar kasuwa_
Tunda su Bebi suka fita yau take ƙunci hatta kallon arziki bataiwa kowa ba haka sukaita cinikin awarar tasu duk jikinsu hussaina yayi sanyi sabida ƙuncin da bebi takeyi ƙarfe uku awararsu ta ƙare, tawajan dasu siba suke suka wuce wanda siba yayi saurin sada kansa ƙasa yayin dayaga Bebi ta zo giftawa ta wajansun sabida tsoro! danshi yanzu Bebi mugun tsoro take bashi bawai ɗan kaɗan ba sam yarinyar tariga data firgitashi tun ranar data ɗebo masa police.
Suna tafe hassana ta dubeta"Waike yau wani salon iskancin ne yau narashin magana ya motsa miki?".tafaÉ—a mata tana tsareta da ido tura baki tayi gaba tana tafe tana gunguni.
"To duk baku bane zaku cewa mama ƙarya nake akan exam, wai idan nayi karatun nan ku xanyiwa?".tafaɗa tana jan kafarta cikin sauri sabida bakaramin haushinsu takejiba, yadda suka zaƙe awajan mamaa ɗazu musamman hussaina.
Gaba tayi tabarsu abaya tana mita"Kema dai da ɓata baki nidaman nasan abinda yake damunta shiyasa kikaga nai banza da ita".cewar hussaina wadda take kallon hassana cikin dariya,"Hmmm ai halin Bebi se ita Allah dai ya shirya mana ita, ashe duk akan makaranta take wannan ƙuncin" hassana tafaɗa itama cikin dariya tafiya suke suna kuma mai maita halin Bebi harsuka iso gida wanda ita tana gaba su suna bayantane...........
*************************
Cikin nutsuwa ya saka ƙafafunshi akan lallausan makeken carfet ɗin dake malale acikin falon, wanda babu komai na tarkacen kujeru acikinsa face TV tare da wasu irin tum-tum da aka jera se uban kamshin dake tashi tare da wani irin sassayan sanyin AC'n dake faman ratsa cikin falon.
Sallama yay can cikin ƙasan maƙoshinsa tare da kallon wasu ƴan mata farare masu kyau kana ganinsu kaga tagwaye.
Tunma kafin yace komai sukai saurin rissunawa "Yaya Aliyu barka da fitowa yaya aiki?".da sauri suka bar wajan har suna rige-rige sanin baze tanka masuba.
Se asannan nabi bayansu da kallo babu laifi ƴammatane cikakku waɗanda kana ganinsu kasan ansha boko domin ba yara bane ba, kuma kallo ɗaya xakayi musu kasan ƙan nansane sabida sunɗanyi kama ta jini sedai su farare ne.
Tsaki!yaja afili tare da neman waje ya xauna, still wata budurwar ce ta kuma fitowa cikin nutsuwa wadda kallo ɗaya zaka mata ka gane itama ɗin kanwarsace sabida kamarsa da ita harta ɓaci hatta kalar fatarsu gudace sedai ita ɗin daga gani ta girmewa waɗannan tagwayen.
"A,a yaya harka dawo ina yini ya aiki?". tafaÉ—a tare da nufar wani É—an kwana anan cikin falon, ruwa ta É—auko masa tare da glass cup, sannan ta kawo masa gabansa tana zama agefensa.
"Lafiya ƙalau Amina yanaki office ɗin?" shima ya tambayeta.
Dariya taÉ—anyi kaÉ—an"Hmm wallahi yaya yau É—in nan se a hankali".tafaÉ—a tana gyara zamanta agabansa, wadda daga gani ana good time atsakanin Æ´an uwan juna nan.
"Ok, ina Ammi?". yafaɗa murya can ƙasan maƙoshinsa,"Tana bedroom ɗinta amman naga tana shirin fitowa nan ɗin sabida ya abbakar yace tayi masa dambu yana hanya".wara idanunsa yay waje,"Aikam nima kamar tasan banci abinci ba yau".................
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.