Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 76 of 81

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }

_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_

*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_

*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»

_kai ƙoƙarin ganin kayi payement domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*
11/14/21, 3:20 PM - Allah Akbar: *97*

Tafiya ce mai tsayi daga kamfaninsu zuwa unguwar da bebi take.
Seda ya tsaya a kasuwar Æ´an kaba ya sayo mata kayan fruit, sannan ya nufi gida a bakin hanyar da zata sadashi da layin gidan yay parking ya nufi wani sabon gurin daya gani wanda ake gashin kifi, wajan da layi seda yaÉ—an jinkirta kafin azo kanshi leda biyu yay musu tare da drinks masu sanyi sannan ya nufi mota ya zube su a bayan motarshi sannan ya nufi layin gidan nashi
Gate ya buɗe ya shigar da motar sannan ya kasheta ya ɗebi ledojin hannunshi ya nufi gaban ƙofar part ɗin bebi, spare keyn dake hannunshi yay amfani dashi ya buɗe kofar bakinshi ɗauke da sallama ya nufi cikin gidan.
Lokacin wajan karfe biyar ɗin yamma, sosai yay mamakin yadda gidan yake tsaf ko ina ƙal ƙal, ga bakin famfo nan kamar ma ba,a amfani dashi.
Sallama yaketa faman yi yaji shuru kai tsaye kofar falon ya nufa nan ma seda yay sallama tare da buÉ—e labulan.
Wutar nepa ta haske falon ga fanka tana kaɗawa a hankali, tana kwance a ƙasan carpet ta cure hannunta a tsakanin cinyarta zube ledojin dake hannunshi yayi da sarsarfa ya nufi gabanta ya zauna daɓas yana mai saka hannunshi ya tattarota gaba ɗaya ya ɗorata a saman cinyarshi yana mai tsirata da idanunshi jiyake yana matukar missing ɗinta tamkar yay shekara dubu bai gantaba.
Juya kanta tayi tana mai gyara kwanciyarta batare data san da zuwanshi ba.
"Ummee! ummee!! nadawo fa"
YafaÉ—a yana hura mata iskar dake cikin bakinshi.
Lumshe idanunta tayi tare dajan numfashi kaÉ—an a hankali ta buÉ—e idanunta tarwai a saman fuskarshi, janye jikinta tayi wanda yake zafi zau kamar wuta.
Cikin sanyin jiki ta mike ta nufi tsakar gida.
Yawu ta zubda tana mai wanko bakinta sannan ta dawo É—akin.
"Sannu da zuwa ina yini?"
TafaÉ—a tana mai zama daga É—an nesa dashi.
Kafa mata narkakkun mayun mayunwatan idanuwanshi yayi yana nazarinta gaba É—aya tai wani irin duhu ta rame a mai makon taÉ—an ciko irin na masu ciki a,a ita se uban duhun datayi da kuma rama.
"Zonan"
YafaÉ—a mata fuskarshi É—auke da damuwa.
Da jan jiki ta iskeshi gab dashi ta matsa kamar zata hau saman jikinshi.
Hannunshi mai cike da gargasa kota ina ya saka ya janyota ta faɗa samanshi ya saka ɗayan ya taɓa saman wuyanta.
"Meke damunki naji zazzaɓi ajikinki?"
YafaÉ—a cikin matsananciyar damuwa.
ÆŠan xamewa tayi daga jikinshi tana yamutsa fuskarta sam bata son warin turaren nan.
Da sauri ta mike aguje tai tsakar gida tunma a bakin kofa take kakarin amai tana mai saka hannu tana dafe maƙoshinta.
Da ƙyar ta karasa gaban rariya ta dinga sheƙa amai wanda babu komi cikinshi se ruwa.
Yana tsaye akanta harta gama aman da kansa ya zuba mata ruwa ta wanke fuskarta da bakinta.
Cikin lokaci kaÉ—an ya gyara wajan sannan ya kamata suka nufi falon ya kwantar ta saman sopa.
Idanunshi jajur da alamun damuwa atare dashi.
YaÉ—an matso gabanta.
"Sannu kinji".
YafaÉ—a a tausashe.
Hawayen datake dannewa ne yake zubowa.
"Nidai ka matsamin wallahi wannan turaren naka bana sonshi kamar zan mutu"
TafaÉ—a tana juyawa tai ruf da ciki tare da danne hancinta da tafin hannunta.
Kamar zeyi kuka ya dubeta.
"naji amman dan Allah ki gyara wannan kwanciyar sabida gudun matsala bara na sauya kaya sena kira dector".
Yafaɗa yana mai tsayawa akanta da ƙyar ya samu ta gyara kwanciyar tata tare da toshe hancinta da ɗankwalin atamfar jikinta.
ÆŠaki ya wuce ya sauyo kayan jikinshi sannan ya fito wayarsa ya É—auka yana mai dannawa ya kirawo likitanshi bugu É—aya ya É—auka magana yake masa cikin harshen nasara bayan sun kammala ya katse wayar yana mai komawa gabanta.
"Sannu meke damunki yanzu?"
Cikin sauri ta mike daga kwanciyar tana mai dafe kanta.
Sannan ta zauna kasan carpet tana kallonshi
Idanunta yay wani irin ja cike da damuwa ya zauna a gabanta ya saka hannunshi ya kamo nata hannun ya tsirama faracenta idanu sunyi wani irin fari tas wanda ke nuni tana É—auke da juna biyu.
"Wallahi nima ban saniba amman bakaji yadda nakeji ba"
TafaÉ—a kamar zatai kuka!
"Look dan Allah kada kimin kuka! please yanzu dector zezo kinji"
YafaÉ—a cikin kwantar da murya kamar ba Ali ba.
"Zafi nakeji bara nai wanka dan Allah kozaka cewa babansu mufida ya kawon kankara, kullum innace ina so se maman mufida tace bazan shaba wallahi ni kaɗai nasan zafin da jikina kemin kofa zazzaɓi nake bana rufa sabida zafin jiki"
TafaÉ—a muryarta tana rawa.
"A,a bazaki sha sanyi ba kibari likitan dai yazo yanzu mai zakici?"
Juya mai ƙeya tai tana kallon ƙofa tanajinshi yana ɓaɓatunshi tai masa banza itafa ala dole ya bata haushi
Tashi yayi ya janyo ledojin dayazo dasu ya miko mata gabanta.
"Ki duba kozaki samu abinda zaki iyaci"
yafaÉ—a yana mai zama agabanta.
"Nifa na gaya maka kankara zansha da lemon fanta".
"Kamar yaya?"
Ya tambayeta.
"Ka ɗaukon kofi ka juyon lemon seka sakan kankara ciki ka ƙaran ruwa zantashan abuna har gobe"
"Gaskiya bazaki sha sanyi ba wallahi kinjima na rantse".
YafaÉ—a mata fuskarshi daure.
"Tom shikenan"
TafaÉ—a gwanin tausayi.
Sannan ta mike ta nufi uwar É—aka tabarshi anan batare data bude ledojin ba.
Dafe kanshi yayi ahaka umman mufida wadda batasan da zuwanshi ba tayo sallama tana cewa.
"Haba anty bebi yau tun safe bakici komaiba kinata zama ahaka ga awarar na samo miki wallahi seda na fita wajan gari wai ko baccin nedai baki tashi ba?"
TafaÉ—a tana yaye labulan É—akin ganinshi a zaune yasa tai saurin komawa tana mai jin tsananin kunyarshi.
Tashi yayi ya nufo tsakar gidan ya ikota.
A mutunce suka gaisa.
"Kayi hakuri wallahi bansan kana gidan ba dayake ban lura da motar taka bama"
A sake yace mata.
"Lah babu komai ina laifin mai kula maka da naka nagode sosai da kokarinki tace ke kike miko mata abinci ma angode"
Murmushi umman mufida tai.
"Wallahi oga yarinyar ce take bani tausayi sabida cikin naku mai tsurfane ga laulayi mai zafin gaske bakaga yadda take fama ba, kagafa yau tun safe ko ruwa bata kai bakinta ba ta dage se tasha lemo da kankara wai na gayawa babansu ya siyo mata nikuma naki sabida kasan yadda sanyi ke lalata yaro aciki shike sakawa a haifi yaro da cutar limoniya, to shine tace awara kuma kasan babu anan wallahi seda na fita da kaina na samota ka ganta yanzu a hannuna"
ta miko masa robar awarar.
Sosai yake mata godiya sannan yace ze bawa goma sako ya bata.
"Amman in tanason awarar sena saka akawo wake ana yi mata in ba takura?"
A sake tace.
"Wani takura kuma oga bara dai mugani kasan abin masu ciki hawa da saukane in tai na'am tana ci É—in ai seka siyo matan".
Godiya yayi mata kana ta juya ta fita daga gidan.
Shiga É—akin yayi ya sameta kwance a saman kafita rannan a haÉ—e tamau jira take ace mata ket ta fashe.
A tsaye ya tsaya akanta.
"Ga saƙonki inji matar goma ki fito falo ina jiranki".
YafaÉ—a yana mai komawa falon ya zauna.
Cikin sauri ta fito sanin sakon nata.
Washe bakinta take tare da zama agabansa ta amshi awarar ta budeta jikinta yana rawa ta somaci hannu baka hannu kwarya.
duk yawan awarar seda ta cinyeta tass har tana neman kari.
"Dan Allah akawon wata wallahi akwai daÉ—i"
Murmushin jin daÉ—i yayi ganin taÉ—anci abincin.
"Tom ga kifi nan da kayan fruit awarar kuma za,a siyo wake se ana yi miki"
Janyo ledar tayi kamar abin arziki ta bude ta kifin taÉ—an yagi kaÉ—an takai bakinta.
Wani masifaffan amai ne ya taso mata wanda kafin tai yunkurin tashi tuni yagama wankesu tas ta amayar da duk awarar dataci jan gefe tayi tana zuba uban Nishi tare da dafe kanta dake mata ciwo.
"Sannu"
YafaÉ—a a kasalance da tausayawa.
Da kansa ya gyara ko ina harda fesa turaren daki sannan ya É—agata ya kaita tsakar gida ya tube mata kayan jikinta.
Komawa É—aki yayi ya sauyo kaya ya fito da wanda ya tube É—in ya tari ruwa a famfo ya wanke mata jikinta, se wani kare kirjinta take da hannu haka ya sunkuceta yakai saman kafita kana ya komo tsakar gidan omo ya zuba saman kayan nasu.
First in history Aliyu sunkuye gaban famfo yana wanki abinda ko singlet ɗinsa bai taɓa wankewa ba sabida sunada washing machine ɗinsu agida,amman yau soyayya da tausayi ya sakashi sunkuyen wankin kayan aman bebi, hannunshi na masa zafin rashin sabo amman haka ya daure ba ƙyamata haka ya wankesu tass ya shanya ya wanke tsakar gidan sannan ya nufi toilet yay wanka tare da ɗauro alwalar magariba ya nufi ɗakin.
tana zaune saman kafita ta sauya kaya zuwa doguwar riga.
Tana rike da carbinta ahannu ta kammala azkar ya shigo É—akin ganinshi daure da tawul yasa taÉ—an kauda kanta sabida yadda ya cika mata É—akin da girman jikinshi.
Gaban jerin kayansa ya nufa ya shirya cikin farar jallabiya sannan ya tako gabanta.
"Sannu gimbiya bara naje nai sallah kafin dector ya karaso kema ya kamata kiyi sallah kafin na dawo".
Murmushi tai kaÉ—an tana kallonshi.
"Hmm bara naje na
wanke kayan can ai naji daÉ—in jikina wallahi ba kamar É—azuba"
Dariya yay kaÉ—an.
"Sedai ki wankeni amman na kammala wanke kayan ay"
zaro idanu tayi waje can kuma setai rau rau da idanu.
"Haba ka dawo ko abinci ban baka ba ban kai maka ruwan wanka ba sannan na haɗaka da aikin da baka da ƙwarewa akansa ai da tausayi ma wallahi nidai kadama ka wanke barshi xan wanke abina".
Tsira mata idanu yay yana kallonta.
"Nafa wanke karki damu ni ay kin biyani bazaki gane komai ba sena dawo xaki bani abincinki mai daÉ—i Allah yasa na wannan karon yafi na ko yaushe"
Da sauri ya fita jin ana kokarin data sallah, itama a hankali ta mike ta fita tayo alwala ta dawo ta tayar da sallah.
Tana zaune saman sallaya suka shigo bayansa wani mutum ne dogo siriri Allah yasa da hijab jikinta shima ganinta shirye yasa ya mayar da ajiyar zuciya daman baima kawo tana falon ba shiyasa suka shigo da dector É—in.
A mutunce suka gaisa da likitan har yana tsokanar Aliyun, sannan ya fara fiddo da kayan aikinshi.
Gwaje-gwaje yay mata sannan ya bata wata kwalba yace taje tayo fitsari yanzu ta kawo masa.
A kunyace ta amsa shiko Aliyu ko ajikinsa sema hirarsu dasuke shida likitan.
Bayan ta kawo masa xama tayi agefe guda tana kallon yadda yake zuba fatsarin awani dogon abu, mintuna kusan goma ya kammala komai cike da ƙwarewa akan aikinshi ya dubi Aliyu.
"congratulation mr Aliyu madam fa tana É—auke da juna biyu na tsayin kwanaki goma"
Cikin farin ciki Aliyu ya mikawa dectorn hannu suka kuma musaba sannan yace.
"Masha Allah dector kenan kwana É—aya ne abin ya samu sabida yaufa kwananmu sha biyu da aure".
Murmushi likitan yay.
"A daren farko ma ana iya samufa bare washe gari lallai kai gwarzone Allah ya inganta ga magunguna zan haÉ—a muku na karin jini sannan kana kula da ita sosai wannan zafin jikin kuma karka damu zata dena soon insha Allah".
"Nagode amman tana amai fa"
"Okey shima in tana shan wancan jan maganin dana baku zeÉ—anyi sauki kasan shi wannan daman ko wacce mace tana yinsa inta da ciki marasayin basu da yawa"
"Ok nagode"
HaÉ—a kayansa yayi likitan kana ya dubi Bebi wadda take kunshe fuska.
"To madam Allah ya raya semun zo suna"
"Dariya Aliyu yayi kaidai yau dr kana ta babbar kyauta wallahi muje mota"
Fita sukai atare.
Da sauri bebi tayi daki tana dariya wai yau ita take da ciki oh daman haka mama tai ta fama lokacin datake da cikinsu katifa ta faÉ—a.
"Naiwa Æ´ata wanka na saka mata pampars taimin kuka nai mata rawa"
TafaÉ—a a fili tana dariya.
Sallamar dr yay da kudi masu yawa kana ya dawo ya tarar da ita tana dariya a É—aki ita kaÉ—ai zubewa yay agabanta.
"Kema kina murna xaki haihu kenan?"
Ya faÉ—a yana É—age mata gira É—aya.
Bata ce mai komai ba ta rufe fuskarta tana dariya.
Wayarshi ya dauka ya soma neman layin ammi.
Bugu É—aya ta É—auka bayan sun gaisa ya soma ratta ba mata bayani.
"Ammi fa yau bazan dawo gida sabida Mai sunanki batada lafiya dr kuma yace ciki gareta ai mana addu'a ammi"
Sosai ammi tahau murna tana hamdala nan tace ya bawa bebi waya amman fafur bebi taki amsa haka ammi tai masu fatan alkairi ta katse wayar usman ya kira ya shaidawa aifa nan usman yayta murna yana masa tsiya wai yacika haÉ—ama.
Numbern mama ya kira wadda yacewa usman É—in ya tura masa to bayan ya turo masane ya soma kira.
mama duk suna asibiti wajan ladi hassana ta miko mata wayar amsa tai tare dayin sallama bayan ta É—aga.
Jin muryar Aliyu yana gaisarta yasa ta saki fuska a nutse suke gaisawar.
Jimm yay kafin kuma yace mata.
"Mama ai mana addu'a dan Allah"
Murmushi mama tayi sannan tace.
"To Allah ya dafa maka adukkan lamuranka"
"Amin mama sedai fa mama kinyi jika wai bebi tana É—auke da juna biyu É—azu dr ke shedamin gatama zakuyi magana"
YafaÉ—a batare dayaji kunyar hakanba sabida yadda yake É—aukin cikin.
Kunyace ta rufe mama amman jin muyar bebi yasata dole tai magana.
"mama kun manta dani ko? ina nan bani da lafiya akawon ihsan mama"
Murmushi mama tai irin nasu na manya sannan tace.
"to naji uwar Æ´an raki haka kike masa wannan sangartar halan? to dai ki kula da kanki da wayonki na samu cikin arfa sabida haka ki kula da kanki Allah raba lafiya amin".
Murmushi bebi tayi"mama anty hassana fa?"
"Gata"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.