Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 53 of 81
*Alhamdulillahi nacika alƙawarin dana ɗaukar muku wanda rashin caji yasa ban cika da wuriba amman gashi nan nayi dik da ba,a kan kari nai ba waɗanda suke kai zasu gani waɗanda basa kai sedai in ALLAH ya kaimu gobe sa gani nagode* !
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2
NAKUÆŠINE
               *74*
Da baya taja ta zauna a gefen gadon tana dafe saitin kanta wani irin sihirtaccen tsorone yake ratsa ilahirin jikinta tunda take arayuwarta ta duniya bata taɓa jin makamancin tsoro kamar na wannan datake cikin kaɗaici haka.
Ta taso tare da mahaifiyarta da ƴan uwanta tunda suke basu taɓa raba makwanciba a iya wayonta, ko anguwar kwana mama bata zuwa kullum suna tare haka zalika suma bata barin suyi nisan anguwar da zasu kwana, to inama suke zuwa bayan dangin mahaifinsu sun juya musu baya duk irin yawansu, dangin mama kuma ƙalilan ne waɗanda suke zaune anan anguwar ƴan kusan suma kuma bawai shine dasu ba wannan dalilin yasa haɗuwarma take wahala amman duk da haka mama takan sakasu agaba da sallah takaisu suga danginta duk da batada uwa bata da uba kuma iyayenta ita ɗaya suka haifa sedai akwai ƴaƴan ƴan uwanta wannan yasa take ziyartarsu lokaci zuwa lokaci batare datayi gigin bita cikin gida ba ma'ana gidansu kawu tasi'u wanda in bazata manta ba kwanakin baya da babarsu kawu tasi'un ta rasu da mama taje gaisuwa da ɓacin rai ta dawo shiyasa ma yanzu dataji ɗayar tana ciwon ɓarin jiki koda wasa bata je dubiya ba.
Yau gata a ƙaton gida ƙaton ɗaki wanda ya cika da kayan alatun more rayuwa amman babu kowa nata tsananin kaɗaici tare da tsoro da zulumin kewar ƴan gidansu ita ta kuma kamata.
Zamewa tayi daga kan gadon ta zauna a ƙasan tiles sanyinshi na ratsata, hawayene masu zafi da raɗaɗi suke sauka daga kuncinta.
Babu tunanin datake face na ahalinta yanzu tasan Æ´an biyu sun can tare da mama suna baccinsu ita ko tsananin kaÉ—aici ya dameta.
Sam tunanin Aliyu ko nawani sharetan dayay bai dameta ba sabida batada wannan hangen a ranta auren ma bata kawoshi a wannan lokacin ba amman cikin hukuncin ubangiji segashi yazo mata itafa abinda ke damunta É—ayane tsananin kewar gida tare da tsoro.
Wani mugun fitsarine ya kamata amman yadda takejin tsoron É—akin yahanata nufar bathroom tayi bitsarib duk da taganshi acikin É—akin amman bata tunanin iya tashi daga inda take.
Ahaka bacci ɓarawo ya saceta batare data hau saman gadon ba bare kuma ta sami zarafin fitsari kowani abu.
Cikin tunani zee ta ƙarasa cikin ɗaki zama tayi abakin gado tana jiran usman wanda ke cikin bathroom yana wanka, mintuna kusan goma ya ɗiba kafin ya fito yana tsane jikinshi, seda ta bari ya kammmala komai cikin tsanaki sannan ta dubeshi a yayin dayake zama a gefenta.
"Yaya nidai inada magana dakai fatan zaka bani amsa mai kyau".
Mirginawa yay saman pilown dake gefenta sannan ya dubeta.
"Ina jinki amman son samu ki barni wallahi nagaji baccine akaina".
Murmushi tayi tare da shafo saman kanshi da hannunta.
"Yaya dan ALLAH da gaske waccen bakuwar ALIYU ce? naga sam batai wayewar business ba bare ace abokiyar kasuwancin sace pls dan girman Allah kaimin bayanin dazan gamsu".
TafaÉ—a cikin kwantar da murya.
Janyota yayi zuwa saman ruwan cikinshi.
"Yes my zee baƙuwar Aliyu ce da gaske amman wannan bakuwar bata tafiya bace ta xamace domin tuni ya aureta".
Zumbur! Zeee ta mike tare da furta.
"What! kana nufin waccan yarinyar matar Aliyu ce da gaske?".
Da kallon mamaki usman yabita sannan yace.
"Eh mana matarshi ce ta sunnan ko kina mamakine?".
YafaÉ—a yana janyota zuwa jikinshi tare da kai hannunshi saman ruwan cikinta.
"Haba yaya zaki saka nai asarar bebina kina wannan mikewa haka ai seki taromin aiki".
Zamewa tayi tare da kallonshi.
"Tayaya ya aureta bayan yasan zuri'armu ba'a AUREN BARE! gaskiya abin da mamaki ace kwananshi huÉ—u da aure yaje ya auro wata daban wadda bana tunanin su ammi ma sunada masaniya akan auren".
HaÉ—e ranshi yayi tamau kamar ba usman ba sannan ya mike ya zauna yana kallonta.
"Zee tuhumar auren sunna kike koko wata manuface aranki ina ruwanki da auren sa?".
Yafaɗa yana tsare girar sama data ƙasa.
"Babu ruwana da aurenshi amman maganar daka faÉ—i ce batada tushe balle makama in Ali bai auro wata ya kawoba kai zaka iya auro wata ka kawomin nan batare dana saniba tunda halinku na maza babu wanda bai fita ba".
Dariya zee tabasa daman wannan zargin natane yasa tai wannan mikewar zumburr lallai mata se abarsu amman seya basar tare da kallonta.
"Kinsan dai maganar irin haka bata taɓa haɗani dake ba why note zaki nemi musanta maganata alhalin kuma nasan yes da gaske nake maki".
Zama ta komo tai gefenshi tana kallonshi.
"Da gaske kake dan Allah in har kai ka aurota dan Allah ka gayamin danna san Aliyu baze zauna da waccan Æ´ar yarinyar ba sabida sanin son girmanshi duk da tanada kyau amman dai wallahi ina tam tamar yadda akai auren".
Riko hannunta yay tare da bata hankalinshi gaba É—aya.
Zayyane mata yadda akai auren yay batare daya ɓoye mata komaiba hatta haɗuwarsu da su bebi seda ya faɗa sannan ya zuba mata idanu yana kallon re action ɗinta.
jikinta yay matukar yin sanyi cikin sanyin jiki ta dubeshi.
"To amman fa abin da ban tsoro sabida akwai rikici agaba wallahi dan kuwa inhar alhaji yaji akwai case amman dik da haka bana goyon bayan ya saki marainiyar ALLAH wallahi harnaji ta kwanta min araina".
Dariya ya saki yana cewa.
"Da har anhau kishi amman da akaji ba matata bace ba an saki nizo mu kwanta ma zanta gobe shima mai amaryar baccinsa yake sabida haka komi ta famjama fanjam gobe ayita ta kare dan wallahi kafarshi kafarta dan ba auren jingina xaiyiba".
Ranta wasai tabi bayan mijin nata suka kwanta suna barwa gobe komai in ALLAH ya kaimu.
*NOTE*
_Assalamu Alaikum barkammu da dare dan Allah inkunjini shuru kucigaba da uzurina kamar yadda kuka saba wallahi se addu'a kwana biyunnan banjin daɗin jikina kunsam yanayin garin yadda ko ina ake fama da maleria kusan kowani gidama se ansami mai zazzaɓin nan sedai fatan Allah ya warware mana, tonima gani inafama da ɗan rashin jin daɗi kwana biyun nan kokari kawai nake wallahi wannan ma bana tunanin yakai one read more nadai yine danna cika alkawari dan Allah kuyi hakuri insha Allah gobe zanyi da yawa kuma ina muku ma albishir da cewa auren bare ya kusan zuwa makara fatan Allah yasa mugama lafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali amin summa amin nagode_
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2
NAKUÆŠINE
                 *73*
Jin tattausan hannunshi mai azababban ƙamshi datayi a saman bakinta shiya kuma ƙarawa jikinta rawa da kyarma akan wanda yake tun fitowarta.
Kafin taji dirin tsaiwarshi a bayanta hannunshi guda ɗaya ya saka ya riƙo tsakiyar ƙugunta irin riƙon nan na tsauri tare da jiyo da ita saitinshi tana fuskantarshi.
Wata azababbiyar faÉ—uwar gaba mai cike da firgici zulumi tsoro sune sukai mata dirar mikiya fiye dana da, Rintse idanunta tayi tana addu'a cikin ranta inda xaka kula lokacin zakaga kirjinta yana tsalle kamar ze faso ya fito waje sabida tsabar kaÉ—uwar datayi
Kallonta yake sosai ta cikin hasken farin watan daya haska tsakar gidan, batare daya É—auke idanunshi daga kanta ba.
Yace mata.
"zomu wuce".
Still hannunshi na riƙe da ƙugun nata, yana cigaba da kallonta se yanzu yake ƙara ganin ƙarancin shekarunta sosai.
Zumɓuro bakinta tayi gaba kamar yadda ta saba yima mama shagwaɓa duk da yadda takejin tsoronshi amman bai hanata turo bakin gaba ba, tana dira ƙafafunta ƙasa.
"Ni bazan bika ba dan Allah ka barni da mamammu".
Shiiiiiiiiiiiiii yace mata da bakinshi tare da jan hannunta da ƙarfi ya fitar da ita har zuwa soro.
Abakin ƙofar waje ta kuma takurewa tare da tsayawa waje ɗaya alamun bazata bishi ba.
"Karki ɓatamin lokaci wallahi in baki shige mun tafiba ranki ze ɓaci,Wayace ki zaɓi aurena shasha sha kawai".
Hawayene ya zubo mata cike da tsoro ta bi bayanshi tana ayyana shikenan tayi bankwana da gidansu tayi bankwana da mamanta da Æ´an biyunta, abakin kofar gida ta kifa kanta tana cigaba da kukan datake yi.
Ganin yayi tafiyarshi ya barta a wajan yasa tabi bayanshi salo salo kamar wadda ƙwai ya fashewa acikinta,tana ayyana Allah sarki sadiya ko sallama basuyi ba.
Lokacin data ƙarasa gaban mota usman yana wajan driver yama tada motar su kawai yake jira, azuciye Aliyu ya buɗe motar ya shige yabarta awajan cikin sakin fuska usman ya leƙo da kanshi.
"Ƙanwata buɗe gidan baya mu wuce kinji daina kuka zan ɗauko mama na kawo maki ita har gida".
Cike da sauri ta balle marufin ta shiga tana gyara hijabinta, domin batada zaɓin daya wuce haka sabida tariga tasan ƙaddarar aurenta ce tazo mata da hakan, duk da karancin shekarunta amman tasan kaddara kuma tana yarda da ita sabida gwajin imanin bayi ce.
Cikin nutsuwa yay revars tare da jan motar ya fita daga cikin layin da ita,lokacin gari yay tsit sabida taran darema ta wuce gakuma walƙiya da akeyi sosai iska mai ƙura tana kaɗawa alamun hadarin garin gab yake da zubar da ruwa, kasancewar garin yanayin damuna ne.
Tafiyar mintuna goma daga layinsu bebi zuwa kan titi usman yay, lokacin da motar xata bar layin seda bebi tai kuka harda shashsheƙa,tana jin missing ɗin anguwarsu har wajan gawayin shahid ta kalla tana share hawayenta.
"Yanzu kai abinda kaimin tsakanin ka da girman ALLAH kayimin adalci kenan?".
Aliyu ya faɗa cikin ƙasa da murya wadd ta shaƙe kamar zeyi kuka!.
Cikin sauri usman ya kunna redion motar sabida bayason Bebi taji abinda zasu faÉ—i.
Ware redion yay da ƙarfi yana tukinshi batare daya tankawa Aliyun ba.
"Adalcin kenan kuma bana shakka sabida alkairi na ƙulla ba sharri ba, sannan kuma da sannu zakazo min da buhun godiya nan bada jimawa ba".
Cikin ƙufula ya kuma duban usman a karo na biyu.
"Daman haka zakace man, sabida kai kasan baka cikin case tayaya zan dubi abba nace masa nayi aure bai sani ba? tayaya zan fuskanci ammi, dan Allah kai akaran kanka kayimin adalci kenan kariga ka sakani acikin sarƙa wadda batada mabuɗi".
Dariya usman yay har yana dukan sitiyarin motar shi sannan ya kalli Aliyu wanda yake faman sababi yana jin ransa yakai ƙololuwar ƙarshe a ɓaci sannan yace.
"Karka damu mai afkuwa ta riga ta afku sedai muyi maku fatan addu'a ALLAH ya kawo ƙazantar ɗaki, haba ƙanina ka tambayeni shawara tare da hanyar warwareta nikuma naga wannan auren shi kaɗaine masalaha sabida ceton maraici kagafa in suka mata auren nan sun cuceta kuma kanada kamasho tunda kaine sila, Yanxu ko daka aureta ai magana ta ƙare, nina san abba yasan ciwon haihuwa baze taɓa cewa ka rabu da ita ba koda yay faɗan ma na lokacine amman ze huce, amman duk da haka yanzu zamu soma kaita wajan ammi semuji mizata ce".
Tunma kafin usman ya idda numfashinsa Aliyu ya kuma cafke maganar usman cikin hargagi da masifar dake ranshi wadda yake dannewa.
"Miya ruwanka dani, danna zo maka da shawara ina ruwanka da haɗani aure da ita ina ruwanka da shiga hurumina wallahi nai dana sanin gaya maka halin danake ciki kuma wallahi bada ban ƙimar wancan dattijon ba wallahi dase na saketa sedai kai ka aureta".
Ta inda yake shiga bata nan yake fitaba baƙaramin tsoro hakan ya bawa usman ba baitaɓa tunanin ƙanin nashi nada faɗa irin hakaba har suka ƙarasa gida yana masifa kamar ze ari baki.
Harda cewa usman ya cuce shi yaje ya auro masa ƴar cikinshi ko uban me ze ɗauka ajikinta oho yarinyar da ko wankan tsarki ƙilanma bata iya ba masifa tijara babu irin wadda baiyi a motarnan ba wanda har tsoro seda ya tsirgawa usman.
Inda Allah ma ya taimaka sun kunna redio yana da tabbacin bebin bazataji maganar dasuke ba ammn yasan inda taji abinda ALIN ke faÉ—a seta fishi shiga halin tsorata da zulumi.
Bai bar usman ya ƙarasa parking ba ya ɓalle marufin motar ya fice azuciye.
Cikin rawar jiki shima usman É—in ya balle nasa side É—in yabishi seda usman ya haÉ—a da gudu sabida Aliyu badai sauriba, yana ayyana yau na É—ebo ruwan dafa kaina
Hannu ya saka ya janyo kafaɗun Aliyu wanda harya kusan kaiwa ƙofar part ɗinshi.
Yadda kalar idanunshi suka sauya launin kala yay matuƙar razana usman sabida sunyi wani irin girma tare da ja kamar gauta wanda ko ba,a faɗa maka ba kasan yana cikin tsananin damuwa da fushi.
Sanin kanshine in Aliyu na cikin fushi ko ammi bata kulashi harse ya sauka, dan haka cikin sanyin jiki usman ya saki kafaÉ—un sa tare da komawa wajan motar ya rabu dashi har zuwa gobe.
Tsaki yaja da ƙarfi tare da banko gate ɗinshi ya shige batare dako ya juya wajan usman ɗin ba.
Yana son ko a iya wannan daren ne ya nunawa usman kuskurenshi na wannan shiga hanci da ƙudundunen daya masa wanda baƙaramin haushi usman ɗin ya bashi ba.
Haka ya ƙarasa cikin part ɗinshi azuciye kota kan ɗakin dija bai biba ya haura ɗakinshi ya faɗa saman gadonshi yana dafe kanshi dake barazanar tarwatse mashi bai shirya haɗa maganar daze fuskanci ammi ba, yana son dogon tunani da nazari kafin ya ƙaddamar da komai, zumbur ya miƙe zuwa gaban frij ɗin dake manne cikin ɗakin nashi budewa yay tare da ɗaukar gorar ruwan faro mai sanyi ya kafa a makoshinsa wanda ya bushe ƙaraf babu ko alamun miyau acikinshi seda ya shanye tass ya wurgar da gorar ya kuma ɗaukar wata ya shanye tass sannan ya mike yana rangaji kamar ɗan maye ya kuma faɗawa gadonshi ya shiga duniyar tunanin mafita?
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.