Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 51 of 81

Cikin ƙayataccen room ɗinshi ya shiga system ɗinshi  ya ɗauko ya zauna akan sopa ya ɗorata akan cinyarshi yana duba aikin kamfaninshi na tokarawa, wanda insha Allah next mounth yake tunanin buɗeshi yanzu abubuwan dasuka rage mashi kaɗanne amman kafin nan yana son fita waje sabida shigo da wasu kayan, dan haka yake son komai ya kammala cikin next week insha Allah, ranar friday ma yakeson shiga can ɗin inyaso inya gama komai se yay zancen viza  maganar dasuka gama yi da abbanshi ɗazu kenan.
Har aka kira magariba yana zaune, seda aka kusan tayarwa sannan ya aje system É—in bayan ya kasheta ya shiga bathroom ya dauro alwala ya É—auki wayarshi ya fice daga É—akin.
Seda ya karasa room É—in dija yace mata ta tashi tai sallah sannan ya fita, wannan karonma ta bishi ta fesa masa turare sannan tai mashi adawo lafiya kana ta koma É—akinta.
Masallaci ya nufa wanda cikin lokaci ƙalilan aka tayar da sallar, suna idarwa ya zauna cikin masallacin ya gabatar da azkar ɗinshi sannan ya soma lazimi.
Har akayi sallar isha'i yana zaune seda aka kira sallah aka idar sannan ya fito.
Kusan atare suka jero shida ya abbakar a harabar gidan suka tsaya suna hirarrakinsu akan maganar sabon kamfanin da Aliyun yakeson buÉ—ewa.
Cikin barkwanci ya abbakar yake cewa Aliyun.
"A,a kaifa ƙaninnan nawa duniyar tai maka kyau ga amarya ga sabon kamfani sauran sabuwar mota, koda yake kai yanzu aiko jirgi zaka iya siya ba mota ba kana lokaci kaninmu".
YafaÉ—a yana dukan gefen kafaÉ—unshi.
Cikin mamaki ya dubi ya abbakar yana yamutse fuska amarya kuma?yana mamakin jin hakan seda ya tuna da batun dija sannan ya saki murmushi batare dayace komaiba.
Wayarshi dake cikin jeans É—inshi ita ta soma ringing lokacin kusan takwas takusama.
Da sauri ya fito da ita lokacin ne kuma ya abbakar yay mashi sallama ya wuce nashi part É—in.
Ganin usman ke mashi wayarsa yasa ya É—anja tsuka kaÉ—an yana karawa a kunnenshi.
"Ango kana ina haka?".
YafaÉ—a daga cikin wayar cike da zolaya.
"Kai ni banson wannan suna faÉ—i matsalarka malam"
Dariya usman yay yana ayyana nai maka tarko dan ubanka amman a fili seyace.
"Ina tambayarka kana ina haka?"
"Ina compound amman inka kara minti É—aya baka karasoba zan koma gida sabida ina da uzirin dake gabana".
Tun kafin ya katse wayar yaga usman agabanshi kamarma wanda yayi gudu".
Murmushi ya saki yana miƙawa usman ɗin hannu sukai musabaha sannan yace mai.
"Lafiya kira da wannan tsakar daren" yana ɗage girarshi ta ƙasa.
Dariya usman yay Æ´ar kaÉ—an sannan yace.
"Nazo kamin rakiya dan darajar Allah kada kacemin A,a kaji ɗan ƙanina".
Yafaɗi yana haɗe hannayenshi alamun roƙo.
Shafa sumar kanshi yay wadda bata cika yawaba tare da kallon usman.
"Amman gaskiya banson mujima kamar rannan sabida kaga yanayin garin ana walƙiya kuma kasan bana son dukan ruwa zazzaɓi kesani".
Murmushi usman yay yana kaÉ—a keyn motar hannunshi sannan ya kalli Aliyun.
"Karka damu amman pls ka sauya kayan jikinka kasaka manya dan ALLAH".
Wani wawan kallo yay mashi.
"Kasan girman Allah bafa zan sauyaba sabida ba zance zaniba kuma ba surukai zanje ganiba in shigata batai maka ba sedai ka hakura da rakiyar tawa kai tafiyarka".
Cikin sauri usman yace.
"Wane mutum naƙi kabini maza muje hakan ai jallabiya cema".
Bai maganaba se jan kafafunshi dayay suka nufi parking space.
Wata white honda accourd 016, mai black tinted windows,suka nufa usman ya shiga driver site shikuma Aliyu ya shiga emty site na kusa da driver cikin sauri usman ya fisgi motar ya nufi gate yana danna uban horn.
"Kaga malam akan gidan masu dambu wallahi baxaka zubar daniba in kasan wannan ɗanyen gudun zakai sena sauka haba wannan gida in zakaje kullum jikinka yana rawa kamar ka taka ƙulli a ƙofar gidan".
Usman yana jinshi yana kunshe dariya yasan duk sanadin zamewa yake nema shiyasa yay mashi tsitt yabarshi akan insun je can ɗin ayita ta ƙare.............

*TOFA ANZO WAJAN! INNAGA RUWAN COMMENTS ZANYI KOKARIN BAYARDA 71 AKAN KARI INSHA ALLAH*

💃💃💃💃💃 Haɗuwar gadanga da bebi! #team dija how market😛😛😜
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

                                *71*

"Ni zaka mayar mahaukaci,ina maka magana kaimin banza sabida ka É—aukeni ban san minakeyi bako?".
Aliyu ya dubi usman wanda hankalinshi ke kan driving yake gaya mishi hakan.
"To yaya kakeson nace maka? cewafa kayi na taka ƙulli yau kuwa zakaga na taka ƙulli ganin idanunka".
Usman ya faɗa yana dariya,Tsaki yaɗanja kaɗan tare da fiddo da wayarshi yana neman layin Alhaji aminu abokin business ɗinshi, ringing ɗaya Alhaji aminun ya ɗauki wayar Gaisawa sukai ya soma yi mashi bayani akan harkokinsu wanda har suka ƙarasa unguwar su Bebi bai daina wayarba har seda usman ya shiga cikin layin sannan ya kashe motar ya zubawa Aliyun idanu tare da jiran ya gama wayar su shiga cikin gidan.
Sun kai kimanin mintuna goma acikin motar usman yana faman jiranshi agogon dake hannunshi ya kalla tara saura na dare.
Alokacin shikuma ya kammala wayar yana ajeta cikin aljihun wondonshi sannan ya dubi usman É—in.
"Kaje ka fito ina nan ni kasan babu inda zan bika".
HaÉ—e hannaye usman yayi kamar ze zuba ihu sannan ya dubi Aliyun.
"Haba angon dija kaiwa girman Allah kazo muje kaga inna ga idanunka bazan zauna kamar rannan ba musamman in kana zabgomin harara da idanunka".
Shi dariyama usman ɗin ya bashi amman dayake wanda ya rigaka kwana tofa seya rigaka wayo seda usman yasan yadda yayi ya ribace shi ya fito yana mita suka ƙarasa ƙofar gidan agarin saurima seda Aliyu ya ƙume da ƙofar gidan, yana ayyana insha Allah ze taimaka masu a gyara musu gidan dan ƙofar kaɗai ma se taima mutum illah.
Daga bakin ƙofa usman yaɗan dakata tare da ɗaga murya kaɗan yay sallama.
Mama dake sauraran malam wanda ke mata bayani akan mahaifinsu Aliyu, ita tai saurin amsa sallamar kuma atake anan taji sanyi ya ratsa mata zuciyarta sabida tun É—azu acikin zuciyarta zulumin yadda mijin Bebi yay biris da zuwan take.
Cikin sauri ta É—auko babbar tabarma ta baje a tsakar gidan akusa da malam sannan ta gyara mayafinta wanda ya kuma haskata sannan ya fito mata da ainihin kyawunta na hausa fulanin Usul.
Usman ke gaba Aliyu na bayanshi, Cikin nutsuwa suka ƙarasa cikin gidan zama sukai akan tabarma da mama ta shinfiɗa musu.
Cikin lkunya usman ya gaisar da malam tare da mama, Shiko Aliyu ko ajikinshi cikin sakin jiki ya gaisar dasu duka biyun yana duban malam.
"Niko baba kamar naso gane fuskar nan wallahi?"
Cewar Aliyu yana É—an nazarin inda yasan malam lado.
Shima malam se a sannan ya dubi Aliyu da kyau sannan yace.
"Lah kar dai wannan yaron ne wanda kataɓa kawoni gida kwanakin baya bani da lafiya ina titi ka ganni a zaune ka tsaya ka ɗaukoni harka bani kuɗi aiko na ganeka ɗan kirki".
Murmushi Aliyu yay.
"Allah sarki baba nine naso sake komowa na ganka kuma senai tafiya Allah bai nufa ba se yau".
YafaÉ—a yana kallon malam.
"Masha Allah hakan ma nagode sosai in wanine ma ai baze kalleka ba".
Sannan ya juya yana kallon mama wadda kanta ke sunkuye.
"Wato Aishatu na jima banga yaron arziƙi mai tausayi irin wannan bawan ALLAH ba, kwanakin baya naje kasuwa wajan wani abokinmu, zan masa ta,aziya wallahi bayan na dawo se ciwon kai da kumallo ya kamani a hanya sena zauna bakin wata bishiya ina dafe kaina, sabida juwar data kamani kawai senaga wannan yaro akaina yay min sallama cikin nutsuwa , yana tambayata baba mai yake damunka haka, sena ɗago nace masa kaina ke ciwo da kuma juwa wallahi aisha bakiga yadda ɗannan ya damuba da kanshi ya ɗagoni ya sakani amotarshi yacemin ze kaini asibiti a dubani abani magani nace masa yabari innaje gida inada maganina, kinsan seda ya kawoni har bakin layin gidana sannan ya ɗauki dubu ashirin ya bani, wato Aisha wannan yaro ɗan arzikine, amman yanzu na daina mamakin alkairinsa tunda bai ɗauka abanza ba jinin alhaji idirisa ai dole ya gaji alkairi".
YafaÉ—a yana kallon Aliyun da yabawa.
Shiko ko ɗago kanshi bai ba amman yana mamakin yadda har yau mutumin bai manta yadda akaiba  lokacin shima ya dawo daga office ne lamarin ya faru, shaff ya kuma mance, da batun seda yaga fuskar tsohon sannan ya shaida shi kuma abin ya faɗo masa.
"Wallahi kam baba maganarka haka take Allah bamu dacewa kawai".
Cewar usman yana kallon malam danshi bai mamaki ba sabida kowa a gidansu yasan Aliyu akwai tausayi duk zafinshi yana da mugun tausayi aranshi.
"Masha Allah baba gwara da Allah yasa muka sameka anan ɗin kaga base munje can ba gashi na kawo maka baba seka damƙa masa amana".
Dariya malam yay yana kallon usman tare da cewa.
"Aiko ni ko birnin sin wannan yaro ze tafi da balki wallahi ban damu ba sabida tun kafin nasan shine na yaba bare kuma da Allah ya haÉ—ani dashi na ganeshi kasan wannan shi ake kira da ka gina alkairi a baya domin ka girbi abinka agaba".
"To malam Aliyu ya kamata ka É—ago ka fuskance ni sosai tare da kunnen basira".
Cewar malam yana kallon fuskar Ali.wadda take can gefe guda.
Cikin nutsuwa kamala haiba Aliyu ya juyo yana kallon malam kacokan ya basa dukkan nutsuwar shi, aranshi yana mamakin komai ya kawo hakan oho?.
"Da farko dai Malam Aliyu ni dakaina da kuma wannan baiwar Allah".
Ya nuna mama da hannunshi.
Sannan ya cigaba.
"Muna miƙo buhun godiya wajanka da kuma yi maka addu,ar mai yawa mai albarka, yadda kai mana Allah yay maka yadda ka taimaki maraici ka rufa masa asiri kaima Allah ya duba bayanka kada ya wofantar dasu, naji abin alkairi a wajan ɗan uwanka abubakar da kuma usman mungode mungode"!!
Zaro manyan idanunshi waje yay waɗanda suka ƙara haska masa kyawunshi.
*WANNAN LITTAFI NA KUÆŠINE KADA KI KARANTA BAKI BIYABA NAIRA 200 BABU YAWA IN KINA BUƘATARSA TUN TUÆI WANNAN LAMBAR KAI TSAYE 08142105218*
Tare da kuma matukar mamakin mai yay masu haka suke masa godiyar data saka jikinshi yay sanyi.
"Aliyu ga amanar bilkisu nan mun baka har abada babu janyewa mun baka bilkisu kamar yadda ka buƙata kuma mun cika maka kudirinka na ɗaura muku aure ayau kamar yadda ka bukata harka turo mana usmanu da abubakar sabida haka yanzu muna jiran ta bakinka domin bama fatan balki ta kuma kwanar mana agida se agidan mijinta"
Cikin sauri usman ya tari numfashin malam.
"Ai malam wannan lamarin yay mana daɗi sosai Allah dai ya ƙara girma dayake shima ɗin yau kwananshi uku da yin auren farko amman duk da haka babu damuwa insha Allah zamu san abinyi sabida hakama bama bukatar komai naku Bebi kawai muke buƙata".
Wannan kalamin  na usman sune suka saka Ali ya farga ga batun nasu.
Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un hasbinallahu wani'imal'wakil!
Tabbas inba ƙarya kunnenshi yay mashiba usman yazo tare da abubakar yayansu sun karɓa masa auren wannan yarinya batare da saninshi ba.
Gumine ya soma fito masa ta saman goshinsa batare daya shiryaba.
Maganar mama ita takuma katse masa tunaninshi.
"Ni mahaifiyar Bebi ce nasan komai daga cikin halinta ina rokonka daka riken bebi amana intai ba dai dai ba ka hukunta min ita inda hali ka sakata a makaranta domin ta sami zurfin ilimi ko ze saka ta daina wannan shirmen nata nagode nagode................

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.