Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 10 of 86
Ido Goggo Dada ta zuba musu ganin yadda Aminullah ya tsare Mahmoud É—in da magiya.
“Please a im begging you Mahmoud ka shirya kaje mana Turkey Nan, ba wani daÉ—ewa zaka yi a can bafa dudu bazaka wuce one month bafaâ€.
Ba tare da ya kalleshi ba yace.
“Ba zan jeba, kai kaje manaâ€.
Cikin sanyi yace.
“Ka sani bana son weather É—in su na yanzu, kasan cutar dani yakeyiâ€.
Gyara zama yayi tare da jawo plate É—in chips ya É—an zuba ketchup tare da fara ci yana É—an Sipping black tea É—in da yasha haÉ—in na musamman.
Goggo Dada ce ta ƙarɓi Zaitoon da Fariyda ke miƙa mata tare da cewa.
“Kayi haƙuri mana Babana kaje tunda ba jimawa zaka yi ba.
Sannan kasan shi baya son sanyi yanzu kuma lokacin sanyin nasune ka saniâ€.
Cikin isa Fariyda ta É—an juya tare da kallon Aminullah É—in cikin sanyi tace.
“Ai ma babu inda zaije a yanzun nan kam.â€
Tayi mgnar tare da juyawa ta nufi kitchen cike da takaicin yadda sanyin halin Aminullah yasa ƙaninsa ke juyasa.
Shi kuwa Mahmoud wani dogon tsaki mai cike da hatsala yayi tare da cewa.
“Kinji ko Goggo Dada ai ga Æ™anwar uwarsa ta yanke hukuncin ba inda zaije, ai dama na sani wannan naci da magiya duka so yake ya mata biyayya ne ya mata yadda take sone, ita yar iyayin me yasa zata sa mana baki a mgnarmu ni da É—an uwanaâ€.
Ya ƙare maganar yana cusa chips ɗin a bakinsa.
Ita kuwa Fariyda a kitchen ta samu Ummi tsaye tana duba danderun da take haÉ—a Mahmoud É—in wanda duk babu jan mana ko tsoka É—aya, duk na jijijiyane irin farare nennan masu tauri da dango, amman sabuda wuta da suka sha da kekkyawan aiki yasa sukayi lug dai-dai ci ga wanda yasan yadda zai iya cin su cikin mgnar zuci tace.
“Shi ko tausayinsa ma bayayi, yasan baya son weather É—in can Amman rashin tausayi yasa yake nuna dole sai shi É—in yajeâ€.
Da sauri Ummi ta kalleta tare da cewa.
“Mahmuod ko?â€.
Da sauri ta É—an jujjuya kai alamar a'a.
Ta gane sarai shi É—in ne kwaffa tayi tare da ci gaba da aiki tana mai gyara goyon da tayiwa Zaid dan rikicinsa da ya tsaannan a kwanakin nan.
Aunty Amina ce zaune da yaranta cikin bada umarni tace.
“In Allah ya kai mu jibi zamuje gida.
Wunin Æ™arshen wata, Hafiza tun gobe zamu shiga kitchen dan ina so in É—an har-hardada Mahmoud snacks da É—an dama ko Ummi zata É—an huta kwana biyuâ€.
kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
“In sha Allah, jiyama da naje naji yana cewa ai masa danderu kinga sai muyi masa koâ€.
Tana miƙewa tsaye tace.
“Ai tunda yace a masa nasan Ummi zatayi masa, zan dai masa dambu da pepper chickenâ€.
A hankali ya jawota jikinsa cikin lumshe idanunsa yace.
“Hmmm Oum Zaitoon Mahmoud fa ya fini shan wahalar kula da kasuwancinmu, ko ba komai ni ko yaushe ina gida, zanci duk abinda nakeso zanyi bacci cikin gamsuwa ta, shifa mafi akasarin rayuwarsa yana zirga-zirga tsakanin Æ™asashen duniya da muke kasuwanci dasu shiyasa yace ya gaji kinga fa bai wuce wata biyar ba dawo Chaina a can yayi kusan wata uku, daya dawo hutun wata É—aya yayi na turasa Italy yanzu watanshi É—aya ne da dawowa nake son turashi Istanbul, in dai kinga ya kafe min kan abufa to ya gaji neâ€.
Gyara kwanciyarta tayi bisa ƙirjinsa cikin danne abinda takeji kan ɗan uwan nasa na tsananin tsana mai cin rai tace.
“Ka sani bana son nesanta da kai! Ina kuma jin tsoron yanayin can kada ya cutar da kai, sannan kuma ai shine ƙarami, sake mishi da kakeyi fa yana yawa.
Ta yaya zaka bari yafi Æ™arfin ka tanÆ™warashiâ€.
“Hmmm, bazaki gane bane, shimafa yana buÆ™atar hutu, dukiyar nan fa da akewa hidima wake da yaranki yake yiwa, tunda shi iya kar abinda shi ya amfana dashi ne kaÉ—ai rabonsa, bazaki gane cewa cutar dashi nakeyi ma da dukiyar da ba wani morarta yake yi ba kuma ko a gaba ba wani morarta zaiba tunda rayuwarsa shi kaÉ—ai É—insa neâ€.
Da sauri tace.
“Hmmm Yah Amin kenan, motocin da Mahmoud ke hawafa sunfi naka tsada, suturar da yake sawa ko Abba baya sa masu tsadarsa bare kaiâ€.
Graya blanket É—in da suke ciki yayi da kyau tare da yiwa kanshi Garkuwa da É—umin jikinta da blanket É—in wa sanyin AC da suka É—an kunna.
“Bazaki gane bane Oum Zaitoon Mahmoud fa iyakar abinda ya amfana a jikinsa kansa rayuwarsane kawai, ba mata ba É—a bare aje ga jika. Hidimar fa da wahalar duk mu yakeyiwaâ€.
Zuba mishi ido tayi ganin lips É—insa da suke É—an rawa alamun rawan sanyi ne yasa tace.
“Gafa É—an sanyin Ac nan da bai taka kara ya karyaba, duk jikinka tsuma yake yi, inaga in Istanbul kake. Nifa lafiyarkace damuwata, shi tunda bashi da wani uzuri ai sai yajeâ€.
Murmushi yayi tare da lakace mata hanci yace.
“Ni wai yaushe kika zama hakane!â€.
Lips É—inta ta É—an tura tare da cewa.
“Darasinka ne aiâ€.
Ta ƙare maganar dasa hannu ya zaro remote ɗin Ac ta kashe shi.
Zaune yake a dinnin area a ƙasa gefen dinnin table ɗin kan wani tattausan carpert dake shimfiɗe a wurin, ya ɗan kishin gida da tum-tum dake wurin wanda hakan ya bashi damar fuskantar laptop nashi da kyau.
Kayayyakin da suke buƙata a Gombe, Zamfara, Logos, Taraba, yake duba list ɗin da duk MD ɗinsu nacan suka turo musu.
Numfashi ya É—an fesar tare da lumshe gajiyayyun idanunsa,
Sai kuma ya ɗan ja gajeren tsaki saboda surutun da baƙin gidan nasu da mutanen gida keyi ya ɗan fara hawa mishi kai.
Dariyar Aunty Amina ne yasashi É—an tsagaita wa da aikin da yake yi É—in tare da É—an maida hankalinsa kan hirar tasu.
“In dai Mahmoud bai ne sha mai kaiba ya gwaleki duk wannan uban hidimar da kika yi masaâ€.
Cewar Fariyda da take bubbuɗe Wormas ɗin da ke jere a parlour da kuma wasu snackle box guda biyu masu ɗan girma da kyau, ɗayan ta jawo gabanta tare da kallon yadda Aunty Amina ta shirya masa ƙwalama a ciki alkaki ne a bowl ɗin forko sai wardi a na biyun ɗayan kuma riɗi mai sugur ne a ciki sai na tsakiyar kuma kwakumeti ne mai kyau. Kwakumetin ta ɗan ɗiba kaɗan tasa a baki tare da lumshe ido dan garɗinsa.
Sai kuma ta jawo É—ayan ta buÉ—e wanda ya É—anfi girma dan shi box É—insa 4 ne.
Spirin roll ne ana forkon sai meat per a na kusa dashi sai kuma dayan soyayya namana ragone, sai na tsakiyar kuma samun naman kazane da yayi masifar kyau da taushin.
Hafiza ce ta É—an kalli Fariyda tare da cewa.
Aunty Fariy karfa yaga ansa hannu wlh bazai cibaâ€.
Kai ta É—an juyo ta kalli Hafiza tare da cewa.
“To kar yaci man ai dama ba iya shi kaÉ—ai akayi waba ko?â€.
Da sauri Ummi tace. “Sosai ma kuwaâ€.
Tayi magnar tana kallon Aunty Amina data amshi zancen da cewa.
“Amman wannan na box ɗin dai nasane shi kaɗai kun sanshi.
Ga naku a leda na ƙullo muku komai.
Sai abinci kuma yau na hutar da kene Aunty Fariyda kema karki shiga kitchen ki huta musha hira kawai shi yasa nazo da wuri maâ€.
Aminullah ne ya buÉ—e Worma dake gabanshi.
Kai É—an juya ya kalli Fariyda tare da cewa.
“Ke kin tsayawa kwalamar Mahmoud gama abinda ya kamata kiyi happy dashi, ni É—auko plate ki samin pepper chicken nan naga da zafinsaâ€.
Murmushi tayi tare da cewa to kana ta miƙe ta nufi kitchen.
Hafiza kuwa kan dinnin table taje ta shirya duk na Mahmoud, saida ta juya zata bar wurin ne ta lura dashi, cikin sanyi tace.
“Afwan Our Uncleâ€.
Hannu ya É—aga mata alamun tayi shiru taje kawai.
A parlour kuwa Hafiz ne ya kalli Aminullah gefenshi ya matso tare da cewa.
“Uncle na gayawa Momynmu fa batun haÉ—awa Uncle Mahmoud birthday É—in bazataâ€.
Kai ya gyaÉ—a mishi tare da cewa.
“Ai ta kirani munyi mgna da ita jiya, tace in bar mata aikin komai ita zatayiâ€.
Fariyda na zama a gefenshi ta kalli Samira dake cewa.
“Shekara nawa ma zai cika?â€.
Goggo Dada dake amsar plate ɗin pepper chicken da Fariyda ke miƙo matane tace.
“Zai cika 30 ne ai ko?â€.
Tayi magnar da alamun tambayar Ummi.
Ido Fariyda ta É—an fitar tare da cewa.
“Kai Goggo Dada ya kamar kina Æ™arawa yaron nan shekaru ne, naga yanzu nema zai cika 28 ne ko 29â€.
Kai Aminullah ya jujjuya tare da cewa.
“Kar ya jikifaâ€.
Murmushi Ummi tayi cike da son surkar tata dake miƙa mata bowl ɗin data zuba mata dambun nama tace.
“To in ya jita ma ai yayarsa ce dan ta faÉ—i haka ba laifi baneâ€.
Samira ce ta ɗanyi ƙasa da kai tare da cewa.
“Tab wlh kada dai ta bari yaji tana ce mai yaroâ€.
Miƙewa Fariyda tayi ta nufu hanyar fita tana faɗin.
“Ummi bari in É—auko snacks box a kitchen na, in kawo a sawa Abba nasa a cikiâ€.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.