Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 76 of 86
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAR MAKAFI*
Page 38
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Maida kanshi yayi ta inda take wayam ya gani dan tuni ta bar wurin sai shigarta É—aki ya hanga.
Washe gari da yamma. Lekme salon surdhara, zaune yake yana riƙe da waya, yana ɗan riƙe da hannun Zaid da ake gyarawa kai, bayan an gama masa nasa gyaran wanda akayiwa Zaid ɗin irin nasa. Cikin gamsuwa da shawar zuciyarsa yake sauraron Sa'ad dake koro mishi jawabin yanayin da yake ciki na rashin waya da Fariyda da yadda mahaifiyarsa ma ta karɓi magnar ya ɗaura da cewa.
“In ka amince min zan zo Ahmedabad É—in Yah Mahmoud dan ina son ganinta, ina son mu fahimci juna, dan magabatana suje ga naku magabatanâ€. Cikin tsaida magna yace.
“Ba matsala Sa'ad zaka iya zuwa, batun magabata kuma, kada ka damu nine mai aurar da ita, batun neman izini kuma akwai Bappanmu a Gombe zan baka number É—an uwana Sulaiman shi zai muku jagoro shi Bappa namu shine mai zantarwa dan dama ko yayana na raye shine mai yin komai dan bamu da kamarsa, ka zo kawai ku dai dai ta ba matsalaâ€. Cikin farin ciki Sa'ad yace. “In sha Allah ranar Saturday da safe zanzo kuma zan gayawa Bappana duk yadda mukayiâ€. Daga nan sukayi sallama suna fita side É—in maza ba tare da ya leÆ™a gefen matan ba ya wuce waje da Zaid É—in a bakin kujerun dake wurin ya zauna yana kallon wayar Yah Amin É—in da kiran Salim ya shigo, katse kiran yayi tare da zura wayar a aljihunsa, miÆ™ewa yayi ya É—an leÆ™a gefen matan. Dai-dai lokacin aka gamawa Fariyda gyaran kai É—in dan da Zaitoon aka fara har kitso akayi mata. Dogon gashin da mai salon É—in ke naÉ—e matashi ya É—an kalla a fakaice kana ya janye idonsa ya kama hannun Zaitoon suka fita, suna fita ba É—aÉ—ewa ta fito suka wuce masauÆ™insu.
A parlour ya zauna da sauke su Zaid dake kafaÉ—arsa, ba tare da ya kalli inda takeba yace.
“Ke zo nanâ€. Yi tayi kamar bata jisaba taci gaba da tafiyarya dan so take taje tayi wanka tsarki dan shirin yin sallan magrib, da sauri ta tsaya saboda jin yadda yayi mata magnar da wata iriyar muryar bada umurnin da dole yasata juyowa. "Zo nanâ€. Ya faÉ—a yana nuna mata wurin zama a Æ™asa.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Ganiâ€.
Ƙasa ya kuma nuna mata da hannunsa. Kan hannun kujera ta zauna tare da cewa. “me nene?â€. Cikin daÆ™ilelliyar murya yace.
“Ni mata É—inki ne, ina sama kina sama, sauÆ™a Æ™asa ko in É“alla Æ™afarâ€. Da sauri ta zame Æ™asa dan ta lura É“alla mutum baya masa wuya yanzu zai iya É“allatan. Cikin Muryar girma irin wacce uba yakewa yayansa magna da ita da tsaida kalamansa cikin bada umarni yace.
“Mun gama magna da wannan yaron Sa'ad na bashi izinin fara zuwa, jebi zaizo ku dai-daita, zan datse igiyar da su Abba suka Æ™ulla a tsakaninmu, kin kma san bana so, ba kuma zan soba har gaban abadan tunda kin dai san na tsaneki ai ko?â€.
Ya dire mgnar tare da kafeta da ido,
Itama É—in idon ta zuba mishi cikin yanayin tsiwa.
Ido cike da isa yaci gaba da cewa.
“Kin san bana sonki! na tsaneki!! Bana son ko ganinki!!! dan haka zan aura masa ke dan shi yace yana sonkiâ€.
Miƙewa tsaye tayi har lau idanta na kanshi cikin wani irin kallon mai cike da takaici da baƙin cikin aura mata shi da iyayensu sukayi tace.
“Sai ka bari ranar da ka da Zaitoon ta girma kayi mata wannan umarni tabi, bani nan Fariyda ba ni ai nima É—in dole aka min da kai da babu É—aya neâ€. Da sauri shima ya miÆ™e tsaye tare da cewa. “Ke gata zan miki fa in rufa miki asiri in aura masa ke tunda shi mayen mataneâ€. Wani irin kallo mai cike da baÆ™in ciki tai masa kana tace. “Ni dama asirina a rufe yake, banyi lalacewar da kai zaka aurar da niba, ina da iyayen da suka isa dani, kuma ina da masoyan da zasu iya bada rayuwarsu a kainaâ€. Cikin tsuÆ™e fuska yace. “Shima wannan banzan ai zai iya bada ransa a kanki, ina sone muyi abun a sirri, shiyasa dan in su Abba suka sani da Baba Malam bazasu aminceba, zasuci gaba da tirsasamana zama da juna, dan haka weekend É—in nan zai zoâ€. ÆŠaukar su Zaid tayi ta Juyawa ta nufi bedroom ba tare da tace mai komai ba.
Wanka tayi musu bayan ta shiryasu itama ta shiga tayi wanka sabulu kana ta É—aura dana tsarki, cikin wasu tattausan riga da wandon pallazo Turkish masu masifar kyau ta shirya.
Ganin lokacin sallan magrib tayi ne yasata shimfiÉ—a sallaya.
Tana kan sallayan bayan ta idar da sallan Isha, ta ji shigowarsa bathroom ya wuce.
Bai fitoba har ta É—auki su Zaid ta wuce Dannin area É—in hotel É—in dan yin dinner.
Yana fitowa ya wuce parlour ya kimtsawa cikin wasu datatstsun suit masu masifar kyau Magenta color mai ɗan karen ƙyalli daga nan ya numfi.
Holl É—in da da ake taron nan ya wuce.
Shiru parlour alamun ya fita, numfashi mai nauyi ta sauƙe tare da shaƙar ni'imtaccen ƙamshi turarensa daya haɗe da sanyin Ac da kuma lumshin dare ya bada ni'imtacciyar isaka ta musamman mai tafe da yanayi mai sauƙaƙawa zuciya tunanin.
Ido ta zubawa yaran ganin sun hau kan 2 seatter sun kwanta.
A hankali ta zare sawunta daga cikin snicker É—in dake sawunta. “Uhmmmmâ€. Ta sauÆ™e numfashi da zira yan sawunta cikin takalmansa dake gefenta, sunkuyo tayi da sauri ta kalli sawun nata tana É—an tattakawa sabida jinta so Comfortable wani laushi da daÉ—i taji takalman sun mata, kai ta jinjina ta wucewa bedroom, rage kayan jikinta tayi ta wuce bathroom ruwa ta watsa kana ta kimtsa cikin riga da wando na bacci masu masifar taushi Pink collar rigar mai haÉ—e da wulace, hannunta ta É—an zura cikin aljuhun gefe da gefen rigar.
Numfashi ta sauƙe ganin tuni su Zaid sunyi bacci, kan gadonsu ta kai su bayan ta canza musu pampers da kaya.
Ƙarfe 10:00 pm aka tashi daga taron. A hankali yake tafiya saƙale da wayarsa a kunne shiru yayi bayan ya gama yiwa Sulaiman ɗan bayanin yadda sukayi da Fariyda, ɗan kallon wayar yayi saboda jin shirun Sulaiman ɗin yayi yawa, kiran bai katseba kuma baiyi mgna ba. Shi kuwa Sulaiman cikin nitsuwa da fara yarda da gakyar mgnar a zuciyar Mahmoud ɗin dan yadda ya mishi bayani ya gamsu har cikin ransa yake son rabuwa da Fariyda.
“Wai bacci kayi ne?â€. Cikin sauke numfashi Sulaiman yace. “Sai kace kai bacci in one minute, idona biyu kawai dai ina tuna ta yadda zamu warware sarkar makafin da su Abba sukayi neâ€.
Yana É—an lumshe gajiyayyun idanunsa yace. “Ai ba wani wuya, kawai kayiwa Bappanka magna, iyayen Sa'ad su zo wurinsa neman aurenta ya bawa É—ansu aurenta. Muna dawowa ta Gombe zamu sauÆ™a sai an É—aura aurenta da Sa'ad sai mu taho kano tare da bappanka ya tayani yi musu bayaniâ€. Cikin É—aurewar Kai Sulaiman yace.
“To amman Mahmoud ya batun lfyarka da Yah Amin ya tabbatar ka warke, kai kuma yanzu kana inkari, sannan ita Fariyda tace ma bata sonka neâ€.
Tsaki mai tsawo yaja tare da cewa.
“Yarinyar da akace ma, suma tayi da taji wai an É—aura mata aure da ni, toma ko tana sona ai ni bana sonta, na tsaneta, kai batama sona bana sonta bazamu taÉ“a son junaba. Kuma zan saketa dan tabbatar da aurenta da Sa'ad É—inâ€. A hankali Sulaiman yace.
“Naji baka sonta bata sonka, to amman ai bata yarda da tsarin karba, ko dole zakayi mataâ€. Cikin isa yace. “Yess ai dole in aurawa wani itaâ€.
Da sauri yace.
“To kai kuma wa zaka aura tunda ka warkeâ€.
Yayi tambayar dan fahimtar gskyar lamarin dan samun yadda zai shigo da mgnar Jidda tunda ya kafe kan sakin Fariyda, hakan yasa yake jin burin Jidda zai cika dan yasan tabbas zai saketan tunda ya furta zaiyi, duk da bai faɗawa Mahmoud ɗin saƙon Jidda ba amman yana shiryawa haka, tunda yanzu dai shi ya kirasa, sai sun tsaida matsaya kan batun Fariyda zai shigar masa da batun Jidda ko zuwa gaba ne. Cikin faɗa yace.
"So nake ka gaya min ya zanyi ta yarda dan in ta yarda abin zaifi zama sirri, duk da ko taÆ™i Wlh sai na mata doleâ€.
A hankali Sulaiman É—in yace. “Ka tausasa mata lafazi, ka nuna mata amfanin auren Sa'ad É—in dunta itama ba sonka takeba, ka bita a hankali ka mu'amalanceta tamkar Wa da Æ™anwa ka daina hantararta da nuna mata isa bare kace mata dole yaran yazu ko iyayensu ai basa musu dole bare kai. Da zaran ta yarda da Sa'ad ni kuma zan baka goyon bayan ayi komai a sirri dan bana fatan kuci gaba da zama a haka kana cutar da itaâ€.
Numfashi mai zafi ya fesar da cewa.
“Ta isa ita uwatace da zan lallaÉ“ataâ€. Da sauri Sulaiman yace.
"Kenan dai baka shirya rabuwa da itaba, Malam in sonta kake ai matarkace kuci gaba da zama kawaiâ€.
Ya ƙare maganar da katse kiran saboda jin wani dogon tsakin da Mahmoud ya ja masa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.