Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 35 of 86

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala 6 ne na sha kala huɗu ne sha da kumu tea jiƙawa dantafasawa, na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki,

idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da basu iya bada tarbiyaba. set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu ina kuma bada sarinsa a farashi mai sauƙi.
Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA

Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba kuyi haƙuri kada kumin mgnar ku bari sai kun shirya,kada kuzo mu ɓatawa juna lokaci Allah y sani bana son mutum yaga na mishi ba dai-dai ba nima Kuma bana so ayi min wasa da hankali a harkar kasuwanci 🙈🤗🤣, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi duka.
🤣😘🤝

Kusan duk a tare sukayi sit tare da miƙewa tsaya suna kasa kunne dukkan jinsu da nitsuwarsu ta koma kan shaidar tabbatuwar ɗaurin Auren Mahmoud da Fariyda.
Murmushi mai cike da farin ciki Goggo Dada tayi tare da É—aga hannunta sama tayi hamdala.
Sai kuma ta kalli Mamy tare da cewa.
“To Alhamdulillah aure dai ya ɗauru Allah Ubangijin talikai ya sanya alkhairi ya basu zaman lfy, yasa auren ya zame mana alkhairi a zuriyarmu baki ɗaya.”
Cikin zubawa Fariyda ido Mamy da Aunty Amarya da Aunty Jamila suka amsa da.
“Allahumma Amin Ya Allah.”
Fariyda kuwa tun kalmar forkon da taji ta zaro dukkan idanunta waje.
Tare da jan dogon numfashi da har yanzu bata direshi ba.
Saddiqa ce ta kalli Adda Nana da ta shigo a guje, da sauri ta riƙo hannun Aunty Amarya tare da cewa.
“Aunty wai me nakeji? Kamar fa wai auren Fariyda aka ɗaura?”.
Cikin zaƙuwa da son ƙarin tabbatarwa Amina, Jidda, Samira, Habiba, Abida, duk suka zubawa Aunty Amarya ido.
“Eh tabbas haka ne Nana auren Fariyda aka ɗaura da Mahmoud ƙanin Aminullah...”
Da sauri duk suka juyo kan Fariyda data ɗaura hannunta bisa ƙirjinta da ya harba da ƙarfi ta sakin wani irin numfashi mai tafe da sautin.
“Innalillahi wa inna'ilaihi raji,un Allahummma ajjirni”.
Sai kuma kawai tayi luuuu ta faɗi kan Goggo Dada a sume”.
Da sauri Goggo Dada ta tallabeta tare da fara jijjigata tana kiranta.
“Fariyda! Fariyda!! Ya Salam Fariyda”.
Da sauri Matar Barrister ta ɓalle marfin goron ruwan sanyi da yake gabanta, tare da fara yayyafa mata.

Mamy kuwa kai ta jinjina ta juyowa tana kallon Salma dasu Raihana da suke bakin ƙofar parlour dan, parlour ya cika ba ta inda zasu shigo.
“Hmmm ai dama na tuna haka”.
Mamy ta faɗa tare da zama gefen Amina da tunda tayi hamdala sai kuma tayi zuru tare da faɗawa tunanuka ta yaya? Ya za'ace anyiwa Mahmoud aure? Bayan sanin asalin aininhin ƙaddarar Mahmoud ta sawon shekaru goma, ta yaya su Abba sukayi wannan haɗin? Yaushe aka tsara haka? Mahmoud ya sani ma kuwa? Wanne irin bahagon aure ne wannan su Abba zasu haɗa? Lallai dan su iyayene a garesu amman da tace basu yi aikin tunani ba! in ma su maza basu saniba ai Ummi da Goggo Dada sun san tsakanin Mahmoud da Fariyda koda bashi da muguwar ƙaddara a rayuwarsa Fariyda dai ba matar aurensa bace har gaban abadan.
Numfashi mai nauyi ta fesar jin su Goggo Dada na hamdalar farfaÉ—owar Fariyda data farfaÉ—o da wani irin maraitaccen kuka mai cike da tsanain tashin hankali mara misaltuwa gami da ruÉ—ani mai haÉ—e da rauni.
Cikin faÉ—a Mamy tace.
“Mutuwa akayi ne da zaki fashe mana da kuka?”.
Kai ta fara jujjuyawa tana dafe da ƙirjinta dake Beating so fast saboda tsananin kaduwa murya a raunace tace.
"Goggo Dada me Aunty Amarya tace?”.
Hannu tasa tana goge mata ruwan da aka feffesa mata tace.
"Kiyi haƙuri Fariyda anyi haka ne domin makomar su Zaid A duk faɗin duniyar nan Mahmoud ne kawai zai aureki ya cike miki dukkan gurbin Aminullah.
Mahmoud ne kaÉ—ai zai aureki ya hana yaranki maraici da amsa kiran sunan agola Mahmoud ne kaÉ—ai zai aureki ya É—auke miki tunanin rashin mijinki.
In sha Allah hakan zai zame muku alkhairi”.
Wani sabon kukan da yasa Salma dasu Saddiqa hawaye ta kuma sakewa tare da kife kanta bisa guiwowin Goggo Dada murya na rawa tace.
“Oh mutuwa me nayi miki, kika ɗauke min dukkan farin cikina na gidan duniya, kika yi sanadin haɗani da baƙin cikin duniya ta inuwar matun mafi tsanuwa a zuciyata.
Wlh bana so, wlh bazan taɓa yin zaman aure dashi ba, na tsaneshi bana san ganin ko fuskarsa ko sunansa bana son ji a cikin rayuwata, Goggo Dada kin sani bana sonshi, na tsaneshi ya tsaneni.
Wlh tallahi na rantse da girman Allah bazan z!!.”
Da sauri ta rumtse idonta jin wani irin marin da Mamy ta yarfa mata.
Aunty Amarya ce tayi saurin riƙe Mamy data yunƙuro da niyar ƙara mata wani marin.
“Kiyi haƙuri Mamy mu tafi part ɗinki kawai wurin baƙinmu”.
Ta ƙare maganar tare da janta suka fita Mamy na faɗin.
“Wlh in kika kuma cewa wani abu ban yafe mikiba Fariyda a gaban ƴar uwarsa da Goggonsa kike faɗin kin tsanesa, to ai Allah da yayisa kam yana sonshi”.
Da haka suka fita.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.