Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 44 of 86
Da sauri duk suka kalli ƙofar parlour jin sallamar Hafiz da shigowar ƙamshin turaren Mahmoud daya ɗebo a parlour sa daga zuwa kiransa.
“Ina yake?”. Hajja inna ta tambaya cikin zaƙuwa, gefen Sadiq ya zauna tare da ƙara juye musu ragowar danderun duka da jawo ledan bread ɗin yana faɗin.
"Yana zuwa”.
Sai kuma ya ƙwalawa Samira kira tare da cewa.
“ Please two cups na tea”.
A hankali ya turo ƙofar ya shiga tare da sallama a kan lips ɗinsa.
Lumshe ido Aunty Jamila da Saddiqa sukayi a tare dan jin ni'imtaccen ƙamshin turaren shi daya bugosu, kasan cewar bai jima daga fitowa wankaba.
Sadik ne ya ɗan zuba mishi ido a hankali yake tafiya cikin ƙwarji, Pajamas ne a jikinsa mai fari da baƙi sai sheƙi da ƙyallin da sajensa keyi ya ƙara ƙawata kekkyawar surarsa da fuskarsa, wani irin ƙamshin da yakeyi mai cike da ni'ima”.
Kanshi ya ɗan juyo yana kallon Hajja inna dake cewa.
“A'a da gani dai wannan ne angon nawa ko, daga ƙamshinsa ma ai na ganesa”.
Fuska ya ƙara tsukewa a ransa yake tunani da yasan ba masu buƙatar taimako bane kamar yadda ya zata da Hafiz yace tsohuwace kuma bai santa ba da bazai sauƙoba, jin abinda ta kuma faɗane ya ƙara tabbatar masa cewa kakar Fariyda ce dake Gembu.
“Zo nan mijin mata biyu yau ai kusa dani zaka zauna”.
Kamar bai jitaba yayi sai kuma ya kalli Ummi dake cewa.
“Bismillah zauna a nan”.
Tai magnar cikin bada umarni mai cike da isa, inda ta nuna masan ya zauna amman gefen Centre table ya ɗan zauna.
“Kakar Fariyda ce da ƙanwar mamanta sai addanta Saddiqa.
Kai ya gyaɗa mata ba tare ya kallesu yace.
“ina yini”.
Murmushi Saddiqa tayi tare da amsawa da lfy ita da Aunty Jamila, dan daga muryarsa zakaji ruwan miskilanci.
“Ni wannan turare naka fa kar yasani mura”.
Har lau bai kalleta bai kuma ce komai ba.
Ummi ne tace.
“Yanzu dai kinga mijin naku ko Hajja Inna”.
Baki ta ɗan taɓe tare da nunashi da bakin tace.
“Fariyda baki bashi tuwo bane, naganshi ba fara'a kin san ance mayunwaci fafaɗa cine”.
Hararan ta inda yake Fariyda tayi ba tare da tace komai ba.
“Yah Mahmoud ina yini”. Sadiq ya faɗa yana kallonsa. “Alhamdulillah”.
Ya amsa a taƙaice.
“Kai wai bata baka tuwo bane naga baka dariya”.
A daƙile yace.
“Haka nake”. Dariya tayi tare da cewa. “A'a Fariyda na bar miki abinki mutum Allah yayisa mai kyau ga gayu da ƙamshi amman kaƙi dariya kace haka kake, kuma fa a hakama kyau kayi”. Dariya Hafiz da Goggo Dada sukayi,
Aunty Saddiqa da Jamila yar dariya sukayi suna jinjina kai tabbas Mahmoud baida M, Aunty Saddiqa ta faɗa a ranta.
Sadiq ne ya ɗan gyara zama tare da cewa.
“To nifa na gama ku nake jira”.
Da sauri Aunty Jamila da ta kasa daina kallon Mahmoud ta miƙe tare da Saddiqa.
“To saduwar al'khairi sai kuma in Allah ya ƙaddara zuwanmu”.
Kai ya ɗan juyo tare dasa hannunsa cikin aljihun ya zaro rafan dari biyar-biyar na dubu hamsin hamsin guda biyu, gaban Hajja inna ya ajiye tare da ɗan kallonta yace.
“Ga wannan ba yawa”.
Sai kuma ya kauda kansa daga ganin kallon da Ummi ke masa, a hankali ya miƙe tare da ɗan matsowa kusa dasu Aunty Jamila.
“Mungode Allah ya tsare hanya, a gaida Malam”. Ya faɗa da fuskar ba yabo ba fallasa, murmushi Saddiqa Aunty Jamila sukayi tare da cewa.
“Amin ya Allah, Allah ya bada zaman lfy da zuriya ɗayyiba”.
A hankali ya juya cikin parlour yayi kamar bai jisuba.
Ita kuwa Hajja inna godiya tai ta musu da cewa.
“Yar nema harda suma da taji an ɗaura aurenta dashi, yanzu ko tayi bulum buƙui harda ɗan kumari tayi, wata ƙil ita yana mata dariya a ɗaki ko Fariyda”. Ita dai Fariyda kai ta sunkuyar ba tare da ta kalli kowa ba. Saddiqa da ta gaza danne dariyarta ne tayi sauri tayi gaba.
Daga nan suka fita da rakiyar Fariyda, Ummi, Goggo Dada harda Abba
Shi kuwa Mahmoud sama ya sake haurawa yana jan tsaki.
Bayan kwana biyu su Hajja inna suka koma Gembu membila, Aunty Saddiqa ma ta koma Adamawa yanzu gidan ba baƙi.
“Allah ya kiyaye hanya ya bada sa'a.”
Ummi tace masa.
“Amin yace tare da yunƙurawa ya miƙe tsaye sai kuma ya ɗan koma ya rusuna jin Abba na magna.
“In ka fita ka biya ka duba surkinka da jiki jiya a asbiti aka wuni dashi Sugansa ya ɗan tashi”.
Shiru yayi tare da zubawa Abban ido yana mai-maita Surki! Surki!! Surki!!! Ya kuma faɗa karo na uku, idon da Abban ma ya zuba mishi ne yasa yace.
“Abba waye Surki kuma!”.
Ya tambaya da iya gskyarsa dan shi yama kasa tuna sunan da nasabar dake sa asawa mutum sunan surki.
Fuska ya tsuke tare da cewa.
“Surkinka mahaifin matarka Fariyda aminina malam Ibrahim ka gane yanzu ko baka ganeba in ƙara maka bayani”.
Kai Ummi ta jinjina cikin zuba mishi ido kai ya gyaɗa tare da cewa.
“In sha Allah”. Yace tare da yunƙurin miƙewa tsaye, Abba yace.
“Zauna da sauran mgna”. Gyara zamansa yayi tare da maida hankalinsa kan mahaifin nasa da yayi gyaran murya cikin yanke hukuncin da yasan ba fashi yace.
“In sha Allah gobe, matarka zata koma sama side ɗinka, ku haɗu a can da kai da ƴaƴanka da matar taka.”
Sunkuyar da kai yayi ganin kallon da mahafin nasa ke masa, shiru yayi cikin tunanin tudun dafawa ta yadda zai kaucewa tsaɓawa umarnin Abba da yasan ba abinda zai hana shi aiwatar da abinda ya faɗa sai Allah.
“Anjima idan Hafiz ya dawo makaranta, zaije ya ɗauko sabon gado za'azo a shirya mata shi, a fidda tsohon gadon a bawa Maman Samira”.
Har lau bai iya cewa komai ba, illa gefen lips ɗinshi na ƙasa da ya ɗan tauna, ta ina zai haɗa ma zauni da ita, ai sun sani shi bayan sheering komai nashi da wani part ɗinsa nasane shi kaɗai in Banda Yah Amin ba mai kwana a ciki, numfashi mai sanyi ya fesar tare da kallon Ummi dake cewa.
“Baka jine?”. Kai ya ɗan jujjuya tare da kallon Abba cikin ɓoye shirinsa a kanta da ya gama kitsimawa yace.
“To Abba”. Ba tare da ya kalleshi ba yace,
“Tashi kaje”. Kai ya gyaɗa tare da miƙewa tsaye
Daga nan ya fice.
Da sauri tace.
“Yaushe ban saniba”.
Ta ƙare tambayar tana gyara riƙon wayar tare da sauraron Adda Nana dake ce mata.
“Ai shekaran jiya dare dare Nasir ya tafi dashi asbiti sugansa ya hau har 23. Acan ya kwana ma amman Alhamdulillah jiya da yamma sun dawo gida, mu yau duk mukaji yanzu hakama muna gida”.
Tana miƙewa tsaye tace.
“Nima ina zuwa yanzu”.
Daga nan ta katse kiran, ba kowa a parlour alamun suna parlour Abba.
Juyowa tayi ta kalli Samira dake shogowa tace. “Abba ne ya fita da mota yanzu”.
Tace. “A'a Uncle Mahmoud ne”.
Kai ta gyaɗa cikin gamsuwa ta kuma juyo ta zauna tare da kitsima abinda zatace in ance ta nemi iznin.
Da sauri ta kalli Ummi data fito.
"Ido cike da ƙwalla tace.
“Ummi Baba Malam ba lfy jiya a asbiti ma ya kwana”.
Cikin kulawa Ummi tace
“Mahmoud ɗin ne ya gaya miki?”.
A, ta furta da nufin cewa a'a sai kuma tayi saurin gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh Ummi, kuma ina son zuwa”.
Tana ɗan gyara ɗaurin zaninta tace.
“Kin tambaye shi ko”. Da sauri tace.
“Eh yace inje”.
Ummi tace. “To ba matsala shirya bari in kira Hafiz yazo ya kaiki”.
Tace. “A shirye nake ma Ummi”.
Ƙarfe tara dai-dai tana gaban Baba Malam ɗin tare da sauran duka yan uwanta mata da suke ɗakunansu a nan cikin Kano da su Raihana da Zainab.
Murmushi dattijon yayi yana kallon su Zaid dake ta kwaramniya a tsakiyar su yace.
“Alhamdulillah jiki da sauƙi sosai Fariyda ya yaranki da mijinki da surkanki”.
Tana ɗan yin ƙasa da kai tace. “Alhamdulillah Malam sunce in gaidaka da jiki sai sunzo”.
Kai ya jinjina cikin jin daɗi ganin ta ɗanyi kumari yace.
"Ngd matuƙa Allah yayi miki al'barka”.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.