Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 9 of 86
Daga cikin gidan in ka shigo ta gate É—in gabas É—in.
Wanni babban garding ne mai ɗauke da dukkan sirrai da shuke shuke wanda yake a zagaye da guntuwar katanga sai waya dake sarƙafe a sama.
Daga gefen lammun ta kudu nan ne part É—in su Ummin sashin ne mai masifar kyau da tsari da girma.
Kana buɗe ƙofar farko corridorn ne mai faɗi sai kofar shiga main parlour.
Parlour babbane mai É—auke da kujeru irin set É—in nan mai guda goma 3 sitter guda biyu sai ona-ona sitter mai É—an girma guda biyu.
Sai kuma wasu yan É—agwas É—in ona-ona sitter suma guda biyu,
Sai mainyan labulaye na alfarma da carpert masu masifar taushi duk sky blue color.
Sai daga gefen can dannin area ne mai ɗauke da Dannin table mai kujeru 8, daga nan ciki ƙofar kitchen take daga gefe kaɗan ɗakin Goggo Dada yake, sai kuma can gefen corridorn da zai sadaka da bedroom ɗin Ummin da kuma tura kar Abba da suke a jere daga cikin corridorn ɗin kuma akwai ƙofar da zai sadaka da parlour Abba,
Wanda kuma yake da ƙofar shigowa to cikin corridorn ɗin forko na ƙasan matakalar haurawa sama side ɗin Mahmoud.
daga gefen hagu kuwa matakalar haurawa sama ne a shimfiɗe mai faɗi. Wanda yasha gyara na musamman a jikin ginin duk wani datsetstsen madubunine mai fidda hasken farin wata, yadda ƙasan yake haka saman yake sai dai shi 2 bedroom ne.
Yayinda komai na cikinsa yake fari ƙal-ƙal.
Haka kuma part ɗin su Yah Amin ɗinma yake sama da ƙasan.
Idan ka shigo gidan ta gate É—in yamma da part É—in su Yah Amin É—in zaka fara, daga gefe.
Daga can bakin gate É—in akwai É—an madaidaicin part ciki da parlour da bayan gida wanda na Baba idine da matarsa Uwani, sai yarsu Samira da Abba yasa zamanta ya dawo cikin gida domin sun zama tamkar yan uwa.
Sai can gefe kuma BQ ne mai girma. Daga can gefen kuma wani part É—in ne irin na Yah Amin sak da sak a rufe kib.
Gidan duk zagaye yake da guntayen bishiyoyin dabino masu É—auke da Æ´aÆ´a rungus a jiki.
A hankali yake taka steps ɗin har ya haura sama sai kuma ya ɗan zame ya zauna kan kujerar dake bakin ƙofar parlour bayan ya ƙonƙosa ƙofar.
Juyowa yayi jin an buɗe ƙofar.
A hankali ya miƙe ya shiga.
Kai tsaye ya nufi gefen dama a hankali yake tafiya cikin corridorn É—in da zai dashi bedroom É—insa.
Shi kuwa Salim murmushi kawai yayi tare da juyawa ya shiga É—aya É—akin.
Kwanaƙi sun ɗan ja.
Cikin sanyi Jidda ta kalli Salim dake gefenta yana murmushi yace.
“My daer sis please ayi min indomei mai É—an yajiâ€.
Tana É—an lumshe ido tace.
“Allah ni na gaji Yah Salimâ€.
Kamo hannunta yayi ya fara janta tare da cewa.
“Daga gobe dai zaki huta sai na kuma zuwaâ€.
Da sauri tace.
“da gaske gobe zaka koma?â€.
Yana janta tsaye yace.
“To ya zanyi Yan Amin da Yah Ahmad sun uzzura min sati biyu kacal nayi Amman gani suke kamar nayi shekara biyu ne, Please tashi dan Allah yunwa fa nakejiâ€.
Da sauri tace.
“Zanyi maka dan Allah in tambaye manaâ€.
A hankali yace.
“To ina jinki Allah yasa na saniâ€.
Tana É—an kauda kai gefe tace.
“Kama sani kamâ€.
“Hmmm yi tambayar ina jinki?â€.
Da sauri ya runtse idanunsa sai kuma lokaci ɗaya ya buɗesu cikin sanyi ya zuba mata idonsa da suka cika da baƙin cikin jin tana faɗin.
“Wai dan Allah Yah Salim da gaske Yah Mahmoud bazai taÉ“ayin aure ba a rayuwarsaâ€.
Cikin sanyi ya gyaÉ—a mata kai alamar eh.
Cikin zaƙuwa tace.
“To meyasa? Allah ya sani ina son Yah Mahmoud.
Dan Allah Yah Salim ka gaya masa, nace Mama ta gayawa Baba ya gayawa Abba amman wai sai tace min ai shi bazai taÉ“a yin aureba, wai kar kuma in sake in gayawa kowaâ€.
Sai kuma tayi saurin kamo hannun Salim É—in ganin zai tafi cikin rauni tace.
"Dan Allah Yah Salim meyasa kuke cewa bazai taÉ“a yin aureba a rayuwarsaâ€.
Ido cike da tashin hankali yace.
“Sabida b........!
*Littafin Saƙar Makafi na kuɗine 1k ne kacal ku biya ku karanta ba haƙƙin kowa a kanku. 5843176522 Moniepoint Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta nan 09097853276 mutanen Niger 1000cfa +22790440050 .*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 4
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta 09097853276 Mutan Niger 1000cfa +22790440050*
“Saboda baki da kunya, shine zaki tsareni da batun wai kina son aure, aurenma Mahmoud kike so! Lallai na yarda kin rainani Jidda me zai hana shi ki taresa ki faÉ—a masa da kanki wato sai nine marainin wayonki, shi da yake kin sansa farin sani No Nonsense man ne ai baki tinkaresa ba, yoh kima gwada mana ki gani, zan baki shawara kar rashin kunyar ki da zubar mutuncinki ya kaiki ga tsare Mahmoud kice kina sonsa wlh tabbas nasan in ya fara tsitstsinka miki mari har sai ya zubda miki haÆ™owaranki ya baki su a tafin hannunkiâ€.
Tsuma jikin Jidda keyi baki ɗaya domin faɗa da har gitsewar Yah Salim ɗin nata yayi masifar bata tsoro, bata taɓa zaton haka daga gareshin ba, ido ta zuba mishi tana hango asalin wutar ƙunan dake zuciyarsa wanda ke gaurayi da tausayi gami da rani.
Sai kuma ta rumtse idonta jin yana faÉ—in.
“Uwar me kike kallo a fuskata mara kunya, to wlh kika kuskura kika yi wannan maganar a wurin Babanmu ko Abba ko Yah Ahmad ko Yah Amin da Ummi sai na tayar miki da hankali fiye da yadda zaki tayar musu da hankali, banza mara aji ga masu sonki yara na gari me zai hana ki fito da Ubaid dake nacin zuwa wurinkiâ€.
Cikin sanyi da fahimtar babban lamarin da ake tsoron tunawa dashi akan mgnar Mahmoud É—in akan batun aurensa ne yasa tace.
“Kayi haÆ™uri Yah Salim ban san ranka zai É“aci hakaba, kuma in sha Allah ba wanda zan sake wannan maganar dashi sai inda ya daceâ€.
A kufule ya wuce Side É—insa.
Bayan kwana biyar
Salma ce kwance bisa 3 sitter tayi pillow da cinyar Mahaifiyarta Mimy ido a lumshe tace
“Mimy ina son Mahmoud wlh har raina ina sonsa amman Fariyda taÆ™i ta fahimceni sai dai tai ta kushesaâ€.
Numfashi Mimy ta fesar tare da cewa.
“Kada ki damu Salma in sha Allah.
Mahmoud mijinki ne, bi'izinillahi ta ala, in dai kinga bai aureki ba to sai in Allah bai rubuta shi a matsayin mijinki ba, muyi ta addu'a, in sha Allah zaki sameshi sai dai in har kece kikace kin daina sonsaâ€.
Fuska cike da farin ciki tasa tafin hannunta ta rufe idonta cike da gamsuwa.
Adamawa Salim ne kwance bisa gado, yana riƙe da waya.
“Eh yau one week kenan da dawowa ta.â€
Sai kuma ya É—anyi shiru yana sauraron abinda Sulaiman ke faÉ—i.
“Ina son zuwa gida amman Yah Amin ya hanani wlh nayi missing guy nan, shekara É—aya kenanfa cib bamu haÉ—u ba, nayi missing hataransa maaifarsa faÉ—ansa Citta Man yana nan da halinsa ko?â€.
Murmushi Salim yayi tare da cewa.
“Yoh mai zai sauya mutumin da a waya ma ranar naji yana rufeka da faÉ—a kamar ubanka, to ko jiya wai cemin yayi shifa baya son shashanci jifa kamar wani ubanaâ€.
Dariya sukayi da sauri Sulaiman yace.
“Afwan bari in amsa kiran Hayateeâ€.
Daga nan ya katse kiran.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.