Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 38 of 86

Abba ne ya gyara zama tare da kallon Mahmoud.
“Mahmoud!
Mahmoud!!”. Ya kuma kiransa a karo na biyu.
Ba tare da ya kalleshi ba yace.
“Na'am”. Cikin kaurara murya da bada umarni yace.
“Ga nan matarka mahaifinta da kansa ya kawo maka ita, kamar yadda ya kawowa ɗan uwanka ita a baya.
Har lau bai kalleshi ba kuma ko ƙala baice ba.
Cikin isar da saƙo Abba yace.
“Ɗan uwanka Aminullah ne yace a maka aure, ni kuma nayi maka auren matar kuma gata nan na cika wasiyyar ɗana, ban saniba ko zaka tayani cika wasiyar ko zaka ƙi aiwatar da muradinsa na zamewa yayansa uba tako wanne sashin”.

Hannunta Baba Malam ya kamo tare da miƙar da ita matso da ita kusa da Mahmoud ɗin, hannunsa ya kamo ya damka mishi hannun Fariyda cikin nasa tafin hannun,
ya kalli Goggo Abu da Aunty Amarya yace.
“Ku tashi mu tafi gida, Alhamdulillah na kawota ɗakin mijinta Mahmoud da kaina. Mahmoud ga matarka Fariyda Allah ya baku zaman lafiya.
Ku kuma kuyiwa Saddiqa mgna in su ƙarasa shigar da kayanta su fito mu tafi.

Da sauri Bappa Lawan yace.
“Malam muyi musu addu'a mana”.
Kusan a tare suka ɗaga hannunsa kana Baba Malam ya fara jero musu addu'o'i samun zaman lafiya da zuriya ɗayyiba.

Ita kuwa Fariyda tunda akasa hannunta cikin na Mahmoud da taji yayiwa hannunta wani irin azabebben riƙon da saida hannun ya bada sautin ƙas.
Ta rumtse idonta da ƙarfi sabida wani irin azaban gotar mata da ƙashin hannun da yayi da zafin targaɗa mata hannun da yayi da gangan. Lip ɗinshi na ƙasa ya kuma ciza tare da ƙara damƙe hannun da ƙarfi dai-dai lokacin da yaga duk iyayen nasu sun fita cikin yin mgnar zuci yace baki isa inyi musu ko sa'insa da iyayena a kankiba.
Ita kuma Fariyda tunda ya gotar mata da ƙashi bata kuma sanin me sukeyi ko me suke cewa ba. Gigitaccen zufar azaba ne ya fara tsatstsafo mata ta dukkan hudar gashin jikinta baki ɗaya.
Su Abba na sauƙa suka samu su Saddiqa a parlour Ummi akwatunan Fariyda kab na jere can a gefe.
Gaida Abba da Bappa Lawan sukayi kana suka kalli Salim da PA sukace.
“Salim zamu tafi dare nayi fa”.
Da sauri Salim da PA suka miƙe tare da cewa.
“To bi'inillah.
Daga nan suka sallami Ummi da Goggo Dada suka fita dukansu harda Aunty Jamila.
Cikin jin dadi Ummi tai ta musu godiya, Goggo Dada ce ta bawa Salma dake kusa da ita rafan dari biyar-biyar na dubu hamsin tace.
“Ga kuɗin kawo Amarya mun gode Allah ya nuna mana naku”.
Cikin kunya Salma tace.
“Mon gode”.
Saura kuma suka amsa da Amin.
UMMI ta kalli Baba Malam dake cewa su Mamy su tafi.
“Malam mun gode Allah ya bar zumunci da qauna ya basu zaman lfy”.
Yana kallon ƙanwarsa Goggo Abu dake miƙa Goggo Dada Zaid da Aunty Amarya dake miƙawa Ummi Zaitoon yace.
“Amin ya Allah”.
Daga nan duk suka juya suka fita...

A can sama kuwa, a fusace ya miƙe tsaye tare da fizgo hannunta da ya targaɗa da har yanzu yake cikin hannun nasa.
Wani irin gigitaccen ƙaran wahalar azabtar zogi ta cilla tare da saurin tashi tsaye still dai bai saki hannunba.
Da ƙarfi ya fincinota ya nufi ƙofar parlour nasa, yana isa ya buɗe ƙofar ya da ƙarfi ya hankaɗata waje tare da yarfa hannun nata da ƙarfi, ba tare da ta gama dawowa daga duniyar azaban zogin da ya cillataba wanda a take taji fitsarin azaba na taho mata, sai kuma ya banko ƙofar da ƙarfin da yasata yin taga-taga zata faɗi da hannunta na dama ta dafe ƙargen dake zagaye da steps ɗin.

Kar-kar Tamkar mazari jikinta ya saki wani irin rawa da zufa wani irin zafin da ya ɗauke kukanta cak ya sako mata rawan jiki da bushewar zuciya ne yasa ta fara taka downstairs ɗin ta sauƙo.

Su Bappa Lawan da Mama da Jidda na fita daga corridor ɗin ƙofar parlour da step ɗin ke ciki, ita kuma ta sauƙowa.
A hankali ta murda handle ɗin ƙafar parlour Ummi ta shiga da sallamar da tayi da disashesshiyar muryarta

Da sauri Ummi ta kwantar da Zaitoon ta miƙewa tsaye rungumeta tayi cikin so da tarin farin ciki tace.
“Barka da dawowa ɗiyata , Alhamdulillah yau yata ta dawo wurin Umminta”.
Sai kuma ta ajiyeta kan kujera.
Goggo Dada kuwa goya Zaid tayi tare da nufar kitchen jim kaɗan ta dawo riƙe da tray da plate cike da fruits akai sai bowl dake cike da gashesshen naman da akayiwa Abba da bappa Lawan.
“Bismillah matso kici abinci ko Fariyda”.
Tana mai jin azabtar hannun da ya ɗauke mata kukan murya cike da raunu tace.
“Ummi na ƙoshi Saida naci abinci a gida”.
Ummi tace.
“A'a kada muyi haka dake ƴata”.
Tana cije lips ɗinta ta kalli Ummi da kumburarrun idanunta cikin rawan murya tace.
“Ayyah Ummi kiyi haƙuri wlh bana jin yunwa”.
Ta ƙare maganar tana kallon Goggo Dada dake cewa.
“To in kawo miki Rufaida Yogurt”.
Kai ta jujjuya tace. “Alhamdulillah”.
Kiran da Abba yayiwa Ummi ne yasa ta nufi Side ɗinsa.
Ita kuwa Goggo Dada tray ta ɗauka ta koma kitchen dashi.

Cike da rauni ta miƙe ta nufi bedroom ɗin Goggo Dada.
Akan 3 seatter dake ɗakin ta zauna ta ɗaura hannunta ɗaya mai lafiyar a kanta.
A parlour kuwa a tare suka fito.
“Ina ƴar taki?”.
Cewar Ummi.
“To ko ta haura sama wurin Mahmoud ɗin ne”.
Goggo Dada ta faɗa tana kallon ɗakinta data hango wutan ciki a kunne.
“Ko kuma tayi ɗakinki ba”. da sauri Goggo Dada ta nufi ɗakinta.
Cikin so da kulawa tace.
“A'a nan kikayi ne? Yamin ko wurin Mahmoud kika tafi ai”.
Da sauri ta girgiza kanta ta zamewa ƙasa ta zube kam guiwowinta murya na rawa tace.
“Ayyah Goggo Dada dan girman Allah da Manzonsa kiyi haƙuri ki barni a ɗakinki”.
Ta ƙare maganar hawaye na kwaranyowa mata.
Da sauri duk suka kalli bakin ƙofar jin muryar Ummi na cewa.
“Ki zauna mana Fariyda am, ke da ɗakin goggonki, duk inda kikeso a gidan nan ki kwana, in ɗakina kike soma zo muje”.
Murya a sanyaye tace.
“Ummi Ngd nan ma yayi”.
Cikin nuna so tazo ta kwantar da Zaitoon kan gadon.
Goggo Dada kwantar da Zaid da sai yanzu yayi bacci tayi.
Sai kuma ta kalli Ummi da cewa.
“Amman dai bari in kawo miki koda tea ne kisha, in dai kina son kwana a nan”. A hankali tace to.

A hankali take Sipping tea ɗin, sai kuma ta ɗago kanta ta kalli Ummi dake zaune gefen ta. Narai-narai tayi da idanunta da suke bayyana tsananin damuwar da take ciki.
“Ummi cikina ya cika”.
Tana shafa kanta tace.
“Kiyi haƙuri Fariyda na ki shanyeshi zanji daɗi”. Dan dole ta shanye.
“Yauwa kinga haka yafi Allah yayi miki al'barka”.
A hankali ta amsa da Amin.
A tare suka fita suka barta a ɗakin.
A ƙalla wa ɗaya da rabi suna zaune a parlour mgna sukeyi ta manya masu kamala da jinƙai daga bisani sukayi Saida safe.
Da sauri Goggo ta ƙarasa cikin ɗakin ganinta zaune a kan kujera ta kife kanta bisa guiwowinta hannunta mai ciwon yana kan hannun kujerar.
“A'a Fariyda bakiyi bacci bane taso kizo ki hau gado ki kwanta ai zai ishemu”
Kai ta jujjuya mata tare da cewa.
“A'a Goggo Dada nan ma ya isheni”.
Tana mai gyara mata wurin kwanciya tace.
“A'a fa zo nan ki kwanta”.
A hankali ta dawo bakin gadon ta kwanta tare da bawa yaran baya.
Ita kuwa Goggo Dada bathroom ta shiga alwalayi tayi kana tazo ta rage musu hasken ɗakin tare da yin addu'a ta kwanta, in minutes bacci yayi awon gaba da ita.
Ita kuwa Fariyda azaban ciwon hannun ya hanata bacci.
Da sauri ta dawo kan kujerar ta zauna tare da kife kanta jikin kujerar.
Sai kuma tayi saurin miƙewa tsaye jikin ginin ta kife kanta saboda zogi.
Sai kuma ta dawo kan kujerar.
Bayan kamar awa biyu tana ta sintirine, ta kuma ta shiga bathroom ido ta zuba wa hannun ganin yadda ya kumbura.
Da kyar tayi abinda zata yi ta gyara jikinta cike da mamakin saura mata kwana biyar date period ɗinta Amman sai gashi ya dawo mata yau. Don tsananin ɓacin rai da tashin hankali kan iya jawo hakan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.