Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 68 of 86

Mutanen WhatsApp da Arewapen makaranta littattafai na masoya na ga Link na Arewapen
https://arewapen.com/u/garkuwa

kuyi Following É—ina mu haÉ—e

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 32
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

“Fasiƙancin da kuke aikatawa ta faɗa min. Kuma yana nan rubuce a littafin aiyukanka littafin da rubutunsa baya gogewa, marubucin da baya mantuwa baya ƙarya kuma ya rubuta tun lokacin da bakaji kunyar mahaliccin mu ba ka tuɓe gaban fatsiƙa, kayi fasikanci mafi najasa wanda sai marar tsoron Allah ne kaɗai zai iya wannan ƙazantar”.
Wani irin tsuma jikinsa ya farayi, lips É—insa kuwa sai rawa suke yi amman ya kasa furta komai, idanunsa da suka kaÉ—a sukayi jazir tamkar zasu yi aman wuta ya zuba mata jin tana faÉ—in.
“Ma zinaci dai yasan makomarsa wutar jahannama c”.
Da sauri ta juya da gudu tayi bedroom ɗin tana shiga ta maida ƙofar ta rufe. Tare da dafe ƙirjinta da hannunta duka biyu saboda ganin yadda jikinsa yake rawa da yadda ya yunƙuro yayi kanta yayi masifar bata tsoro na gasken gaske, a hankali ta koma bakin gadon ta zauna tana maida numfashi cike da jin tsanarsa a fili tace.
"A haka wai Baba ya amince ya aurar dani ga mazinaci”.
Sai kuma tayi saurin rumtse idonta cikin nazarto kalaman Yah Amin da ya taɓa ce mata.
Ai Mahmoud bazai taɓa yin aureba har gaban abadan sai dai in har shine yazo yace yana buƙatar a mai aure.
A hankali tace.
“Ok wato yasan ɗan uwansa mazinacine baruwansa dayin aure ko wacce ya samu a titi maidata matarsa yake. Ƴaƴan tsinannun harda kuranta shi a matsayin ɗaya cikin dubu na shu'umin namiji, a haka su Abban suka zuba mishi ido suka barshi kenan yaci gaba da zina baza ma su masa aure ba, sai ni Fariyda da aka tsana aka ɗauka suka ƙaƙaba min masifeffen ɗansu mazinaci”.
Sai kuma ta lumshe idanta hawaye na zuba cikin rauni tace.
"Mutuwa ce ta jaza min da ta ɗauke tsarkakken Aminullah ta bar wannan masifeffen mazinacin”.
A can parlour kuwa zama yayi tare da kafa guiwowin hannunsa kan cinyarsa ya riƙe kansa da tafukan hannunsa da masifan ƙarfi.
Innalillahi kawai yake iya mai-maita wa.
Yana mai jin ciwon tozarcin da Idaya tayi masa a gaban wannan yar ficilar yana tafasa masa zuciya da jini, tabbas da ta tsaya zai iya mata shaƙa da hannu ɗaya da zata iya rasa numfashi ta, jin yadda jikinsa ke rawa da tsuma ne da hauhawar fusatar da zuciyarsa ke nuna mishi ya ɓalla ƙofar ya figo yarinyar nan ya ɓallata ya watsa a dozbin ko zaiji sanyi.
Jin karfin huɗubar shaiɗan na shigarsa ne ya ƙara kaimin nanata Innalillahi dan yasan in dai ya ɓalla ƙofar zai iya mata shaƙar mutuwa.
Wayar Yah Amin dake gefensa da yaci gaba da Vibrating ne yasashi ƙara rumtse idanunsa.

Sa'ad kuma addu'a ya rinƙayi da fatan Allah yasa a ɗaga wayar.
A kufule ya É—aga wayar tare da karawa a kunensa, cikin jin daÉ—i Sa'ad daya gane muryasa yace.
"Afwan big broz ashe number ka my princess ta samin.”
Cikin sauƙe nannauyan ajiyan zuciya da jin samun damar raba kanshi da ita ya ɗan sassauta muryasa tare da amsa gaisuwar da Sa'ad ɗin ke masa cikin girmamawa.
Shiru yayi jin abinda Sa'ad É—in ke cewa.
“Afwan Yah Mahmoud ko zan samu yin magana da ita, ko a bani number ta sai in kirata”.
Cikin danne yanayin da yake ciki yace.
"In na koma zan bata wayar”. Jin haka yasa ya fahimci baya gida kenan.
Cikin jin dadi ya kira Mommynsa bayan sunyi sallama da Mahmoud É—in.
Murmushi mai cike da jin daÉ—i tace.
“In sha Allah Fariyda matarka ce, dan Allah ya nuna min haske a alaƙarku a cikin mafarkina a daren jiya”.
Cike da jin daÉ—i yace.
"in sha Allah Mommy”.

Ita kam Fariyda da tunanunkan tayi bacci bayan ta samu su Zaid ma sunyi bacci.

Ƙarfe biyu dai-dai ta farka da wata iriyar fitina niyar yunwa mai sa rawan jiki, da kyar ta iya salla ko nafila bata ɗaura ba ta miƙe tsaye.
A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito parlour cikin sanɗa take ɗaga kafarta.
Ajiyan zuciya ta sauƙe ganinsa tsaye da wani ɗan matashin da jikin rigarsa ke ɗauke da tambarin hotel ɗin, kayansa ta gani yana miƙa masa alamun wanki yake bashi.
Amsa yayi ya juya ya fita cikin danne tsoronta ta ƙara matsowa cikin parlour.
Kan Centre table ɗin dake gabanshi ta sauƙe idon ta Tray ne mai ɗan girma sai plate guda ɗaya, sai 2 bowls sai cups biyu, da flacks sai kayan tea, plate da bowls ta kalla wanda yayi musu fes, alamun yaci ya kai geji kenan ta sani shi da cin wani abu kuma sai gobe kenan, dan ta fahimci in yaci ɗaya lafiyeyye dai sai kuma washe gari iyaka da dare ya ɗan sha fruits ko Custard sai ko ya ɗanci Cookies da ɗan chocolate tea shike nan.

Zamanshi ya É—an gyara tare da gyara zaman system nashi bisa cinyarsa, sai kuma ya É—an É—auki wayarsa da duba sakon Dr Imran Patel, na basu lokacin da zasu je su ganshi gobe da yamma.
Murɗawar da cikinta ya kumayi ne, yasa ta ɗan ƙara matsowa cikin parlour a hankali tace.
“Yunwa!”. Ko inda take bai kallaba, da ɗan ƙarfinta da ya rage tace.
“Me zanci yunwa nake ji fa”.
System nasa yake dannawa yana aikinsa Tamkar bai jitaba.
Cikin rawan murya tace.
“Da kaifa nake magna”.
Har lau bai kulata ba, sai ma kanshi da ya É—an juya yana kallon bedroom É—in dan jin kamar kukan Zaid.
A hankali ya miƙe bayan ya ajiye system nashi bisa Centre table ɗin ya nufi bedroom.
Jim kaÉ—an da shigansa ya fito dasu.
A kan kujerar ya ajiyesu tare da jawo flacks ɗin tea ɗin dake cike ya juyo musu a cups ɗin da yake da bakin fida a jikin marfinsu, maida marafen yayi ya rufe tare da miƙa musu da sauri suka fara shan tea ɗin da zafinsa ya taimakawa Zaid wurin sanyi da ya fara ratsa shin.
Hawayen daya cika mata idone ya silalo mata, murya a raunace tace.
"Yunwafa nakeji me zanci?”. Ta ƙare tambayar cikin murya da kaji kasan kuka take yi, da gefen idonshi ya ɗan kalli inda take tsaye ta ɗaura hannu duka biyu kan cikinta fuska a raunace ido na zubda ƙwallan, wani irin tuƙuƙin ɓacin rai ne ya tokara mishi ƙahon zuciyarsa, kuka akan yunwa harda hawaye shi ya tsani wannan banzar ɗa'iba ta koki banza koki wofi.
Cikin rauni tace.
“Wayyo Allah cikina ciwo yunwa”. Tayi magnar da sasssyan kuka ta zame ƙasa ƙasa ta zauna, buɗe plate ɗin da taga yana rufe, ɗan guntun namane a ciki amman irin naman da yakeci jijiya ne ta sani ko a gida da ban ake ɗaure masa nasa iya shi ake dafawa, ita kuma bata iya cinsa bama.
Meda plate ɗin ta rufe, jiki na rawan yunwa ta lafe jikin kujera ta saki sassayan kuka dan har wani duhu-duhu da jiri take gani”.
Tsaki yaja tare da miƙewa tsaye, menu ɗinsu na kitchen dake kan Dannin table ya ɗauko ya wurga mata shi kan cinyarta, daga nan ya juya ya fita.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.