Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 56 of 86
Bayan kwana uku Mamy ne da Aunty Amarya zaune a parlour Ummi sunzo dubiyar jikin Zaid Fariyda dake ajiye musu ruwa da drinks ne ta ɗan kalli Mamy dake amsa gaisuwar Mahmoud da Ummi ta kirashi a waya ya sauƙo gasu malam suzo duba Zaid.
“Wai dole sai anyi masa aiki ko”.
Mamy tace yana ɗan yin ƙasa da kansa yace.
“Eh gwara ayi aikin zaifi dan Maganin nan fiye da wata uku anayi ba sauyi”.
Aunty Amarya tace.
“Allah yasa ayi a sa'a a dace da samu lfy”.
Cikin jin dadin addu'arta yace.
“Amin ya Allah. Malam fa?”.
Goggo Dada tace.
“Yana parlour Abbanku”.
Kai ya gyaɗa tare da miƙewa ya nufi parlour Abba.
Bayan sun gaisa Malam yace.
"Wai India zaku je ayi aiki ko”. Kai ya gyaɗa yace. “In sha Allah”.
Allah yasa ayi a sa'a.
Da Amin suka amsa.
Haka dai sukayi ta hira har sai ƙarfe tara da rabi na dare kafin suka tafi.
Mama ne ta kalli yaran nata Salim da Ahmad dake ta tsara shirin yadda za'ayi auren.
Cikin tsaresu da idon tace
“Kuma naga batun Mahmoud da Jidda baya gabanku”.
Salim ne yayi saurin cewa.
“Mama ni dai wlh ina baku shawara Jidda ta bawa Sulaiman haɗin kai zai fiye mata al'khairi dan wlh Mahmoud wannan auren ma, ɗan uwan banune har yau na kasa gane manufar su Abba da suka yiwa Mahmoud aure bayan sun san matsalarsa, kema kuma kin sani bayan wannan babbar ƙaddarar da ta cire tsammanin zai yi aure a rayuwarsa kun san cutar ƙyaƙyaminsa da duk sanda fatar wani ya taɓa fatar jikinsa sai yayi ƙuraje yayi ta ƙaiƙayi har sai yayi zazzaɓi iya wannan mafa kun san ya isa ya hansa aure fatar Yah Amin ce ka ɗai in ta taɓashi baya komai ko ni da Sulaiman iya karmu dashi tafin hannunsa da namu su haɗe ko cikin rashin sani fatarsa ta gogi ta wani sai yayi wannan yan ƙananan ƙurajen borin jinin fa, bare kuma ga wannan iftila'in da kin sani auren nan ma da akayi bashi da wani ma koma mai kyau,
a haka kuma kike biyewa shirme Jidda kuma itama ɗin ta sani, in bata son Sulaiman naga wani ma na zuwa wurinta Khalid kuma na bincikesa na gane ɗan Dirankadi ne yaro ne mai mutunci”.
Da sauri ta katse shi da faɗin.
“Subahanallah kaja numfashi mana, ka hutar da kanka in dai ina raye in sha Allah sai Jidda tayi zaman aure da Mahmoud tunda tana sonshi kuma in bai warkeba Aminullah bazai bar wasiyar a aura masa waccar sadakayellar ba ya dade baiyi ƙurajeba dan jarabar ƙyanƙamin tsiya”.
Ahmad ne yaja numfashi tare da kallonsu a tsanake sai kuma yace.
“Allah yayi mata zaɓi mafi alkhairi”. Da Amin duk suka amsa.
“Inaga dai Amina za'a barwa aikin haɗa kayan auren, tunda sana'artace”.
Da sauri Salim yace.
“Eh haka Baba ma yace”.
Baki Mama ta taɓe tare da cewa.
“Bafa za'ayi auren kan nanba sai an haɗa dana Jidda, dan haka ku rinƙa haɗa lissafi da kayan ɗakinta”.
Da sauri Ahmad ya ɗan ture Salim da buɗe baki da nufin yin inkari sai kuma ya kalli Yah Ahmad dake cewa.
“To Mama yadda kikeso haka za'ayi”.
A hankali take tafiya tare da yin hamma da lumshe idonta.
Goggo Dada dake goye da Zaid daya kwana kuka na fitan hankali duk da maganin da aka basa a banza sai da asuba suka samu ya lafa.
“Je kiyi baccinki Fariyda in sha Allah yanzu kam ya lafa, na lura abin in ya tashi sai yayi lokacin da sauƙinsa dai in ya lafa yana iya kwana goma bai kuma taɓashi ba.”
Kai ta gyaɗa kana ta juya tafi.
Mahmoud dake zaune bisa kujera yasa laptop nashi a gaba, sai dai hankalinsa na kan waya bisa dukkan alamun bicike yake yi kan Dr Imran Patel da asbitinsa da duk wasu tsare tsare su.
“Ya batun tafiyar nakune kam Mahmoud?”.
Yana ɗan kallonta yace.
“In sha Allah next week zamu tafi, dan in munyi sa'a visa ɗin su Zaid ɗin zai fito a satin nan”.
Sai kuma ya kalli Amina dake cewa.
"Amman Fariyda tasan da tafiyar nan kuwa”.
Yana ɗan tsuƙe fuska yaci gaba da aikinsa.
Ummi tace.
“Ta ya za'ayi ace bata saniba ai ko wanda bazai je bama a gidan nan ya san da tafiyar bare ita da za'a tafi da ita”.
Da sauri ya juyo ya kalli Ummi cikin zura mata ido yace.
“A tafi da ita kuma? Ummi ta ya kuma za'a tafi da ita?”.
Cikin haɗe rai da mmkin ƙarfin halinsa tace.
“Kamar ya ta ya za'a tafi da ita, ai ita kam zuwa da ita dole ne, lallai ne, tilas ne, jazamanne, farillane. Dolen dole da ita za'a tafi......
https://arewapen.com/u/garkuwa
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗine 1k 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo Evidence ɗin ki ta nan 09097853276 mutane Niger 1000cfa kuma +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
*SAƘAR MAKAFI*
Page 24
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Tunda ta fara jera umarninta ya zuba mata ido kamar ya samu tv har ta dire bai iya ce mata komai ba.
Goggo Dada ne tace.
“To dama ya za'ayi ayi tafiyar jinyar yaro ɗan shekara ɗaya da watanni kuma ace banda uwarsa”.
Juyowa yayi ya zuba mata ido itama ya rasa abin cewa ma, kawai dai shi ya sani ba inda zaije da ita.
Ummi tace.
“Kayi shiru bakace komai ba”.
Kai ya jujjuya mata tare da hararan Amina dan duk ita ta jaza masa koma menene da tayi shiru dai sai ranar tafiyarsu ce ai da shike nan. Da sauri ya janye hannunsa daga jikin hannun kujerar, itama Amina da sauri taja nata hannun tare da cewa.
"Ya Salam sannu na taɓaka ko? wlh ban luraba”. Da sauri Goggo Dada ta zubawa tsuntsiyar hannunsa ido tuni yayi jazir wurin ajiye da wayarsa yayi a alijunsa ya fara ɗan murza hannun nasa tare da rumtse idanunsa.
“Baka ce komai ba”. Ummi ta kuma faɗa cikin son sani manufarsa a hankali ya miƙe tare da cewa
“Yanzu zan tafi wurin Fadil ne sai na dawo zan gaya miki duk yadda mukayi”.
Tana kallon yadda yake murza ɗan wurin da hannun Amina ya taɓa hannunsa tace.
“Ai sai ka kirasa yazo gida muyi mgna tunda dai shi ba baƙo bane, tuna kuma primary school fa kuke tare”.
Amina ne tayi sauri cewa
“Niko Mahmoud ina Fadila”.
Hararanta tayi yace.
“Ban saniba”. Daga nan ya fita. Goggo Dada ne tayi dariya tare da cewa.
“Allah sarki ƙuruciya mai daɗi in ba girmaba me zai raba Fadila da Fadil da Mahmoud rigima dai iri iri na gidan duniya mun shashi”.
Amina tai dariya tace.
“ita Fadila Mahmoud take so, shi kuma Fadil sonta yake harda cewa ai mune sunanmu iri ɗaya ki dena masa magna.
Kuma kullum in Mahmoud yazo position one to Fadil zai zo two in Kuma Fadil yazo first to Mahmoud ne second ita kuma Fadila itace ta ukunsu kullum, ni kuma ni Fadil ke kaiwa ƙara, Abbansu Fadil da Abin dariya harda sayawa Fadil chocolate ya kawowa Fadila wai kada ta kalli Fari da hancin Mahmoud ta kalli baƙin Fadil da aljihunsa harfa kuɗi yake bawa Fadil wai ya bawa Fadila ita kuma in an bata chocolate ɗin sai ta bawa Mahmoud shi wani lokacin ya karɓa wani lokacin ya gwatsaleta tai ta kuka in yaƙi kulata Fadil kuma yayi tabi yana bata haƙuri yana cewa kizo wurina ki shareshi”.
Ummi ce tayi dariya tare da cewa.
“Shifa har wurin Abbanku yake zuwa yace Alaji Umaru ɗanka ya kwacewa ɗana budurwa da farinku da kyanwun nan na asali, Abbanku yayi ta dariya yace ai shima Fadil kekkyawane kawai dai baƙine.” sai kuma ta ɗanyi shiru a hankali tace.
“Kyan da masifa ya jaza mishi ya sa mana ƙunci a zukata”.
Da sauri Amina tace.
“Ummi ki dena tuna abinda ya wuce”.
Goggo Dada tace.
“Allah sarki mutum mai sauƙin kai Allah ya jikansa”. Ta ƙare maganar cikin kauda tunanin Ummi kan rayuwar Mahmoud a baya. Amin suka amsa a tare.
Washe gari da safe Abba ne ya kalli Mahmoud dake zaune gefen sa.
“To Mahmoud ta ya kakega tafiyar zatayiwu ba uwar yaron.”
Gyara zamansa yayi cikin nemo hujjar kai da kai yace.
“Abba in ance da ita za'a tafi hidimar zatayi yawa, dan asibitin nasa bawai a Mumbai ko New Delhi yake ba, har Ahmedabad asibitin yake, gashi dole tafiyar sai.munyi transit a Ethiopia ko Istanbul. Sannan in mun sauka a New Delhi ko Mumbai ba nan zamu tsayaba zamu wuce Ahmedabad kuma kasan transit da tsada ko Business seat zamubi na bare first class”.
Ido ya zura mishi dan karantar yadda yake son kaucewa tafiya da ita da wasu hujjoji marasa tushe.
“Duka duka nawa za'a iya kashewa ne Mahmoud?”.
Abban ya tambaya cikin gamsuwa da ni'imar arziƙin da Allah yayi musu.
Gyara zamansa yayi tare da cewa.
“Abba akwai yawa fa kudin, nan ma bamu san nawa aikin zai kama ba a iya tafiyar fa in kunce dole aje da ita,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.