Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 18 of 86

Humaira kam ido ta ɗan zare ganin madarar kyau na zahiri.
Sai baƙin miskilanci da yasa tasha jinin jikinta.
Yah Amin ne yace.
Mahmoud ana gaidaka
Still dai kamar bai jisuba.
Ummi tace.
“Ikon Allah kar dai dashi da ɗan nashi duk bacci sukayi a hakan”.

Goggo Dada kuwa Murmushi kawai tayi dan tasan idonsa biyu.
Aminullah kuwa cikin samun mafita yace.
“Ai kuwa inaga baccin sukayi”.

Ita kuwa Salma bata dai daddaraba.
Ta matsoshi a hankali tace.
“Ga Zaitoon ɗin”.
Kanshi ya ɗago tare dayi mata wani hautsinennen. Kallo da manyan idanunsa kallon da yasa ziciyarta bugawa wanda yasa dole ta kauda kanta.
Zaitoon kuwa na ganinsa ta wangale baki ta yunƙuro tayi kansa.
Juyawa yayi ya kalli Hafiz tare da cewa
“Karɓeta ka kawo min ita”.
Da sauri Hafiz ya mike tare da amsar Zaitoon ɗin ya miƙa mishi ita.
Goshinta ya sumbata ai kuwa tuni tasa hannunta duka biyu ta maƙale wuyanshi tana Balankwace dariya.

Aminullah kam cikin kunya ya kalli Salma dasu Zainab dakeyiwa su Ummi sai anjima, har suka fita bai kuma ɗago kansa ya kallesu ba.

Suna fita Aminullah yace.
“Kai ni Aminu na godewa Allah da kayan kunyan da Mahmoud ke jaza min yarinya tana gaidaka ko ka kula”.
Ba tare da ya kallesa ba yace.
“To me haɗina da ita? Na santane?”.
Da sauri Ummi tace.
“Shi kuma gaisuwa saida wanda ka sanine akeyinsa? Wlh ka canza hali”.
Kai ya ɗan gyaɗa mata tare da cewa.
“Toh Ummi kiyi ta min addu'a Allah yasa halina ya zama yadda kikeso ke da Yah Amin”.
Kai Goggo Dada ta jinjina wannan kalma ita ke tabbatar mata bada gangan yakeyi ba, haka Allah ya halicceshi mutum mai zarrane shi, ta kuma lura shima yana son ya zama yadda suke so ɗin.
Amsar Zaitoon Ummi tai tare da cewa.
“Kaci abinci”.
Kai ya gyaɗa mata kana ya kwantar da Zaid a gefe Sannan ya zamo ƙasa ya zauna suna fuskantar juna shida Yah Amin ɗin.
“To Goggo Dada zuba mana”.
Hafiz ne ya matso da wormas ɗin.
Suna shiga parlour Fariyda suka samu ta shirya musu komai a kan dinnin table.
Rungumeta Salma tayi tare da cewa.
“Wallahi da zan iya cire son Mahmoud a raina dana ciresa na huta”.
Murmushi Zainab da Humaira sukayi tare da cewa.
“Da kin hutawa ranki”.
Ita kuwa Fariyda janyeta tayi daga jikinta tace.
“In ma banda ke duk cikinmu ba wacce take fatan auren Yoro kamar Mahmoud shiyasa ni tun asali nafi son senior Man irin Yah Amin na bawan Allah ɗan aljanna.
Kinga Zainab ma da Raihana basa sauraron irinshi ai ke kika jawa kanki.
Ni zakisa ya rainani ma a banza a wofi yaga ƙawata na binsa”.
Sai kuma ta kalli Humaira dake gaya mata yadda ya gwatsaleta.
Hararan Humaira tayi tare da cewa.
“Duk da haka dai ina son abuna”.
Tsaki Fariyda taja tare da kallon ƙawar tata aminiyarta kuma yar ƙanin babanta tace.
“Sannu uwarsa, dan Allah ni zauna kuci abinci”.
A can parlour kuwa tare suke cin abinci a plate ɗaya.
Awaran Couscous ne da yaji kwai, sai ɗan vegetables soup ɗin da yaji dambun nama a ciki.
Ajiye fork ɗin Aminullah yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ya ɗauki cup ɗin tea ya fara ɗan Sipping.
Shi kuwa Mahmoud kanshi a ƙasa ya kuma buɗe ɗaya kular da ya gani kusa dashi.
Tuƙeƙen tuwone na kusa dashi ya buɗe miyar taushene a ciki.
Medawa yayi ya rufe.
Goggo Dada ce tace.
“Yau har dare Fariyda zata huta shiga kitchen kenan.
Yar kekkyawar wormar dake can gefe, wainace da zafita, kwaya shida ya saka, ya buɗe na miyan danderun jan namane zubawa yayi mai ɗan yawa.
Sai kuma ya kalli Goggo Dada yace.
“Tea”.
Ta gane me yake nufi Aminullah ya shanye masa cup ɗaya shiyasa ya nemi ƙari cup ɗin da Aminullah ɗin ya ajiye ya miƙa mata.
Yun ƙira tayi zata tashi a hankali yace.
“Ina zakije Goggo Dada, naga ga kayan tea ɗin”.
Tana nuna mishi cup ɗin tace zanje in ɗauraye cup ɗin ne”.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“No kada ki damu ba sai an wankeba Yah Amin nane fa, kawai samin a haka”.
Yess sai dai Yah Amin ɗin kam dan ko Umminshi ne in yaga dama zaice a ɗan ɗauraye”.
Nan dai yaci yayi haniƙan kana ya miƙe tare da cewa.
“Bari in haura sama”.
“To me za'a ajiye maka na dare”.
Cewar Ummi yana shafa kan Zaitoon yace.
“A'a ban buƙatan komai nida abinci kuma ai sai gobe in Allah ya kai mu bisa rai da lfy.”
Daga nan ya fita.

Washe gari da safe.
Cikin shigar riga da wando baƙin voyel mai masifar taushi da sheƙi yake.
Tsaye gaban Ummi.
“Zanje asbiti buba Baban Fadil”.
Mahmoud ya faɗa Abba dake kishingiɗa a tsakiyar parlour sa Ummi da Goggo Dada na gefenshi suna hira.
“Amman zaka yi breakfast kafin ka fita ko”.
Ummi ta tambaya kai ya jujjuyawa mata tare da cewa.
“A'a sai na dawo”.
Abba kuwa ido ya zuba mishi yanayi masa wani irin kallo Mai cike da ƙauna haka kawai sai yake ganin kamanninsa ya fito ras shi lokacin ƙuruciyarsa.
“Abba ya dai?”.
Yana gyara zamansa yace.
“Ba komai, Allah ya tsare hanya”.
Yayi mgnar cikin sanyin murya da jiki.
Gaggo Dada ma da Ummi.
Addu'a sukayi masa kana ya muƙe ya fita.

Bayan kamar 40 minutes.
Fariyda rungume da yaranta duka biyu ta fito daga Side ɗinsu ta nufi part ɗin Ummi a can baki part ɗin ta hangi Goggo Dada.
Zaune da roba a gabanta da ɗanyen zogalen data tsinko a lambu.
A hankali ta ɗan tsaye saboda jin yadda ake buga gate ɗin gefen gabas wanda sunfi kusa dashi.
Da sauri Goggo Dada tace.
“A'a ina Mala idi yake ne yaje ya duba waye ne mana.
Tsananin bugun ƙofar da ake da masifar ƙarfi tamkar za'a ɓalle ƙofar da rabka sallama da ake yi da ƙarfi ne yasa Abba da Ummi dake Parlour ma sukajiyo.
Jin an ƙara bugun ne da ƙarfi yasa ta nufi bakin gate ɗin, ita kuwa Fariyda kawai ido ta zuba wa gate ɗin.

Tana isa kusada gate ɗin tace.
“Kai wai waye ne?”.
Cikin ɗaga murya taji Muryar wani babban mutum na cewa.
“Nan ne gidan su Yaro farin nan”.
Da sauri Goggo Dada tace.
“Wanne yaro ɗaya ai duk farare ne, me sunansa?”.
Ita kuwa Fariyda Abba ya data fito daga parlour Ummi na biye dashi a baya ta zubawa ido, sai kuma ta juyo tana kallon mala idi da ya nufi bakin gate ɗin da sassarfa.
Ita kuwa Goggo Dada da saure ta buɗe karamar ƙofar jin mutumin na cewa.
“Farin yaron nan mai gashi, ba baƙin kaya a jikinsa yayi hatsari yanzun nan, maza kuyi sauri kuzo mu tafi asbitin..........

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276, mutanen Niger 1000cfa ne baki +22790440050. Hannatou zakuyiwa magna*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 8
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma sdw, da dai sauran abubudann ban lissafa Sune manyan alamomin infection.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.