Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 71 of 86
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 34
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Jin fitsarin na shirin fasa mata mara. Ko ta inda take bai kallaba ya buɗe ƙofar ya fita ta. Da sauri ta shiga bathroom ɗin, ƙamshin sabulansa da turaren wankansa ta shaƙa tana mai lumshe idanta ta taɓe baki tayi buƙatar ta tare da wanka da al'wala ta fito.
9:23 Am tsaye take a kan akwatin nata.
"Ki É—auke min wannan tarkacen naki a nan ki maidashi can ciki wurin bolar da kike tara musu, kuma daga yau ki rinÆ™a zuwa Dannin area É—insu na can wurin kitchen nasu kina breakfast acan kafin ki dawo zasu samu su shigo su share É—akin, dan naga ke Æ™azanta abun sonki ne, bakya kiyayewa ko saboda lafiyar su Zaidâ€.
Cikin tura baki tace. "Nifa bazan iya É—aga akwatin nan baâ€.
Kanshi a sunkuye yace.
“To wa zai kai miki shiâ€. Ya tambaya ba tare da ya kalli ko ta inda take É—in ba. Tace.
"Kai manaâ€.
A takaice yace.
"Saboda ni bawan gidanku ne ko?â€.
Juwaya tayi ta nufi bedroom tana faÉ—in.
"To a barshi a nan É—in manaâ€.
Da sauri ta tsaya jin abinda yake faÉ—i.
"Ke in kika kuskura kika shiga baki shiga da shiba zan wurgashi waje, maza dawo nan ki É—auki tarkacenkiâ€.
A kufule ta dawo kan akwatin tare da fara. Kiciniyar janshi amman ina ta kasa saboda nauyin lodin da Salma tayi masa.
Cikin sanyi tace.
"Wlh bazan iya bafaâ€.
Bai kulataba sai ma game É—insa da ya fara bugawa a wayarsa.
“Dan Allah ka shigar min dashiâ€.
Ko ta kanta bai bi ba, ganin hakane yasa ta juya ta koma ciki tana mgna Æ™asa-Æ™asa. “Mutum ba taimako in kaga dama ka wurgar mana ai ba iya kayana baneâ€.
Dan Jersey veil ta É—auko tayi Rollin kanta akan doguwar rigar dake jikinta.
Dinnin area É—in su ta tafi bisa jagoranci clinar É—in da ya fito daga room É—in dake kallon nasu.
Yana rakata ya dawo É—akin nasu ya shiga domin gyarawa, shi kuwa Mahmoud mai taxi É—insu yayiwa mgna yazo ya kaishi shopping mall.
Shiru ta tsaya a tsakiyar parlour lokacin da ta dawo, sit ba kowa ba wani motsi sai jarabar Ac da ya bari yana ta fusata sanyin parlour, duk da ba wani datti kirki da tarkacene da suba, amman ta gane an shigo anyi shara dan da tazo ta samu a rufe Saida ta koma Reception É—in su ta amshi card É—in.
Sannan ta samu an shigar da akwati an sashi har cikin Wordrobe, ga kuma kayan su Zaid da nata duk an tattare bisa alamu ya wuce dasu Laundry É—insu.
A Parlour ta zauna tana É—an latsa wayarta.
After 47 minutes taji ana Knocking, buɗe ƙofar tayi tare da ɗan ja da baya, da gudu suka kutsa kai cikin parlour, yana biye dasu a baya riƙe da manyan leda guda uku wanda ke ɗauke da tambarin Kids party mall Ahmedabad.
A tsakiyar parlour ya zauna tare da ajiye ledojin a gabansa, Baby tablet daya fitar sabbi dal a ledansu ɗaya purple color ɗaya Pink, purple ɗin ya miƙawa a Zaid ɗayan kuma ya miƙawa Zaitoon.
Sai kuma ya miƙe tsaye tare da juyawa yace.
"Kada ki Æ™ara dukar min yara akan komai, in abu suka É“ata miki ki gaya min zan biya, ga tab É—in su daga yanzu ba ruwansu da wayarkiâ€.
Da ido ta rakashi har ya fice.
Ledodin ta buÉ—e. Pampers, wipes, tissue da wasu tsala-tsalan riguna kala huÉ—u-huÉ—u komai nasu iri É—aya sai dai na Zaitoon dake da kwalliyar mata.
Sai É—aya ledar NAN ne a ciki da Custard sai Cookies da kuma bread da kwalban zuma.
Bai dawo ba sai dare tuni tayi bacci ita da yara.
Bayan kwana biyu a hankali ta fito daga cikin É—akin, zaune ta ganshi bisa 3 seatter yasa system nashi a gaba.
Numfashi mai sanyi ta fesar, gefen Dinnin table taje, kujerar taja ta zauna, tare da ɗan lumshe idonta, 3 minutes tsakani ta kuma miƙewa tsaye, bedroom ta koma, jin kaɗan da shigarta ta kuma fitowa, a tsakiyar parlour ta ɗan tsaya can gefensa kaɗan. Baki ta tura tare da longwaɓar da kai, sai kuma ta koma bayan kujerar da yake zaune.
Tun fito warta na farko ya jita ya kuma ganta, sai dai ko ta inda take bai kallaba asalima ko kanshi bai É—agoba daga aikin da yake yi, aikinsa yake tamkar ba wani bil'adama a wurinma da sauri ta dawo gefenshi sabida jin yadda yaja wani irin dogon tsaki.
Kanshi ya ƙara sunkuyarwa, ba tare da yace ko ƙala ba, a hankali ta ƙara matsowa kusa dashi, hakan ne yasa shi ɗan ɗaga kanshi ya kalleta a fakaice cikin sanyi tace.
“Please pad nake soâ€.
Kanshi ya maida yaci gaba da aikinsa Tamkar bai jitaba, cikin kwaÉ“e fuska ta É—an É—aga murya kaÉ—an tace. “Ayya ina bukatar padâ€. Ido ya watsa mata cikin nata idon, hakan yasa tayi Æ™asa da nata idon, lips É—inshi ya fara É—an motsawa a hankali yana nanata sunan abinda ta kira masa, so yake ya tuno menene ma hakan, numfashi ya fesar a hankali lokacin da ya tuno sunan abun da kuma Aunty Amina ke sawa Ummi ta aikeshi ya saya mata a dole, kafin tayi aure. Fuska ya tsuke ciken daÆ™ilewar murya yace. “Pad ko? Nine ma É—an aikenki ko?â€. Cikin sanyi tace. “Please dan Allah faâ€. A kufule yace.
“Kinga na kasa pad din ne ina saidawa ko tsabar iskanci ne, zaki É“ace min da gani ko sai na É“allakiâ€.
A hankali ta ɗan ja da baya ta tsaya tana murza yatsun hannunta, ko ta kanta bai kuma biba a ƙalla 4 minutes kenan cikin rashin mafita, ta juyawa ta koma cikin ɗakin.
Da harara ya rakata tare da maida hankalinsa kan aikinsa, sai kuma ya ɗan sauƙe numfashi tare da maida bayansa ya jingina tare da zaro wayarsa.
Ita kuwa Fariyda tana shiga kiran Salma na shiga wayarta, kwanciya tayi bisa gado tare da amsa kiran Salma.
Lakaci ya duba saboda jin ana danna door bell, a hankali ya miƙe tsaye,
Buɗe ƙofar yayi tare da amsar yar ledan da mai taxi ɗinsu ke miƙa mai, amsa yayi tare cewa.
“Thanksâ€. maida Æ™ofar ya rufe.
Time ya kuma dubawa a wayarsa, lokaci bawa Zaid mgni yayi. Ya faÉ—a a ransa. Bedroom É—in ya nufa dan ya É—aukeshi yazo ya bashin mgnanin da yau kwana 8 cib kenan da fara bashi wanda yayi dai-dai da kwanansu goma cib a Ahmedabad, yayinda sukayi kwana sha biyu cib da barin Nigeria.
A hankali ya meda ƙofar ɗakin yayi ya rufe tare da maida hankalinsa kan abinda take faɗin.
“Na rantse da Allah Salma in baki daina min magnar yaron nan ba, zan daina ɗukar kiranki.
Wai an gaya miki kowa irinkine da zan saurari shi har kike tunanin zan kalleshi a matsayin da har abada bazai sameshi a wurina ba, kadafa ki manta shiÉ—in Æ™anin miji naneâ€.
Ƙara damƙe ledar pad ɗin yayi tare da harɗe hannunsa kan ƙirjinsa sai kuma ya jingina bayansa da kofar yana kallonta, yana mai ɗan jiyo muryar Salma kaɗan dan video call suke yi.
“Hmmm ni dai ina rabaki da wannan son girman nan naki na jaraba Fariyda ke da kanki dai kin san Mahmoud fa fintinkau sukayi mana, shine babba akan Salim ma fa dan yace min a Æ™alla Mahmoud na bashi wata bakwai, ya kamata ki sani zaman aure ba wasa bane, duk wanda akace mijinka ne to mgna ta Æ™are ki dena lissafin Yah Amin ne mijinki yanzu dai Mahmoud É—in ne mijinkiâ€.
A faÉ—ace tace.
“Kedai wlh kinyi asara Salma wai har yaran nan sun kai mazan da zaki saurara ki amince da aurensu, tunda ke kinji kin gani ya miki wannan ruwan ki ne.
Amman nidai kam yaron nan yamin kaÉ—an Wlh ai shima kansa yasan nafi Æ™arfinshi sai dai Yah Amin, shi dai kam yamin yaro in banda rashin mutunci me ya iya sai isa Æ™asaita yana abu kamar wani sarkiâ€.
A zabure ta miƙe zaune tare da ɗaukar wayar saboda hango fuskarsa ta cikin wayar saboda hasken ɗakin da yake tarwal.
Hannunsa ya kai dan karɓar wayar cikin sauri ta koma da baya tare da maida hannunta ta baya cikin tsiwa tace.
"Me hakaâ€. Dirowa tayi daga kan gadon ganin ya sunkuyo ta inda take.
Inda ta tsaya ya juya hannunsa ya miƙa mata fuska tsuke yace.
“Baniâ€. Baki ta cinna sama tare da Æ™ara É“oye hannunta a baya.
“Wlh bazan bayarbaâ€.
Ta faɗa a tsiwace. Baya ta kuma ja da baya ganin ya nufota yasa ta juyawa da sauri ta dawo bakin gadon, gabanta ya tsaya tare da miƙa mata hannun fuska tsuke yake mata kallon da yasa tayi ƙasa da kanta, a tsiwace tace.
“Na Æ™arfi neâ€.
Da ƙarfi ta rumtse idonta ganin ya sunkuyo kanta, sai ta kuma buɗe idon da sauri jin ya fuzgo hannunta dake riƙe da wayar.
Ƙara rumtse hannun tayi da ƙarfi tana faɗin.
"Wlh bazan sakeba ai ba kuÉ—inka bane ya saya min ita.â€
A kiɗime ta saƙi ƙara tare da miƙewa tsaye, jin yadda ya murɗa mata hannun tare da zaro mata ido murya a hautsine yace.
“Nine yaro ko? Kinfi Æ™arfina ko?â€. Tana yarfa É—aya hannun tace.
“Karya nayi ne kai ba yaro baneâ€.
Da ƙarfi ta saki wani ƙara tare da fara bubbuga sawutan a ƙasa sabida yadda ya kuma murɗe hannunta, fuska cike da fusata yace.
“Ni zaki kirawa yan gutsa-gutsin Æ™awayenki masu rawan kai kamar an sa muku batur, kina ce musu nine yaron ko ban kaiba ko, Mami ce ta haifa miki ni a matsayin Æ™ani da kike rashin kunyar kirana yaro koâ€.
Ya ƙare maganar da ƙarfi tare da kuma murɗa hannun da ƙarfi, wata iriyar zuface ta keto mata a lokacin da ta saki sabon ƙara tare da yarfa hannunta ɗaya tana tsalle still Kuma bata saki wayar ba.
“Na faÉ—a É—in kuma zan Æ™ara faÉ—a ko kasheni zakayi zan faÉ—a kai yaroneâ€.
Murɗe hannun yayi da ƙarfi tare da taune lips ɗinshi kana ya ja da baya.
Kar-kar jikinta ya fara wani irin tsuma da rawan azabar zogi da sauri ta fara binsa tana jujjya kai dan kukan ya tsaya a maƙoshinta.
Ƙara murɗa hannun yayi tare da sunkuyowa dan ganin tayi ƙasa ta durƙusa kan guiwowinta dan sawunta sun gaza ɗaukarta sabida rawan sukeyi.
Da sauri ta fara rarrafe tana binshi saboda yadda yake ja da baya yana mai ƙara murɗa hannun, da ƙarfi ta saki ƙaran tare da buɗe yatsunta ta sake mishi wayar.
Da ɗaya hannunsa dake riƙe da ledan pad ɗin ya ɗauki wayar ya zurata cikin ajihun Black blue jeans ɗin dake jikinsa hannun ya murɗa da ƙarfi tare da cewa.
“Yaro ko? Nine yaro ko? Sake faÉ—a inji na Æ™arfine ko ai kinfini Æ™arfi koâ€. Cikin tsananin rawan jiki ta fara girgirza mishi kai alamun a'a.
MurÉ—awa ya kumayi tare da haÉ—awa da tsawa.
"Nine yaroko har kina gayawa Æ™wailayen Æ™awayenki sabida ke fitsararriya ce, dan kinga ina barinki ne yasa kike min rashin kunya koâ€.
A gigice take yarfa hannunta tare da ƙara rarrafowa ta matso jikinsa fuska na zubda zufa duk da sanyin Ac a wofi, cikin rawan murya ta fizgo maganar cikin azabar zogin.
“No kai ba yaro bane, dan Allah kayi haÆ™uri ka sakemin hannuna ya karye fa Wlh kafi Æ™arfinaâ€.
Da ƙarfi ya kuma murɗe hannun tare da cewa.
“Ƙarya kikeyi ni yaroneâ€. Ido ya zuba mata sabida ganin yadda take karkarwa haka lips É—in tama suke rawa cikin muryar rauni, tsoro, azaba, da sanin ba maceci sai Allah tace.
"Wallahi kai ba yaro bane, kai babbane ka fini fa da 8 years wlh kai babbaneâ€.
Wani irin numfashi mai tafe da shiɗewa taja tare da faɗawa jikinsa kan mararsa ta manna kanta tare da kakkafe idonta, sabida jin yadda ya murɗa hannun ya yarfa mata shi, har saida ya bada sautin ƙas tabbacin ya targaɗe.
Sunkuyo ya ɗanyi ganin yadda ta manna kanta a jikinsa tayi shiru sai tsuma da karkarwa da jikinta keyi, fuskantar ya leƙa, idanunta dake kakkafe ya kalla sai kuma ya ture ta ta faɗi ƙasa bakin gado kan carpert ledan pad ɗin ya wurga mata tare da cewa.
“In bada Æ™azamar mace wacce zata yi shirin tafiya ta kasa tanadin pad.â€
Daga nan ya juya ya fita yana faÉ—in.
“Da kikace ke mara kunya ce, mai bakin tsiwa. In kin farfaÉ—o ki Æ™ara cemin yaroâ€.
Parlour ya koma tare da zama gefen su Zaid dake ta wasa da tablet É—insu.
Gyara zamansa yayi tare da lumshe idanunsa.
Ita kuwa Fariyda wani irin gigitaccen zufar azabebben zogin da ƙashin hannunta keyi ne ya fara tsatstsafo mata tako wani sashi jikinta, har yanzu idanunta na kafe ba suma tayiba, sai shiɗewar kukan da ya tsaya mata a maƙoshinta yaƙi fitowane yasa numfashinta tsayawa cak duk, rawa da jikinta keyi ne ya taimaka mata wurin samun fizgo numfashi da ya taho mata da wani irin gigitaccen kukan dayaƙi tsaya mata.
Idonsa ya buÉ—e tare da zubawa wayar ido Sa'ad ne ke kira, sai kuma ya É—an juya ya zaro wayarta da yasa a aljihunsa, Yah Mujahid ya ne ke kiranta.
Kai ya ɗan rausayar tare da ɗaura woyoyin bisa Centre table ɗin, sai kuma ya kamo hannun Zaitoon da tazo gabanshi gefenshi ya kwantar da ita, yana kallon Zaid da yake miƙa masa hannun kan cikinsa ya kifeshi bayan ya miƙe sawunsa kan table kanshi ya jingina tare da shaƙan numfashi kana ya fesar a hankali ya lumshe idanunsa.
Kuka take yi cike da rauni da ƙuncin zuciya da rayuwa, ga ciwon kan da kukan ya sakar mata haɗe da zazzaɓi.
Ƙarfe uku dai-dai ya buɗe idonsa daga bacci da sukayi, a hankali ya zame Zaid ya kwantar dashi ganin basu farka ba, time ya duba ganin har uku yayine yasa ya miƙe tsaye yana miƙa tare da kallon ƙofar bedroom ɗin jiyo sautin kukanta.
Tura ƙofar yayi ya shiga a bakin ƙofar ya ɗan tsaya tare da kallon cikin ɗakin har yanzu tana nan inda ya barta, tsaki yaja ya watsa mata kallon takaicin cikin muryar bacci da bai gama sakeshi ba yace.
“Kin isheni fa, gwara ki haÉ—iye kukanki, dan hautsuna min kai yake yi, zan karyaki in kika fusatani, dan ba yadda za'ayi ki hanamu bacciâ€. Cikin kukan ta yunÆ™uro zaune fuskantar da tayi jazir ido a kumÉ“ure take kallonsa cikin mamakin muguntarsa.
Kai ta kife a jikin gado tare da sakin wani sabon kuka mai cike da rauni gajia da kukan.
Bathroom ya wuce, wanka yayi tare da al'wala ya fito.
parlour ya wuce inda bag É—insa yake, jallabiyar da ya zura É—in bayan yayi wanka ya cire, ya kimtsa cikin tattausan riga da wando tare da bin jikinsa da sassayan turarensa, numfashi mai sanyi ya fesar yana zama kan one sitter, ya lumshe ido sai kuma yayi saurin buÉ—esu sabida jin sautin ringing É—in wayar Fariyda da na Yah Amin cikin sauri ya jawo wayar Fariyda ganin wanda ke kiran.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.