Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 48 of 86
Kwantar da Zaitoon É—in tayi gefen Zaid tace.
“To Saida safe ko Fariyda yau zan kwana da kewarku, kwana hamsin harda É—ori ban kwana ni kaÉ—ai ba sai yauâ€.
Ido na cika da hawaye tace.
“Goggo Dada muma zamu yi missing naki badan Abba ne yaceba, da naci gaba da zama a É—akinki har gaban abadan inyi biyayya wa umarnin iyayena da suka nuna isarsu kan sake dawo dani gidan dan zama cikinku yafi min nan dadiâ€.
Cikin sanyi tace.
“Ai hakan shine ya dace Fariyda kuma duk ai muna tare, yadda kika yi haÆ™urin karÉ“ar hukuncin da iyayenku suka yanke Allah ya baki ikon wanzar dashi ya Æ™ara miki haÆ™uri da biyayyar aureâ€.
Daga nan ta fita.
Salim da tunda Mahmoud ya fita bai tashi daga inda suka zauna bane ya ja dogon numfashi tare da cewa.
“Jishi wai zan ja mana raini in nace ina son Æ™awar Fariyda, to ko ya manta cewa shi Fariyda matarsace ne kamâ€.
Kwaffa yayi kana ya miƙe yayi cikin gida.
A nitse ya shigo parlour ya zura hannunsa duka biyu cikin aljuhun 3 quarter É—in jikinsa.
Ƙofar ya maida ya rufe tare da kashe wutan parlour kana ya nufi corridorn ɗin ɗakinsa.
Cikin nauyin baccin dake fizgarta, take jijjigashi, tare da miƙewa tsaye ta fara ɗan tafiya tana hamma.
Gaban dressing mirror ta kuma zuwa wayarta dake kai ta ɗauka sha biyu harda rabi, sai kuma ta juya a hankali jin ya ɗanyi shiru, bakin gadon ta taho dan kwantar dashi tana sunkuyowa ya miƙe sawunsa da ƙarfi tare da sakin kukan da yafi na forkon.
Da sauri ta sauƙeshi daga bayan ta zauna bakin gadon tare da fara kiciniyar sa masa nannan ɗinta dake tsaye cir yasa dole sai ta sunkuyo kansa, kai ya fara jujjuyawa yana mai ƙara kukan, ɗagashi tayi ta aza a kafaɗa tare da jijigashi, da sauri ta sauƙeshi dan ƙara ihun ma yayi.
Kwantar dashi ta kumayi tare da sunkuyowa kanshi ta kai mishi bakin nannan ɗin, jin ya kama e yasata sauƙe ajiyan zuciya tare da lumshe idonta dake cike da baccin bashin da batayi jiyaba saboda rashinsu a kusa na safe kuma Mamy ta hanatayi da faɗarta da korota ta dawo, da sauri ta buɗe idonta jin ya kuma saki nannan ɗin tare da cilla ihu da wurza sawunsa.
Miƙewa tsaye tayi dashi tare da maidashi baya.
Habawa kamar an sa masa batir yadda ya saki ihu ne yasata sauƙo dashi da sauri ta zare misa hular kansa tunowa da abinda ya faru da Zaitoon.
Ba komai a hularsa ta faÉ—a cikin muryar bacci.
Ido ta zuba mishi cike da rasa yadda zatayi dashi, duk iya kar yar hikimar ta tayi ta kasa sashi shiru.
A baya ta kuma medashi tare da cewa.
“Yah Allah na, Zaid meke maka ciwo neâ€. Ta Æ™are maganar cikin tausayawa.
Lokaci ɗaya hawaye ya fara cika mata ido, ta sani da a ƙasa suke da tuni Ummi da Goggo Dada sun karɓeta har su rinka ce mata ta kwanta tayi bacci.
Da sauri ta miƙe tsaye dashi saboda jin yadda ya kuma callara ihu da ƙarfi har bakinsa da jikinsa duk na rawa.
Goyansa tayi tare da fara zirya dashi a tsakiyar É—akin.
Tana mai jin tsoro na rufeta. Time ta kuma dubawa, ƙarfe biyu harda rabi awa biyu kenan cib yana kuka, kuma ba sauƙi a kukan sai ƙaruwar da yakeji ma.
Ganin yadda yake haɗa zufane yasa ta tuɓe mishi kayan jikinsa ya zama dagashi sai Pampas. ruwa ta ɗauka ta bashi amman ina sai buge water bottle ɗin nasuma yayi.
Gafen Zaitoon ta yi da sauri ganin ta tashi zaune tana sosa kai tana fara kwaɓe fuska ɗan uwan ya tasheta cikin baccinta.
Goyon Zaitoon É—in tayi kana ta rungume Zaid É—in yana kuka itama tanayin hawaye.
Can cikin baccinsa ya fara jiyo kukan, a hankali ya juya gefen dama zuwa hagu.
Da sauri ya tashi ya zauna jin kamar muryar Zaid ne ke kuka.
Cikin rawan jiki ya diro ƙasa, tare da jawo jallabiyarsa ya zira yana mai gyarashi yayi ƙasa dashi.
Jin kamar kukan a nan sama yakene yasashi tuna cewa Abba ya dawo dasu nan sama.
Cikin sauri ya buɗe ƙofar ya fito corridorn, da sassarfa ya fito parlour saboda kukan da yaji ƙarfinsa ya wuce na ƙaramar wahala, da ƙarfi ya fara Knocking. Ina bata jinsa saboda sautin kukan Zaid ya toshe jinta, kana itama ɗin kuka take yi tare da zirga-zirga ga Zaitoon dake bayanta da yasa ta fara jin ƙirjinta na amsawa.
Cikin ƙarfi yaci gaba da bubbuga ƙofar tare da cewa.
“Ke ki buÉ—eâ€.
Da sauri ta isa bakin ƙofar jin kamar ana bugawa, da sauri ta buɗe jin bugawar akeyi, da sauri taja da baya ganin shine. Tsakiyar ɗakin ta koma tare da ci gaba da zirga-zirga ido cike da bacci da tausayin ɗan nata kana da ruwan hawayen dake ta sintiri.
Da sauri yabi bayanta tare dasa hannunsa ya amshi Zaid É—in ya É—aurasa a kafaÉ—arsa cikin faÉ—a yace.
"Me kikayi masaâ€.
Ido na zubda ƙwallan tace.
“Me zanyi masa kumaâ€.
Yana ƙara jijjigashi yace.
“To menene ya sameshi kin tsaya kina kuka bazaki faÉ—a min baâ€.
Ido na zubda ƙwalla tace.
“Ban sani baâ€'.
Zare mata ido yayi tare da cewa.
“Shima kin bar kunamar ta cijesa kenan dan baki san zafin É—abaâ€.
Tana sauƙe Zaitoon ta kalleshi da idanun masu cike da bacci da hawaye tace.
“Nima fa ina sonsu tunda ni na haifesuâ€.
Cikin tsawa yace.
“Kika haifesu ko akayi CS aka cire su, da kike wani jin kanki kin haihu keda Doctors sukace bazaki iya haihuwaba, ta ina kika san zafinsu da har zakiyi min gautsin bakiâ€.
Cikin rawan murya tace.
“CS É—in ai cikinka aka tsaga aka ciresu ba nawa baâ€.
Da ƙarfi ta rumtse idonta tare da sa hannunta duka biyu ta kama kanta ganin wani irin fusata da yayi, sai kuma ta buɗe idon a hankali jin yana cewa.
“Innalillahiâ€. Saboda wani irin karkarwa da Zaid ya fara tare da Æ™andarewa yana mai tsala ihu tamkar ransa zai fita.
Da sauri ya juya ya fita.
Daukar Zaitoon tayi tare da maramasa baya.
Da ƙarfi yake bubbuga ƙofar parlour Ummi, Goggo Dada da tun ƙarfe uku take tashi ne yasa idonta biyu yanzu da uku da rabi tayi kunne ta kasa sai kuma ta miƙe da sauri ta nufi parlour.
Jiki na rawa ta buɗe ƙofar saboda jin yadda Zaid ɗin ke kuka.
Suna shiga tasa hannunta ta amsheshi tare da cewa.
“Yah Salam me yasameshiâ€.
Yana bin bayan Goggo Dada yace.
“Waya san me ta bari ya cijeshiâ€.
Da sauri Ummi dake side ɗin Abba ta fito rike da carɓi.
Fariyda dake kuka ta kalla tare da cewa.
“Yi haÆ™uri zoki zauna me yasameshi, dena kukanâ€.
Murya na rawa tace.
“Ummi bansan me ya sameshi ba, wlh na duba jikinsa duka ba abinda ya cijesa, tun sha biyu saura yake kuka har yanzu. Ummi ga yadda yake yi fa kuma yana cewa wai na bar wani abu ya cijesaâ€.
Cikin tausayin ta da ya rufeta ta zaunar da ita.
Da sauri Goggo Dada ta kai bakinta saitin kunnensa tare da fara hura masa iskan bakinta cikin kunnen nasa, hyyyymmmm yaja kukan da ƙarfi sai kuma ya sauƙeshi a hankali, ƙara hura masa iskan tayi ba tsayawa, in seconds yayi shiru.
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da zagayowa bayan Goggo Dada yana kallon fuskarsa kanshi ya fara shafawa tare da hura masa iskan bakinsa ganin goshinsa dake cike da zufa.
Ummi tace.
“Cikinsa ne yake ciwoâ€.
Zaitoon ta karɓa a hannun Fariyda da har yanzu hawaye take yi. A hankali ya fara ajiyar zuciya, tare da fara lumshe idanunsa.
Ganin haka ne Goggo Dada ta zauna tare da kwantar dashi kan cinya.
Da sauri ta kuma kai bakinta kunnensa ganin zai ci gaba da kukan, haka sukayi tayi har sai ƙarfe huɗu da kwata ciwon cikin ya lafa ya samu sauƙin nan da duk ciwo in asuba tayi zakaji salama.
ÆŠakinta taje ta kwantar dashi kana ta dawo ta amshi Zaitoon ma da ta maida baccinta.
“To kuje kuyi al'wala tunda ya samu bacci.
Yana kallon Ummi yace.
“Ni nafi son mu tafi asbiti neâ€.
Tana kallon Fariyda tace.
“Wuce kuje kuyi salla, in kinyi salla kiyi baccinki,
Kada ya cutar dake. Sai da safe za'a kaishi asibitin.
A dole ya yarda da tsarin Ummi suka fita.
Ita kuma Ummi ta koma wurin Abba tare da mai bayanin abinda ke faruwa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.