Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 77 of 86
Zama tayi a bakin gadon gami da sauƙe numfashi. Mitsssss taja tsaki, yau kwana huɗu kenan wayarta bata hannunta, kaɗaicin rashin wayar ne ya sata miƙewa tsaye. Parlour ta fito, a hankali ta ɗan fara dube-duben neman wayarta da batama san da ita yake fitaba.
Da sauri ta juyo jin an turo ƙofar ganinsa ne yasa ta ɗan miƙe tsaye daga sunkuyen da take tana ƙoƙarin jawo drawer Centre table ɗin Jakar system nashi ke ciki wanda ciki yake ajiye wayartan in yana gida in zai fita kuma ya fita da ita. A hankali ya ƙaraso cikin parlour yana tsareta da ido daga sama har ƙasa, kan takalminsa da sukayi mata uban yawa ya tsaida idonsa.
Da sauri ta É—an sunkuyar da kanta saboda ganin yadda ya tsaida idonsa kan sawun ta, da suke can cikin takalmi da É—an mitsilili sawunta suka É—an wuce rabin takalmin.
Kanshi ya É—ago ya kalleta itama kallonsa tayi ba tare da ta cire takalmin ba.
“Uban me kikeyi min anan?â€. Ya faÉ—a yana tsareta da gajiyayyun idanunsa.
Baki ta É—an tura ta juya lumsassun idanta.
“Ni wayata nake dubawaâ€.
Zama yayi bisa 3 seatter haÉ—i da cewa.
“Ok bincike ma kikeyi min kenan in na fitaâ€.
Ya ƙare maganar da zaro wayarta daga ajihunsa.
“Wayar nan dai tawace, dan haka ka bani abuna, ina da buÆ™atar ta tunda ba kai ka saya min itaba, bare ka riÆ™eta dan kuÉ—inka, kuma ko na mutu baka da gadona bare kace ka riÆ™e a madadin gadonkaâ€.
Tayi magnar da murguɗa baki ta ƙara matsowa gabansa sosai ta riƙe ƙugu da hannu ɗaya.
Idonshi ya kuma tsaidawa kan takalminsa tare da É—an taune gefen lips É—inshi yace.
“Gata nan in kina da Æ™arfi ki Æ™wataâ€. Da sauri ta matso gabansa saboda ganin yadda ya riÆ™e wayar da yatsu biyu rak, yatsarsa ma nuniya da kuma doguwar yatsarsa ta tsakiya a tsakaninsu ya matse wayar ya É—aga hannun sama kaÉ—an.
Hannunta tasa ta riƙo wayar tare da ja, da sauri ta kuma sa ƙarfinta duka dan jan wayar da yake riƙe da ita da yatsu biyu, amman ina ta kasa, ɗaya hannun tasa ta fara kiciniyar kwaceta. Uhmmmmmm taja numfashi mai nauyi da ƙara matsoshi da kyau har guiwarta na taɓa nashi cikin haki ta sunkuyo dan tsawonta yafi na hannun nasa tunda a tsaye take. Hannu duka biyu tasa ta damƙo wayar tare da janta da ƙarfi. Ko kallonta baiba haka kuma ko motsi wayar batayi ba, duk ragowar ƙarfinta tasa ta fizgo wayar, a hankali ya ɗan sake mata wayar in one second, hakan ne yasa ta koma baya da ƙarfi saboda bada ƙarfinta da tayi dan jan wayar da batayi tunanin zai sake mataba. Da ƙarfi ta rumtse idonta ta saki ƙara sabida jin yadda tayi luuu tayi baya zata faɗi.
Cikin zafin nama yasa hannunsa ya fizgota sabida ganin inda kanta zai sauƙa in ta isa ƙasa dai-dai bakin kan Centre table ɗin da yake da ƙaifi.
Wasu irin numfarfashi suka fesar a tare lokacin da ta dawo gaba ta abka kan jikinsa tayi lip.
Tana mai sauraron bugun zuciyarta yayinda shima bugun zuciyarta yake ƙididdigewa wanda hakan yasa shi yin shiru kamar yadda tayi shiru ta manne a jikinsa tayi lip, gefen lips ɗinshi na ƙasa ya kamo tare da fara yi masa wani irin tsotsar gamayyar fushi da hargitsa zuciya.....
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 39
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Dib! Dib!! Dib!!! Haka zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da kuma sauri sauri saboda firgita, har lau kuwa ta kasa janye jikinta daga gareshi.
Shi kuwa Mahmoud har lau gefen lips ɗinshi yake tsotsa da ƙarfi-ƙarfi da kuma sauri-sauri sai dai yanzu ya bar lip ɗin na ƙasa ya komawa na sama, wayartan da har yanzu yana hannunsa ya matse da ƙafi.
Kanshi ya maida ya jingina da jikin kujerar tare da rumtse idanunsa da ƙarfi.
A tare suka sauƙe numfashi, gyara zamansa yayi ya zura mata gajiyayyun idanunsa kan wuyanta da tattausan gashin ƙeyarta ke kwance sulup-sulup ganin har yanzu bata ko motsa ba.
Sai karkarwa da jikinta yake yi, numfashi kawai take ja tana fesarwa a gaggauce wanda take jansa da ni'imtaccen ƙamshin turarensa.
“Bakiji ciwo ba dai ko?â€. Yayi mgnar yana kauda idonsa daka kanta.
Tana jinsa Amman ta rasa sanadin kasa yin mgnarta da kasa motsinta.
“Ke bakiji ciwo bafa! Bana son muna funci Kisa yanzu Ummi tayi fushi daniâ€. Har lau bata ce komai ba, a hankali ya É—an dawo da kallonsa kanta, lip take kwance a jikinsa kanta na manne bisa Æ™irjinsa ta cusa hancinta tsakanin wunyasa da kafaÉ—arsa, É—aya hannunta na kan É—aya kafaÉ—arsa da Æ™irjinsa.
“Ke Farriyyah kina jina?â€. Cikin tattaro kuzarinta ta gyaÉ—a masa kai, alamun eh tana maijin idonta na lumshewa.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da cewa.
“Kinji ciwo ne?â€. Kai ta kuma girgiza masa a hankali.
Cikin fesar da numfashi ya É—an gyara zama tare da yin balance kan kujerar ya fara zame jikinsa, cikin kauda kai yace. “Ke tashi min a jikinaâ€. Kai ta kuma gyaÉ—a masa alamar to, ba tare da ya kuma kallon ta ba yace.
“Tashi muyi magna?â€. Kai ta kuma gyaÉ—a masa har lau kuma bata yi koda yunÆ™urin tashi bama. Numfashi mai zafi ya fesar ya maida bayansa ya jingina da jikin kujerar yana mai jan jikinsa.
Hakan yasa kanta ya sauƙo kan ƙirjinsa dai-dai kan nimple ɗinsa da har yanzu yake ciwo.
“Washhhhhh, zaki kasheni faâ€. Har lau bata motsaba, hakane yasa shi yunÆ™urawa hannunsa yasa ya rabata da jikinsa cikin tsuÆ™e fuska yace.
“Zauna muyi magnaâ€. Sai kuma ya Æ™are maganar cikin É—an tausasa lafazi sabida tuno shawar Sulaiman da kuma neman mafita.
Gefen kujerar ta kife kanta tare da É—an buÉ—e lumsassun idanta jin yadda ya ke kiranta da sunan da bata saniba, kamanceceniyar sunan da natane da kuma sanin ba kowa a wurin yasa ta fahimci ita yake kira.
“Farriyyah magna nake so muyi dake, don samun mafita akan matsalata da taki matsalarâ€. Kai ta gyaÉ—a masa tare da zubawa fuskarsa ido.
Cikin É—an sasssauta fuskar faÉ—an yace.
“Ni inaga Sa'ad shine mafitar matsalar mu, tunda yana sonki, ki bari yazo ku zauna ku fahimci juna, in ku dai-daita ni zan miki walicci kuma kin san hakan ya halatta a shariya, ko ba wannan ma ai ke Æ™anwace a gareni, ni mai iya aurar da kenan, in Kuma bakya son Sa'ad ga Mujahid shima yana sonki, kuma shi zai bamu haÉ—in kai ayi aurenku dashi a sirrance, ta yadda iyayenmu bazasu fahimci komai ba har sai an É—aura aurenâ€. Cikin sanyi tace.
“Me zan cewa Baba malam? Mamy zata tsine min faâ€. Ciken dakewa yace.
“Kada ki damu, ni zan gaya musu duk abinda ya dace, zan kareki ni zan maida komai a kaina, yardarki kawai nake buÆ™ata ki zaÉ“i wanda kikeso a cikinsu, in Kuma akwai wani da kikeso ni na baki dama ki fidda wanda kikeso ni zan aura miki shi in huta, ai dama Shari'a ma cewa tayi in miji ya saki mace ta zauna tayi zaman inda a gidansa in ta samu wani zai iya aurar da ita, yanzu faÉ—a min wa kikeso a ciki Sa'ad ko Mujahidâ€.
Ido ta zuba wa laɓɓansa da suke cikin zagayeyyen sajensa da ɗan gemunsa.
“Yah Muhajid zaifi, shi zai riÆ™e min su Zaid kamar yadda ubansu zai riÆ™esu, tunda dama shi É—an uwananeâ€.
Wani irin kallo yayi mata mai cike da fushi.
“Hmmm a zatonta zai bar mata su Zaid kenan tayi aure dasu a wani wurin? Ina Mujahid ya samu tarbiyyar kirki da zai bar masa ragamar tarbiyar ƴaƴan ɗan uwansa dan baya duniya Amman bari ya bita a hakan, ganin kallon da yake mata ne yasa ta ɗanyi ƙasa da kanta.
“Kada ki damu bari shima Sa'ad É—in yazo wata Æ™il kiga yafi miki Mujahid É—inâ€.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Shima ai yana sona, amman auren Yah Mujahid shine mafita, zai riÆ™e mana su Zaid, kuma ko su Baba Malam bazasuyi fushi sosai ba in sunji shi ka aura min tunda shi É—an Æ´ar uwarsune sun san shi sun san asalinsa da tarbiyarsaâ€.
Yana mai taɓe baki yace.
“Yanzu dai shi kikeso kenanâ€. Ido ta É—an lumshe saboda ganin yadda ya zuba mata nasa manyan idanun cikin nata cikin sanyi tace.
“Eh ina sonshi tunda dama shi....â€.
Da sauri ya miƙe tsaye saboda jiyo muryar Zaid da ya saki kuka da ƙarfi.
Da ido ta rakashi har ya shige bedroom É—in.
Lumshe idonta tayi tare da maida kanta ta kife dai-dai inda cinyoyinsa suke inda ya tashi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.