Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 8 of 86
Gyara zama Aminullah yayi tare da zaro car key É—insa a aljihunsa ya watsasu kan Santer table.
Sai kuma yayi saurin juyowa ya kalli Mahmoud tare da cewa.
“Kai Mahmoud tashi in aike ka, kada dare ya Æ™arayiâ€.
Ya ƙare maganar yana kallon time ganin har tara saura ne yasa ya kuma kallon Mahmoud dake ce masa.
“Tohâ€.
Ya faÉ—a yana zarar key É—in da ya ajiye yanzu.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ina motarka da zaka É—auki tawaâ€.
Kai ya É—an jujjuya tare da cewa.
“Key É—in basa kusaâ€.
Ya Æ™are maganar yana miÆ™ewa tsaye ganin Yah Amin É—in nasa na Æ™ara duba time tare da cewa. “Kayi sauri kuma ka tafi a hankali faâ€.
Kai ya gyaÉ—a mishi sai kuma ya zuba mishi ido jin ina zaije masa.
Salim kuwa hannun Mahmoud ɗin ya kamo ya miƙe tsaye tare da cewa.
“Mu tafiâ€.
Idonsa na kan Aminullah É—in yace.
“Menene aiken? Ina zamujeâ€.
Yana É—an duba wayarsa dake ringing kiran Fariyda daya shigo yace.
“Yauwa gata ma tana kirana.
Fariyda zaka É—auk...â€
Shiru yayi da bakinsa ba tare da ya ƙarisa mgnar tasaba.
Jin yadda Mahmoud É—in ya watsa key É—in kan Centre table É—in.
Tare da tsuƙe fuska sai kuma ya koma ya zauna yana mai ƙara tsuƙe tsukekkiyar fuskarsa cikin tsayuwar ra'ayinsa da furuci yace.
“Bazan jebaâ€.
Cikin sanyi Aminullah É—in yace.
“Haba Mahmoud meyasa?â€.
Murya a fadace yace.
“Ni drivernta ne? Ko bawanta?â€.
Cikin sanyinsa da jin tsoron tsana da gabar dake tsakanin ƙanin nasa da matarsa yace.
“Ba daya cikin biyu, sai dai kai Æ™aninane a zatona dai nakai in aikekaâ€.
Kanshi ya sunkuyar yana latsa wayarsa yace.
“Eh ka kai, amman ita bata kai in É—aukato ba kamar wani bawan gidansu, duk inda kake so ka aikeni zanje amman banda aikentaâ€.
Sai kuma ya É—an É—ago ya kalli Umminsu jin tana faÉ—in.
“Ni Wallahi gardamarka da kafiyarka tsoro suke bani Mahmoudâ€.
Yana mai yin ƙasa da kansa yace.
"Wallahi bazanje É—aukota ba, in zai tashi yaje ya É—aukota ya tashi in Kuma bazai jeba ya barta a can har illa masha'Allah Ni ban damuba, gidan ma yafi min daÉ—i da faÉ—i da sa'ada in bata nanâ€.
Ido Goggo Dada ta zuba mishi cikin ƙara mamakin tsaurin idonsa.
Shi kuwa Aminullah shiru yayi tare da lumshe idanunsa haka nan yake jin hawaye na tsatstsafo mishi.
Ganin yadda yayine yasa Salim sa hannu ya ɗauki key ɗin tare da ture kan Mahmoud da ƙarfi kana ya kalli Aminullah ɗin cikin faram-faram ɗinsa yace.
“No Yah Amin kada ka damu bari inje in É—auko mana Our Aunty É—inmuâ€.
Cikin tsuƙe fuska ya kalli Salim ɗin tare da cewa.
“Our Aunty kai da uwar waye ta zama our Auntnku?â€.
Da sauri Salim yace.
“Da kai manaâ€.
Ture Salim É—in yayi ya wuce ta gefenshi yana faÉ—in.
“Banza asararre kada ka sake sani a cikin list É—inka, in kaga dama kaje ka kirata da Mama ta zama uwar ka, Amman banda ni nan Mahmoudâ€.
Kusan duk da ido suka rakasa har ya fice daga parlour.
Numfashi mai nauyi Aminullah ya fesar lokacin da Salim É—in yayi murmushi tare da fita.
Ummi kuwa tagumi tayi Goggo Dada ce ta É—an gyara zamanta tare da cewa.
“Kada wannan abin ya dame ka Aminullah kasan shi Mahmoud mutum ne mai fusatacciyar zuciya. gwara a kiyaye abinda zai haÉ—ashi da Fariyda dan wlh tsab zai iya zaginta yayi mata gwal mu ya barmu da jin kunyaâ€.
Cikin sauri Ummi tace.
“Sosai ma in an barshi zai aikata yanzufa ji yadda ya zagi Salim wai ta zama uwarka ai wannan zagine. Amman ba komai zan yi maganinsa wlh na gaji da lamarin su dole in kai Æ™orafi wurin Abbansu, da can gani nake ni zan iya sasanta tsakaninsu amman yanzu nasan bazan iya ba, kawai Abbansu zan gaya ma ya shiga lamarâ€.
Sai kuma tayi shiru jin abinda Aminullah ke faÉ—a cikin amintacciyar muryarsa yace.
“A'a Ummi dan Allah kada ki gayawa Abbanmu, wlh in anyiwa Mahmoud faÉ—a a kan Fariyda tsanar zata hauhawa zai iya cewa zai kai mata hannufa dan gani zaiyi ta haÉ—ashi da kuâ€.
Cikin sanyi Goggo Dada tace.
“Gsky nima ban goyi bayan a sanarwar Abbansu ba, dan kin sanshi fushinsa Mahmoud ya É—auka ga riÆ™o, kar yaje yayiwa Mahmoud faÉ—an da zai sa ya Æ™ara tsanarta har tsanar ta shafi Æ´aÆ´anta!â€.
Cikin sauri Aminullah ya fara girgiza kai tare da cewa.
“A'a Goggo Dada in sha Allah haka bazai taɓa faruwaba. Mahmoud bazai taɓa tsanar jinina ba, wlh in dai muddin kika ga Mahmoud ya tsani ƴaƴan Fariyda to wlh kada kiyi haufi shegune Fariyda ta shigo min dasu gidana, kada kiyi haufi ba kuma janina bane, Amman muddin jininane ƴaƴanane Mahmoud bazai taɓa tsanarsuba duk tsananin tsanar da zaiyiwa Fariyda in dai nine uban yaran bazai tsanesuba.
Wannan shine babban abinda ke sawa inji bana damuwa da rashin shirinsu a da Amman a yanzu abin ya É—an fara damuna.
Amman duk da haka dan Allah Ummi kada ki gayawa Abbanmuâ€
Cikin gamsuwa da hujjojinsu tace.
“In sha Allah bazan faÉ—a masabaâ€.
Ƙarfe goma dai-dai suka shigo gidan.
A a bakin ƙofar parlour suka samesa zaune bisa kujerar silver dake wurin yasa system nashi a gaba.
Ko inda yake bata kuma kallaba ta wuce da babbar layder a hannunta.
Sai Zaitoon dake bayanta.
Salim na biye da ita, riƙe da Zaid da yake yan koke-koke.
Da sauri yasa hannunsa ya amshi yaron tare rungumeshi a ƙirjinsa.
Gefe ya ɗan ture system ɗin nashi, kana ya miƙe kan kujerar tare da kishingiɗa yana gyarawa Zaid kwanciya tare da ɗan shafa bayansa a hankali ya fara rage sautin kukan cikin two minute yayi shiru.
Shi kuwa Salim da ya isa ƙofar corridorn parlour kai ya ɗan jujjuya cike da sanin halin waye Mahmoud ya fara taka steps ɗin haurawa sama dan ganin ƙofar da zai sadasa da cikin parlour a rufe.
Sha ɗaya dai-dai Aminullah da Fariyda suka meƙe tsaye tare da yiwa su Ummi Saida safe.
Cikin kulawa Ummi tace.
“To Allah ya bamu alkhairi, Fariyda mun gode sosai da tsaraÉ“an Baba Malamâ€.
Ta ƙare maganar tana kallon manyan sallaya guda biyu ita ɗaya Goggo Dada ɗaya, sai tattausar jallabiya da turare na Abba sai turare na Samira.
Sai kuma jallabiya guda biyu da ke hannunta da sallaya da yan kunnen gold na Zaitoon da Baba Malam ya saya mata tsaraba.
A hankali ya buɗe idanunsa tare da ƙara rungume Zaid.
Idon ya kuma lumshewa lokacin da Yah Amin É—in nashi ya isa kansa cikin sanyi murya yace.
“Dare yayi fa Mahmoud tashi ka shiga kawo shi nan koâ€.
Kai ya gyaɗa masa tare da miƙa mishi yaron kana ya miƙe ya shiga.
Ƙofar ya maida ya rufe.
Su kuwa Part É—insu suka nufa.
Kasan cewar gidan babban gidane na gasken gaske.
Shi yasa akwai tazara tsakanin part É—in nasu.
Idan gate É—in gidan biyu ne.
Ɗaya ta yamma ɗaya ta gabas wanda yake ta gabas ɗin shine kan babban titin da zai sadaka da masallacin jumma'ar Nassarawa G.R.A, daga wajen gidan ma wasu tamfasa-tamfatsan shagunane a ƙalla su 12 shida a ƙasa shida a sama wanda aka cikinsu maƙil da kayan ƙawa na mata yan ƙwalisa sai shagon Hafiz na ɗaukar hoto dake tsakiyarsu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.