Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 85 of 86

Tana fita kiran Abba na shigowa, da sauri ya gyara zamansa ya sauƙe sawunsa ƙasa kana ya amsa kiran cikin girmamawa yace.
“Barka da safiya Abba”.
Abba yace.
“Barka dai Mahmoud ya iyalan naka”. Yana ɗan yin ƙasa da kansa dan kallon fatan jikinsa yace.
"Alhamdulillah yasu Ummi na, ina Goggo Dada”.
Abba yace.
“Duk muna lfy gamu nan muna shan tea duk suna jinka, ya jikin Zaid”.
Yana gyara zama yace.
“Da sauƙi sosai Abba yanzu suka fita zasuje suyi breakfast”.
Ummi da Goggo Dada ne suka haɗa baki cewa.
“A to Barka Allah ya ƙara lfy, yanzu kam sai shirin dawowa ko”.
Mahmoud yace.
"Eto dole zamu ɗan ƙara zama dan su ga yanayin aikin”. Abba yace.
“Zadai ku dawo Kafin auren Salim ko, kaga itama Fariyda yar uwarta Salim ɗin zai aura yau saura kwana goma ne cib fa”. A hankali yace. “In sha Allah Abba”. Hafiz da yanzu ya shigo cikin shirin tafiya makarantane yace.
“Uncle ɗazu na kira layinka busy”. Cikin fara gajiya da magnar yace.
"Ina yin waya da Dr Avinash ne”. Daga nan suka ɗan gaisa ya katse kiran.
Sulaiman ya kira bayan ya kwanta yana ɗagawa yace.
"Kai wai ya jikina?”. Cikin mmki Sulaiman yace.
“Ya jikinka kuma? Ni zaka tambaya kuma?”. Yana jan tsaki yace.
"To wa zan tambaya?”. Yana gyara zama yace.
“Dr Avinash mana”. A hankali yace.
Na kira ɗazu yace in bari sai da dare in kirashi video call sabida zasu shiga tiyata”. Numfashi Sulaiman ya sauƙe tare da cewa.
"Maganinka ya ƙarene?”. Kai ya jujjuya kamar yana gabansa a hankali yace. "Ay yanzu ba maganin da ake bani, ka manta cewa su kansu saninsu ya tsaya”.
Kusan 14 minute sukayi suna waya da Sulaiman daga bisani sukayi sallama.
Bayan kwana biyu da yamma baya gidan haka yasa take zaune a parlour tun bayan bawa Zaid maganinsa, waya take yi da Salma.
"Amman dai kin san bikin nan ya kusa ko? Kuma ina sonki a kusa, dan Allah kiyiwa Appiy Zaid magna ya tsaida ranar dawowarku”. Baki ta taɓe tare da cewa.
“Ke nifa bama mgna dashi, kawai dai nasan zamu dawo kafin nan tunda dai jikin Zaid da sauƙi sosai”. Cikin zaƙuwa da kewa tace.
“Yanzufa kusan watanku ɗaya”. Fariyda tace.
“Yaune ma mukayi 30 days cib a Ahmedabad”.
Jin shigowarsa ne yasa ta wuce bedroom.
Washe gari da dare wuraren sha daya
Wayarsa dake Vibrating ya zaro tare da picking call ɗin Salim.
“Wai Dan Allah sai yaushe zaku dawo ne, next week nefa bikin nan”.
Cikin fara jin bacci yace.
“Nima ina son samun ɗaurin aurenka.
To amma kuma yau ne muka koma, ganin Dr kuma yace dole sai mun ƙara kawoshi next week dan zai ƙara tabbatar da samun lfyar Zaid ɗin har cikin jikinsa a matsayin na miji, wannan shine babbar matsalar da zata hananin dawowa”. Da sauri Salim ɗin yace.
“To ko dai a ɗaga auren ne sai kun dawo”. Mahmoud yace.
“Ai kai baka da kai, su Abba da Baba Malam bazasu yardaba, ba komai ayi ina nan zan tayaka da addu'a”.
Yana ɗan kallon Sulaiman daya shigo yace.
“To ya zanyi dole in haƙura zanyi maleji da Sulaiman, gashi ma jiya yazo”.
Daga nan dai suka ɗanyi waya su duka uku kana sukayi salla.

Ranar lahadi da dare tunda ya shigo parlour yaji sit tamkar ba kowa, bisa dukkan alamu da ita da yaran duk sunyi bacci ne.
Kiran Sa'ad dake shigowa ne ya sashi jawo wayar.
“Barka da dare, Yah Mahmoud ya gida ya Zaid da jiki”. Yana kunna TV a taƙaice yace. “Alhamdulillah”. Cikin girmamawa irin na neman biyan buƙata Sa'ad yace. “Babban Yaya, Fariyda fa”. a taƙaice yace. “Sunyi bacci”. da sauri Sa'ad yace. "Big broz a bani number ta, ko dan in dena takuraka”. Cikin iya kar gskyarsa yace. “Meyasa da kazo baka amshi number ta ba”. Da sauri yace. “Bata bani ba, cewa tayi muyi ta mgna da wayar nan ɗin”. cikin ƙosawa yace. “Ni bani da number ta.” Daga nan ya katse kiran. Zuru Sa'ad ɗin yayi ya kasa koda janye idonsa kan wayar, cikin ƙarfin hali ya kuma kira. “Uhmm”. Shine abinda Mahmoud yace.
A hankali ta shigo parlour saboda ƙishin daya fito da ita ɗaukan ruwa a fridge. Ido ta zuba mishi ta tsaya gefenshi kaɗan ta bayan kujerar, yau kwana uku kenan bata sashi a idoba, dan kafin ta farka ya fita, kafin ya dawo kuma tana ciki, fuska ya tsuƙe cikin sauri ya dakatar da Sa'ad dake ƙara jaddada masa roƙon indan sunyi aure da Fariyda yana son a bashi su Zaid, murya a kufule yace.
“In baku su Zaid kai, yanzu inma ita tacema zan baku su Zaid sai ka yarda, ita da bata da hankali tayi tunanin zan bata su, kaima da nake ganinka kamar mai hankali kayi tunanin in tayi aure zan ɗauki yarana in bata. To ai ko Mujahid ɗan uwanta ta aurama wlh su Zaid ko ziyara saidai ita tazo ta gansu in taga dama, in kuwa bata ga damaba tayi zamanta da ma can ni ban nemeta ba, wannan ma ai mgnar banzace ƴaƴan ɗan uwan nawa, to yaushema yaran suka ishemu da har zamu bada su, tukun ma kasa daɗin ɗa kuwa da kake zaton in baku yarana har biyu, kamar wasu masar sadaka”. Ido Fariyda ta zaro cike da mmki da tashin hankali kenan ma shashantar da ita yayi da cewa zai bata su Zaid in tayi aure a hankali ta fara taƙowa tana matsowa inda yake ganin yadda yaja
Numfashi mai nauyi ya fesar tare da ci gaba da faɗin.
Ban gamsu da wani ɗan adam na duniya ba yayi min tarbiyyar yarana ba, bare kai da ban wani sankaba ko shi Muhajid da shima tarbiyyar yake buƙata a ƙara bashi, to bari kaji ai ko Sulaiman ko Salim ne suka aureta wlh su Zaid bazasu koma gidansu ba, kai duk faɗin duniya banga mahaluƙi da zai aureta in ɗauki yarana in basu ko ziyara bazasuje bare ayi musu kallon agololi karma ka sake min wannan mgnar banzar”. Yana kaiwa nan ya katse kiran. Ido cike da kwalla tace. “Ta ya zakace zaka rabani dasu, akan me? ba anan kace min in na yarda da Yah Mujahid ko Sa'ad ayi auren a sirri ba, zaka bani su Zaid sannan yanzu kace babu wanda zan aura a duniya da zasuje wurina,tayaya zakace ko ziyara bazasuje inda nake ba, kenan rabani zakayi dasu.”
Cikin tsareta da ido yace.
"Ke dan baki da hankali sai ki yarda cewa zan baki su”.
Murya na rawa tace.
“Kai kuma sai ka iya rabani dasu kenan, ai ya Mujahid kam ɗan uwana ne, kuma ka sanshi kuma gari ɗaya ake”. A kufule yace.
"Wannan ɗan iskan ne zan bawa ragamar tarbiyar ƴaƴana”. Cikin zubda ƙwallan murya a raunace tace.
"Wallahi Yah Mujahid dai ba ɗan iska bane, kuma yana da tarbiya ɗan uwa nane fa. yaran kuma ka riƙe in kaga zaka iya rabani dasu, shi Yah Mujahid ɗin da zan aura Allah zai Banu wasu yaran tare dashi, tunda shi ba ɗan iska bane bai gama watsar da yayansa a wurin matan baza ba bare ace bazai taɓa haihuwa ba tunda shi cikekken namijine lafiyayyene ba nakasashsheba cikekken mutum ne shi”.
Tunda ta fara mgnar ya zuba mata ido bai ko ƙeftasu, ganin haka ne ya tsananta zubar hawayenta da kuma rawan muryarta. Yayinda shi kuwa Mahmoud jikinsa ne ya ɗauki wani irin gigitaccen tsuma idanunsa sukayi jazir tamkar zasu amaryar da wuta, sai sheƙin jan da sukeyi na tsatstsafo da wasu irin tafasasshen hawaye da yaji yana ratso jijiyoyin idonsa.
Shiru tayi ta zuba mishi ido saboda jin yayi shiru kamar baya wurin, a hankali take bin shi da kallo daga sama har ƙasa saboda yadda taga ya zama kamar marar rai a jiki, rawa jikinsa keyi ne babancinsa da wanda ba rai a jikinsa.
A hankali ya lumshe manyan idanunsa sir-sir hawaye masu zafi suka fara kwarayon masa wani na korar wani saboda kalamanta biyu da suke soke kunnunwansa da dukan zuciyarsa *tunda Yah Muhajid ba ɗan iska bane bai gama rabawa yaransa matan banzaba kuma shi lafiyeyye ne ba nakasashsheba cikekken mutum neshi,* wannan furucin da yake mishi amsa kuwa a kunnensa ne ya ƙara tsananta zubar hayensa tare da jin wani irin gigitaccen zafin ciwon ƙaddararsa.
Wanda hakan yayi masifar kashe mata jiki sai kawai ta fara binsa da ido, ganin ya sunkuya a hankali ya ɗauki wayarsa da jakar system nashi tare da yan ƙananun tarƙacen dake ciki, cikin yanayin da bata taɓa ganinsa ba ya miƙe tsaye, tare da kallon ta cikin siga mafi wuyar fassarawa da ganewa ko hasasowa yanayin da idansa ya nuna yasata yin ƙasa da nata idon.
bedroom ya wuce jim kaɗan da shigansa ya fito, da idon dake zubda ƙwallan har yanzu tabishi ganin ya nufi ƙofar ya fita........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.