Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 16 of 86

Ita kuwa Fariyda jin shirune yasa ta buɗe ƙofar a hankali ta fito parlour.
Dan bata ji ma abinda Aminullah yace ba, iya maganarsa kawai ta iya jiyowa, shiyasa bata san yaji yadda sukayi da ƙanin nasa ba.

Tattare wurin tayi tare da ƙunƙuni.

Bayan kwana biyar da faruwar abin.
A hankali ya zaunar da ita gabansa cikin lumshe ido yace.
“Sannu da aiki yar aljanna, kullum kina hidimar kitchen kin hutar da Ummina da Goggo Dada, gashi Maman Samira yanzu aiki ya ragun mata, sai samiran kawai dake tayaki.
Allah yayi miki al'barka”.
Cikin jin daɗin yabawar mijinta gareta ta amsa da Amin.
Yana ɗan kallonta yace.
“Yauwa na saya miki sabbin kayan ɗaki dana kitchen da parlour kai komai ma na saya miki sabbi dan kin cancanci haka yar al'barka”.
Cikin tsananin mamaki ta zuba mishi ido a hankali tace.
“Kayan daki da kitchen kuma Yah Amin du-du auren mu wata ɗaya nefa, wasu kayan kitchen dinma ko buɗesu banyi ba”.
Cikin badda tunaninta daga zargin wani abu yace. “No kin san komai nayi miki ai kin cancanta ne. Yanzu wannan tsofaffin duk mu bawa Mamy shi kinga zata sa mana al'barka zamu samu ƙarin buɗi har kayan kitchen ɗin duk mu bata komai.
Sai a shirya miki sabbi, kinga ke komai da blue color kika zo ni kuma nafi son komai fari, shiyasa ma naji gwara mu canza din”.
Ya ƙare mgnar yana jawota jikinsa.
Ido ta lumshe a hankali ta fara tuno abinda ya faru. Kenan a kan ƙaninsa zai sauya mata kayan ɗaki, cikin hikima tace.
“No ni dai bana son ka shiga ɗawainiya ka bari kawai”.
Cikin tsaida matsayi a fuska yace.
“Ba'a maida hannun kyauta baya, ba kyau Sannan wannan umarnine ba shawara nake nemaba, gobe za'a zo a kwashi kayan.
Jibi za'a kawo sabbin bana son musu”.
Cikin sanyi da danne tsananin ƙiyayyar Mahmoud da taji yana tsiro mata cikin ƙahon zuciyarta tai masa godiya.
Washe gari aka kawo masu aiki, da kanshi ya rinƙa nuna musu komai.
Ko fork basu bariba, haka aka maida komai cikin kwalinsa aka kwasa akayi gidansu dashi.

Ita kuma Fariyda kasancewarta yarinyar mai hikima da sanyin hankali yadda ya nuna _mata_ tukuicin sabbin kayan yayi mata su bawa Mamanta wannan haka ta nunawa iyayenta.
Har kira mamanta tayi tai ta masa godiya harda kiran Ummima tayi ta mata godiya da sanya al'barka.
Kana ta samu abin alfahari a zuriyar gidan mijinta da yayan yayu da ƙannen mijinta da zuriyar suke da gasar wane yafi kuɗi, yar wacce tafi samun miji mai kuɗi da gasa a tsakaninsu.
Aiko magana ta cika a Santuraki FAMILY, duk da Mamy bata da wannan ɗabi'ar amman matan ƙannen mijinta da na yayun mijinta sun koya mata.
Washe gari kuma akazo aka shirya Fariyda komai sabo dal a ledansa ko kala irin kallar da Mahmoud keso ya zaɓa.
Ita kamta Fariyda tasha mamkin kuɗin da mijin nata ya kashe don kayan sunfi nata na farkon nesa ba kusa ba.
Da yamma cin ranar ne ya shigo tare da Mahmoud ɗin.
A nan parlour ya zauna tare cewa
“Zauna mana, muna da aikifa da yawa”.
Kai ya gyaɗa mishi kana ya zauna a ƙasa yana fuskantarsa.
Files ɗin suka rinƙa duddubawa suna aikinsu.
Ita kuwa ta gama aiki a kitchen ta fito da wormas ɗin nasu Ummi zata kai cikin gidane ta samesu zaune a lokacin Saida ta zubda ƙwalla sabida takaicin tsanar Mahmoud da yadda Yah Amin ya nuna yabi abinda ƙaninsa keso duk da bai fito ya nuna mataba, hasalima kyautata mata yayi...

Numfashi mai nauyi Amina ta sauƙe tare da kallon yaran nata da ta gama basu labarin mafarin gabar.
Sai kuma ta ɗan kalli Hafiza tace.....

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276, gareku mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 7
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

“Wannan abun shine mafarkin ƙiyayya na gasken gaske dake tsakaninsu.
Shi kuwa Yah Amin bawan Allah duk yadda zai ɓatawa wani rai baya so shi yasa yabi wannan hanyar da yayi shawara dani kuma nace dukansu biyu kar ya nuna musu yaji kuma kar yayi musu faɗa dan zai ƙara musu gaba duk wanda akayiwa faɗa akan ɗan uwansa.
Sai yanzu nake nadama da nasani da tun farkon na barshi ya buɗa musu wuta, wata ƙil da abin bai ci gaba da wanzuwa ba konciyar hankalin mu ɗaya tsananin son da Mahmoud kewa Yah Amin bai bari ya tsani yaransa ba.
Shi yasa ko su Ummi Basu san menene sanadin wannan gabar tasuba.
Su abin na damunsu matuƙa gaya, kuma gani su laifin Mahmoud ne da yake an sanshi mutum ne shi mai zuciya a wuya. Da abin bai damuna Amman ganin yadda sukayi ranan naji tsoro sosai, dan ba mmki gaba Fariyda tasa yaranta su tsani Mahmoud in haka ta faru kuwa muma dole abun zai shafe mu dan Mahmoud bashi da wasu yaya a duniya sama da yaran Yah Amin.
Kinga shi yasa nace ki ɗauki darasi a faɗan nasu.
Dan kema macece kada kije kiyiwa ƙanin mijinki irin furucin da Fariyda tayiwa Mahmoud gashi ya samar da illa da gaba mai zaman kanshi a tsakaninsu.”
Numfashi mai nauyi Hafiza ta fesar tare da cewa.
“In sha Allah zan kiyaye Mom”.
Hafiz ne yace.
“Allah dai yasa ki iya, dan kema kin ƙware a gori, ko jiya ina jinki kina waya da Huzaifa kina masa mitar ya koma school da igiyar charginki harda cewa.
“Ba Daddy bane ko Mom suka saya bare zaka tafi min dashi da kuɗina na saya”. Da sauri tace.
“To ai shi ƙaninane shiyasa”.
Mahaifinsu dake shigowa ne yace.
“Ato ai daga gida ake fara koyan gori dan haka ki bari ko mamana”.
Kai ta gyaɗa alamar to Hafiz kuwa cikin sanyin yace.
“To amman Mom meyasa kike cewa Uncle Mahmoud bazaiyi aureba”.
Da sauri suka miƙe suka fita a tare jin yadda mahaifin nasu yayi musu tsawa.
“Kai da Allah ku bar nan yara sai yawan tambaya”.
Suna fita ya maida dubansa kan Aunty Amina data lumshe idonta da suka cika da ƙwalla a hankali yace.
“Kada kiyi kuka Amina, Allah yana son Mahmoud kuma bawai ya mance dashi bane, fatanmu Allah yasa wannan jarrabawar ta zame masa al'khairi da kuma sanadin shigarsa al'janna ki tunafa ƙaddararsa mai tsarkice data tsarkakeshi.
Fatanmu Allah ya bashi aljanna ya samu hurul ien.
Inda zaiji daɗin aure fiye dana duniya”.
Cikin sanyin murya tace.
“Allah yasa haka”.
Amin yace tare da ƙara lallashinta.

Alhamdulillah kwanaki sun tafi.
Yau kwnan Mahmoud sha biyar a Egypt.
Tuni kuma kayansu na Turkiyya sun iso gida Nigeria.
Tuni an rarrabasu wa dukkan garuruwan da mall ɗinsu suke can.

Ayyah Maman Samira.
In Allah ya kai mu gobe zaki shigo ki taya Samira aiki dan zanyi baƙi”.
Cikin yanayin shaƙuwa da girmamawa Maman Samira tace.
“To Oum Zaitoon Allah ya kai mu bisa rai da lfy”.
Da Amin ta asma tare da juyowa tana kallon Samira dake cewa.
“Laa Ummi zo ku gani Zaitoon ta kamani ta tsaya”.
Da sauri Goggo Dada dake riƙe da carɓi tace.
"Eh tun jiya ta fara ai, ni watansu nawa ne yanzu?”.
Samira tace.
“Saura 6 deays su cika wata takwas cib”.
Murmushi Ummi da yanzu ta iso wurin tayi tare da cewa.
“Zata danne ɗan uwan nata kenan”.
Cikin sanyi Fariyda tace.
“Allah Ummi Zaid kamar baida isasshen lfy, musamman in anyi sanyi haka zai kwana kuka ya hanamu bacci”.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.