Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 31 of 86
Mamy ne ta kalli Goggo Abu dake cewa.
“Saura kwana nawa ne fitan takabar nata?â€.
Kai ta É—an juya ta kalli Su Salma da suka fito daga Side É—in Aunty Amarya suka nufi Side É—inta bayan sunyiwa Goggo nasu Allah ya tsare hanya Fariyda ne tayi saurin bin bayansu.
Ido ta maida kanta jin tana ƙara tambayarta.
“Ai abin yazo yau saura kwana shida ne, rana ita yau zata zauna, washe gari jumma'a ne zata fitaâ€.
Tana mai shiga Mota tace. “To sai munzoâ€.
Ranar Litinin da safe wanda ya kama saura kwana huÉ—u fitan takabar Fariyda.
Tsaye ya samu Ummi gefen Goggo Dada da take shirya masa breakfast.
A hankali yake tafiya cikin wasu tattausan wagambari sky blue mai matuƙar kyau ƙamshi mai daɗin gaske yake bazawa.
Ba tare da ya juyoba ya amsa gaisuwar Samira dake tsaye gefenshi da wormas a hannunta da alamu abincin iyayenta zata kai. Da ɗan sauri ya ƙarasa kusa da Ummi dake tsaye gefen Goggo Dada dake shirya masa breakfast akan dinnin table.
Ido ya zuba wa Ummi cikin neman ƙarin bayani jin tana faɗin.
“Fariyda ce ta kirani yanzu, tana cemin Zaitoon ba lfy, tun É—azu take ta kuka, kamar zata shiÉ—e.â€
Sai kuma ya kalli wayarta dake kan fridge dake gefenta jin yana ringing ganin Fariyda ce yasa ta amsa kiran da sauri tare da sa wayar a handsfree.
Cikin rawan murya dake bayyana tashin hankali da take ciki a raunace tace.
“Ummi Zaitoon Ummi Zaitoon É—inmu ba lfy tun É—azu take ta kuka kamar zata shiÉ—e, tafi awa É—aya tana kukaâ€.
Da kyar suke iya jin abinda take faÉ—in.
Saboda tsananin sautin kukan da Zaitoon É—in keyi har tana shiÉ—ewa.
Da sauri Mahmoud ya juya ya nufi waje.
Goggo Dada ce tayi saurin cewa.
“Ga Mahmoud yana zuwa ku kaita asbitiâ€.
Ummi kuwa a hankali ta zauna bisa kujerar dake gefenta.
Hannunta duka biyu tasa ta dafe kanta tare da rumtse idonta tana jin kukan jikar tata na mata yawo a kunne.
Motarsa na fita, motar Salim na shigowa gidan.
Da mamaki Salim ya bisa da kallo ganin yadda ya figi motar a 360.
Baba idi kuwa da addu'a ya rakasa.
Hafiz ma dake gyara labulayen shagonsa.
A fili yace.
“Unlce kuma ina zaijeâ€.
A can gidansu Fariyda kuwa.
Mamy ce ta miƙawa Fariyda Zaitoon ɗin tare da cewa.
“Bata nannan muga ko zata kamaâ€.
Da sauri ta miƙa hannunta ta karɓeta tare da kwantar da ita kan cinyarta kana ta ɗan sata cikin ɗan guntun hijabin jikinta nannu ta fidda tare dasa mata a baki.
Wani irin ciccilla yan sawunta takeyi tare da tsala ihu tamkar bakinta zai rabe biyu.
“Kai ya ilahi Fariyda kiyiwa Allah ki cire yarinyar nan cikin Hijabi haba wannan jaraba da yawa take, ke kullum zaki bawa yara nono sai kinyi ta É“oye-boye da cusasu cikin hijabi, ki barta taji da Abu É—aya mana, ga yadda take ta haÉ—a zufa fa, duk da sanyin damuna da akeyiâ€.
Da sauri ta janye É—an hijabin nata tare da kuma sunkuyowa kanta dan bata nonon.
Da sauri ta É—ago kanta ta kalli Mamy da Aunty Amarya da kukan Zaitoon É—in ya shigo da ita.
Ido cike da hawaye murya cike da rauni tace.
“Mamy taki karÉ“aâ€.
Dai-dai lokacin kuma Raihana ta shigo.
“Mahmoud yazo yana wajeâ€.
Tana amsar Zaitoon É—in ta É—aura a kafaÉ—arta tace.
“Jeki shigo dashiâ€.
Sai kuma ta kalli Aunty Amarya dake cewa.
“To ko dai cikinta ke ciwoneâ€. Tana jujjuyawa da Zaitoon É—in dake hanasu jin maganar juna da kyau sabida sautin ihunta tace.
“Ita kuwa batama da rikici. Zaid ne mai alamun rikicin ciwon ciki.â€
Sai kuma ta zauna gefen Fariyda tare da cewa.
“Kawo magungunan Zaid É—in mu bata, kafin Nasir É—in ya dawoâ€.
Shigowar Raihana dake cewa.
“Mamy gashi ya iso nan, dan Parlour Malam a rufe yakeâ€.
miƙewa tayi ta nufi parlour Aunty Amarya na biye da ita a baya.
Da sauri ya miƙe tsaye tare da miƙawa Mamy hannunsa ya amshi Zaitoon ɗin ya ɗaura kan kafaɗarsa yana mai fara jijjigata da shafa bayanta, Amman tamkar zugata akeyi da sauri ya zauna kan kujera tare da kifeta kan cinyarsa yana jijjigata ya kalli Mamy.
“Zan tafi asbiti da itaâ€.
Da sauri Aunty Amarya tace. “Ai Nasir ya kira Dr Suraj yazo ya duba ta, ya rubuta mata mgni yanzu suka fita tare da Nasir É—in ya tafi sayo maganin Dr yace kunnenta ne ke ciwoâ€.
Dai-dai lokacin kuma Salma da Zainab suka shigo parlour da sauri suka koma gefen Raihana suna tambayarta meke damun Zaitoon É—in.
Shi kuwa Mahmoud gaba É—aya ya kiÉ—ime sai ya kai mari sai ya kai gauro kana ya dawo tsakiyar parlour.
Tare da zama ya ajiyeta kan cinyarsa suna fuskantar juna ido ya zuba mata ganin yadda ta rufe kwayar idanunta da ƙarfi har jijiyoyin kanta sukayi ruɗu-ruɗu sai wani irin zufar azaba dake tsatstsafo mata tako ina ajikinta.
Ihun take yi da muryarta da zuwa yanzu tuni ta disashe.
Cikin wani irin rauni tausayi jinƙai tunowa da ɗan uwanshi ya rumtse idanunsa da ƙarfi sabida jin wani irin gigitaccen zogin zazzafan hawayen dake tsatstsafo mishi cikin jijiyoyin idonsa zuwa cikin kwayar idanun nasa.
Sai kuma ya ɗago kansa ya kalli Aunty Amarya dake riƙe da Zaid dake zamewa daga jikinta yana miƙawa Mahmoud ɗin hannun.
Da sauri ya miƙo hannunsa ɗaya ya amshi Zaid ɗin.
HaÉ—esu yayi ya rungume su a jikinsa.
Wasu irin tafasassun hawayen da bai samu ya zubda a rasuwar É—an uwan nasa bane suka fara silalo mishi wani na korar wani.
Cikin wani irin rauni Fariyda data fito daga ɗakin rike da kwalaben maganin Zaid ta zame ta zauna a ƙasa dirsham kife kanta bisa guiwowinta.
Da sauri ya kuma janye Zaitoon daga rungumar da yayi musu.
Hakan ya bawa Zaid daman da hannunsa duka biyu ya saƙalo wuyan Mahmoud ɗin kana ya zagaya ta bayansa yana murmushi.
Da sauri ya gyara riƙon da yayiwa Zaitoon ɗin ganin zata faɗi dan yadda ta wani narke a jikinsa tare dasa azabebben kuka.
Da sauri ya fara ɓalle botur ɗin rigar sanyin dake jikinta, yana hura mata iskar bakinsa tare da kallon yadda zufa ke tsiyayo mata daga cikin kanta ga fuskar da tayi jazir.
Hannunsa yasa ya zare hulan kanta.
“Innalillahi Wa innalillahi rajiunâ€.
Ya faɗa da ƙarfi tare da miƙewa tsaye ganin wani ƙaton kunama dake kan Zaitoon ɗin.
Cikin zare ido duk sukayi kansa suna haÉ—a baki wurin maimaita innalillahi.
Da sauri yasa hannunsa na dama ya kaÉ—e kunamar tare da yarfe hannunsa domin shima ta dalla mai harbi É—aya.
Ƙafarsa ta dama yasa ya take kunamar da masifan ƙarfi tare da murzawa duk da harbinsa da ta kumayi masa akan karamar yatsarsa.
Ido Fariyda ta zare tamkar zasu faɗo waje tare da sakin kuka mai sauti, ganin ƙaton kunaman da harda ƙoyaye a cikinta.
Wani irin hautsinennen kallo mai cike da tsana mai zafi tare da zafin harbin kunamar ya gyara Zaid dake maƙale da wuyanshi da yatsa ya nunata cikin murya mafi ƙololiwar tashin hankali da ɓacin rai gami da zogin dafin kunamar yace.
“Bazaki taÉ“a yin hankali ba, a rayuwarkiâ€.
Ya ƙare maganar tare da juyawa ya nufi waje da sauri.
Da sauri Aunty Amarya tace.
"Ko dai in bishi neâ€.
Cikin kuka Fariyda tace.
“Eh dan Allah Aunty muje mu bishiâ€.
Cikin sanyi Mamy tace.
“Kamar ma ya fita ai kunji Æ™aran buÉ—e gateâ€.
Da sauri duk suka nufi waje.
Amman ina kafin su isoma tuni ya bar gidan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.