Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 28 of 86
Zaune suke a parlour Aunty Amina, abincin data jera masa ya kalla cikin sanyi yace.
“Yanzu nayi lunch kafin na fito.”.
Tana maida hawayen dake ciko mata ido tace.
“Dama Ummi ta gaya min sam yanzu baka cin abinci, tace yanzu shine Abinda yafi ɗaga mata hankali, gashi duk ka rame”. Kai ya ɗan jinjina tare da cewa.
“Bazaku gane bane, baki san yadda nakeji a cikin zuciyata bane, ni nama mance ya kalar yunwa take, bana jin sha'awar komai”.
Tana share ƙwalla tace.
"Na sani Mahmoud nasan abinda kakeji ko na Ummi bai kai naka ba, amman dan Allah ka daure ka rinƙa cin abinci kada ka cutu”.
Cikin kauda mgnar yace
“Kwana biyu bakije gidaba, shiyasa nace yau weekend ɗin naki ne”.
Murmushi mai tafe da rauni tayi kana a hankali ta miƙo masa fruit yogurt ɗin data haɗa masa tare da cewa.
“Gidan ne ba daɗi Mahmoud shiyasa bana son, zuwa dan yanayin da nake samun ka dasu Ummi kullum shiru ba wani happy tare dasu”.
Lip inshi na ƙasa ya ɗan tauni gefe yace.
“To mu kuma ya zamuyi kenan, haka muke zama, shiyasa nake son in gayawa Abba ya gawa Baba Malam a yaye su Zaitoon randa yarinyar nan zata fita takaba, na tabbatar in sun dawo dai 8%10 na farin cikinmu zai dawo, zasu cire mana kewar gidan da zaman kuramen”.
Tana gyara zamanta tace.
“Yanzuma dama wurinsu zanje, dan jiya da dare muna waya da Fariyda naji Zaid yana ta kuka”.
Da sauri yace.
“Baida lfy ne?”. “Eh haka dai tace min kwana biyu yana yawan kuka, in ya tada kukan ko mamman nashi baya sha”.
Rai a ɓace yace.
“To meyasa bazata faɗaba a kaishi hospital? Na lura sam bata san zafin yaran nan ba”.
Ido ta zuba mishi tare da cewa..“Tace Dr Nasir ya kaishi likitan yara ya ganshi sunce matsalar ciwon cikine amman za'a ɗaurashi kan magani”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“Ok mu tafi”.
Tana kallon jerin abincin da ta ajiye mishi tace.
“Bakaci komai bafa”.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“Mu tafi”.
Hand bag ɗinta ta ɗauka tare da yafa mayafinta ta kalli Hafiza.
“Ki shirya masa shi a basket in mun dawo zai wuce dashi gida.”
Tana mai fara tattare su tace to.
A mota.
“Hafiz kam ya koma gida kenan?”.
Yana hawa Bisa babban titin yace.
“In yace zai taho, kuka Ummi takeyi shiyasa, kawai nayiwa Daddynsu mgna kuyi haƙuri ku bar mana shi. Tunda next month ma Huzaifa zai dawo, tunda ya gama karatu, kinga zai ɗebe muku kewar Hafiz, ko ba komai yana taya su Ummi hira, in baida lectures ko shago baya fita yana tare dasu, da dare kuma shi da Samira da Mamanta ne ka ɗan ɗebe musu kewar”.
Cikin sauƙe numfashi Amina Tace.
“Ba komai ai amman dai yake ɗan leƙomu.”
Bisa jagoranci Sadik ƙanin Fariyda suka shiga parlour Baba Malam.
Yana mai faɗaɗa fara'arsa yake musu sannu da zuwa.
A ƙasa suka zauna, cikin girmamawa Mahmoud ya gaidashi kana. Amina tace.
“Ina kwana Baba malam”.
“Lfy lau Alhamdulillah Amina ya yaranki da mai gidan”.
Tana kallon Aunty Amarya dake musu sannu da zuwa tace. “Alhamdulillah”. Sai kuma ya juyo kan Mahmoud dake cewa Sadik ya ɗauko masa su Zaid.
“Mamuda uban yara”.
Kai ya ɗan sunkuyar ba tare da yace komai ba.
Aunty Amarya da suka gama gaisawa da Amina ne tace.
“Barka da safiya Mahmoud yasu Ummi”.
Alhamdulillah ya bata amsa gajarce.
“Amina mu isa ciki ko”.
Cikin natsuwa Aminan ta miƙe tare da bin bayanta.
A parlour suka samesu.
Tana rungume da Zaid da ya ɗan fara bacci.
Sadik na gefenta riƙe da Zaitoon yace.
“Harda Zaid ɗinfa yace”.
Tana gyara wuyan ɗan ƙaramin hijabin jikinta wanda bata cika yawan rabuwa dashi ba tunda ta shiga takaban.
“Barshi kai mishi Zaitoon ɗin kawai, na samu ya fara bacci zai tada shi ya tafi ya barni da kukansa”.
Mamy dake fitowa daga kitchen ne tace,
“To tashi ki kai masa shi, tunda dai kin san ganinsu ne ke kawoshi, ke tunda baki da karar zuwa ki gaidasa ki masa godiya ko dan hidimar da yakeyiwa yaranki”.
Kanta ta sunkuyar cikin sanyi tace.
“Mamy bacci yake yi fa”.
Cikin tsareta da ido tace.
“Kin dai san bazaizo ya tafi baiga yaran nan ba, in bakya son ya tashine to tashi ki kai masa shi in ya ganshi ko a hannunki ne sai ki dawo dashi”.
A hankali ta ɗan ɗagoshi tare da miƙawa Sadik ɗin shi.
“Gashi kaisu”.
Dai-dai lokacin su Aunty Amarya suka shigo.
A hankali ta miƙe tsaye tare da rungume Amina.
Itama rungumeta tayi cikin sanyi tace.
“i miss u so much Our Aunty”.
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Wallahi nina har mafarkin su Ummi nakeyi.”
Ta ƙare maganar tana saketa.
Sai kuma ta koma ta zauna ganin Aminan tasa hannun ta amshi Zaid tana mishi kallo Mai cike da so tace.
“Bawan Allah ya jikin da sauƙi ko Fariyda”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“A Alhamdulillah yau tunda gari ya waye baiyi kukan irin na jiya ba, yanzu har bacci ma ya fara”.
A hankali ta miƙawa Sadik ɗin tare cewa.
“Gashi kaisu wurin Babansu.
Dan tunda yaji Zaid ba lfy ko ruwa bai shaba yace mu taho”.
Ta ƙare maganar tare da juyowa gefen da Mamy ke tsaye.
“Afwan Mamy hankali nane na kan su Zaid”.
Tana mai zama kan one sitter tace.
“Yo ai gwara ke, Mahmoud fa in yazo ko shigowa nan bai taɓa yiba, kawai turowa yake a kai mishi su, iya karsa parlour Malam ya gama zamansa dasu ya tafi abinsa sai duk jumma'a da sassafe zai turo Hafiz ya ɗaukesu”.
Murmushi tayi tare da gaidata.
Aunty Amarya ne ta nufi Dinnin area ɗinsu drink da bottle water ta ɗauko tare da cup bisa table ɗin dake gefen Amina ta ajiye tare dacewa.
“Bismillah”.
A can parlour Malam kuwa.
Zaitoon ce ta miƙe tsaye a gabansa tare da fara tafi tana gwaranci.
Ɗan guntun murmushin gefen baki yayi mata, ai kuwa sai kawai ta fara kerketa dariya tare da abkawa jikinsa.
Shi kuwa Zaid lamo yayi bisa kafaɗar Mahmoud ɗin dake shafa bayansa, alamun zai maida baccin.
Rungume Zaitoon ɗin yayi tare da lumshe idanunsa.
“Ka gansu fa, ƙiwya sukeyi, musamman ma Zaid ɗin, amman kai suna ganinka farin cikin suma na da banne.
Jiya da Abbanku ma yazo Zaidu ƙin amsarsa yayi kamar bai sanshi ba”. Kanshi ya ɗan juyo ya kalleshi sai kuma yayi ƙasa da kai ba tare da yace komai ba.
Sai kuma ya ɗan sake ɗago kai ya kalleshi yace.
“Malam yaushe za'a yayesu?”.
Cikin nazartar tambayar ɗan Aminin nasa yace.
“Ai da saura tunda yanzu ne ma sukayi wata goma”.
Yana mai ɗan kauda idonsa yace.
“Ranar da Yah Amin zai cika wata huɗu da kwana goma da rasuwa ranar zasu cika one year, inaga a yayesu a ranar kawai.”
Malam yace.
“Anya hakan zai yiwu kuwa ai sunyi ƙanƙanta, kuma uwar tasuma da wuya ta amince. Dan gani zatayi da ta yayesu amsarsu zakuyi”.
Kallon Malam ɗin yayi na yan seconds sai kuma yaja numfashi mai nauyi a cikin mgnar zuci yace
“Ai kuwa ko mutuwa zatayi dolen dole zan amshesu, gwara ita tana da damar samun wasu a gaba mu, kuwa su kaɗai ne garemu.”
Malam ɗin kuma ido ya zuba mishi yana mai ƙara fahimtar zaƙuwarsa da a yaye yaran ya amshesu kuma ko amininnasa ma haka yake nunawa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.