Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 62 of 86
Nigeria.
Washe gari da safe. Ummi ke waya da Amina.
“Ni fa tun jiya tamin voice ɗin banji voice ɗinba sai yanzu, shine hankalina ya tashi Amina ban san wanne halin take cikiba. Mahmoud fa baida mutunci zaije ya bar yar mutane a cikin Airport ɗin garin da bata san kowaba†. Cikin kwantar da murya Amina tai ɗanyi dariya tare da cewa.
“Ummi kifa kwantar da hankalinki yanzu mukayi waya dashi, suna tare dan najita tana kiran Zaitoon, kuma itama munyi chatting da ita da asuba, ta gaya min ai wai bacci tayi a jirgi da suka sauÆ™a yayi fice warsa ya barta tana bacci Saida aka tada ita. Kai koma fa Mahmoud bai kulataba tunda transit ne tana Æ™arÆ™ashin kulawar Ethiopia Airline, in zasu sauya musu Flight ne sai sun sauya su maidasu na Air Indian zata bar hannunsu, in kuma sune zasu Æ™ara wuce dasu nan ma lfy lau kada ki damu Ko Ummi ke dai kiyi ta addu'ar Allah ya wanzar da zaman lfy da al'khairi a tarayyar tafiyar nan tasuâ€.
Cikin gamsuwa tace.
“Allah yasa haka inayi kuma zanci gaba dayi, Allah saura kaÉ—an in gayawa Abbanku Goggo Dada tace in bari in kiraki dai tukunâ€.
Ethiopia.
Ido ta zuba mishi bayan ta zauna a kan table É—in tana cin breakfast É—in da ta É—iba.
Tanaci tana É—an bawa su Zaid duk da basu wani ci da yawa ba, dan sun sha Cerelac kafin su fito.
Shi kuwa Mahmoud kitchen É—in su ya wuce tare da kukunsu na miji wanda shima É—an Nigeria ne, duk wasu girkin Nigeria shikeyi musu.
Kusan a tare sukayi aikin yanayi yana tayshi É—auraye abubuwan da kuma faÉ—in yadda yakeso ayi masa, indomie ne akayi masa na gasken-gaske wanda yaji kifi da kwai sai pepper meat da ya juye a bowl indomei kuma a plate.
Tare suka fito dashi, akan table É—in ya ajiye masa shi kuma Mahmoud kamar koda yaushe tea ya haÉ—a cup biyu É—aya coffee ne É—aya tea.
Zama yayi tare da yin Bismillah ya fara cin indomei yana korawa da tea É—in.
Shiru tayi tana mgnar zuci dan fahimtar shi a yadda takeji ana faÉ—a a kansa.
Okay shiyasa jiya bai kuma cin komai ba, tunda dama in yaci É—aya lafiyeyye dai dai kuma gobe, iya ka dai da dare yasha fruits ko Custard ko Quaker oat.
Miƙewa tayi tare da kallon matar nan da tazo ta bayanta tana cewa.
“Oum twins barka da safiyaâ€.
Tana murmushi tace.
“Barka dai Aunty, gashi ban san sunanki bamaâ€.
Murmushi ta É—anyi tare da cewa.
“Sunana Khadijah Aliyu Garkuwaâ€.
Tana murmushi tace.
"Ayyah me sunan yaranki in kiraki dashi ko ince Aunty kwaiâ€.
Kai ta jujjuya mata tare da cewa.
"Oum Ansar ko Maman Maamah kuma in kince Auntynma ya wadatarâ€.
Ta ƙare maganar tare da miƙa mata wayarta tace.
“Samin number ki muyi zumunci in ba matsala.â€
Da sauri tasa mata number tare da cewa.
"A ba matsalaâ€.
Amsar wayar tayi tare da cewa.
"Bari inje in É—anyi bacci tunda muna da sauran lokacin kafin tafiyar dan Flight É—inmu sai huÉ—u zai tashiâ€.
Tana É—an kallon Zaitoon tace.
"Canma zamuyi isar dare kenan?â€.
Kai ta gyaÉ—a mata tare da juyawa ta tafi.
Ita ma Fariyda a hankali ta É—an juya ta koma room É—insu bayan ta É—auki key É—in a gefensa.
Tana shiga ta kwanta tana kallon time a wayarta ƙarfe goma dai-dai na safe.
Shi kuwa Mahmoud yana gama cin abincin.
Garding ya nufa dasu wanda duk free ne a garesu.
Ƙarfe biyu dai-dai ta farka.
Tayi mmkin ganin har yanzu basa É—akin.
Bathroom ta faɗa tare da yin wanka kana tayi alwala, bayan ta fito tayi azahar da la'asar ɗin duk a ƙasarun.
Mai ta É—an murza a sai kuma ta É—an murza yar farar powder a fuskarta menthol rub É—in nycil su Zaid É—in tasa a pink lips nata.
Humra ta É—an shafa a jikinta tare da goga shuwa.
A hankali ta tsaya gaba dressing mirror bayan ta gama shiryawa cikin wasu irin tattausan kimono masu masifar kyau da sulɓi zubin Turkish.
Riga da wonɗo ne Ballazo maroon color mai faɗin gaske irin mai faffaɗan roban ƙugu, sai yar rigar ciki fara ƙal mai guntun hannu wacce take da wuya, lib rigar ta kwanta a ɗan lafeffen cikinta da ya bawa tudun breast ɗinta damar bayyana, robar na har kan cibiyarta, sai yar na saman mai dogon hannun shima purple color sai ɗan ɗigo ɗigon maroon kamar dai na jikin wondon.
Wani tattausan Jersey Verls da tayi rolin kanta dashi, ta ɗan saka ɗan jersey Veil ɗin tayi tarha dashi cikin wuyan rigarta ta ɗan kwantar dashi, wasu takalma maroon color ta saka masu masakaicin sini, wani irin amintaccen ƙamshi take bazawa tamkar fure.
Ƙofar ta buɗe tare da fita dan tana ɗan son zuwa ta ɗan zaga cikin wuraren hotel ɗin.
A hankali ta kusa kanta cikin gym ɗinsu, da mamaki take kallon yadda yake sa su Zaid kan marshing ɗin gudun na yara, hannunsa ya ware tare da tare Zaid ɗin in yaga kamar zai faɗa, shi kuwa ya dage sai ɗan gudun yake yi wanda yakejin daɗin hakan, da sauri ya kama hannun Zaitoon da tazo da nufin hawa kai ya jujjuya mata tare da kashe marshing ɗin ya sauƙe Zaid dake ta dariya sama ya ɗan ɗaga Zaitoon yana faɗin.
“Banda ke maceceâ€.
Numfashi ta ɗan sauƙe tare da juyawa zata fita sai kuma ta tsaya jin yana faɗin.
"Card É—in bana gado baneâ€.
Fahimtar me yake nufi ne yasa ta ƙaraso ciki tare da miƙawa Zaid card ɗin daga nan ta fita.
Shi kuwa ciki ya nufa da yaran.
Wanka yayi musu dukansu biyu tare da jawo hand lounge É—inta ya buÉ—e kayansu ya É—auka ya sauya musu tare da kimtsasu tamkar ya sabayi.
Bobo ya kuma basu ganin kamar suna jin yunwa ba musu suka amsa, wanka ya shiga yayi tare da al'wala kafin ya fito tuni har sunyi bacci.
Salla yayi tare da shiryawa cikin riga da wonɗo leuender color sai rigar maroon color mai masifar kyaun gaske, glass yasa tare da ɗaura agogon roles ɗinsa a hannun, kimtsa kayansa yayi da kyau yana kallon time yaga ƙarfe uku kenan.
Yasan yanzu Bus É—insu zai zo dan maidasu Airport.
Ita kuwa Fariyda daga inda suka rabu bakin garding ta nufa bata daɗeba ta dawo Dinnin area ɗin anan ta sake haɗuwa da wasu kaɗan daga cikin mutanen da suke tare, Sandwich kawai ta ci sai fruits yogurt tasha. Wani kekkyawan matashin da bazai gaza su Mahmoud bane ya zauna a gefenta dai-dai lokacin da ta yunƙura zata tashi cikin tsura mata ido yace.
“Fatabarakallahu feeh ahsanil khaliÆ™in, Alhamdulillah Allah na gode maka da kayi min ni'imar ganin wannan kekkyawar halitta da kayi mana mu mazaâ€.
Da sauri ta ƙarasa miƙewa tsaye tare da juyawa ta nufi hanyar fita, dan ganin uku ta cika.
Tuna rashin mutuncin da Mahmoud ya fenta mata jiyane yasa tayi saurin
Nufar É—akin nasu, shi kuma guy É—in da sassarfa yake binta a baya.
A bakin ƙofar ta ganshi tsaye riƙe da hannun Zaid Zaitoon kuwa na kan travelling box ɗinsa, yana ƙoƙarin rufe ƙofar.
Da sauri tace.
“Kayanmuâ€. gefe ya matsa saboda yadda ta raÉ“ashi ta wuce.
Juyawa yayi ya kalli guy É—in dake cewa.
“Please my princess ko number a baniâ€.
Sai kuma yayi shiru yana kallon Mahmoud cikin nazari to ko dai matar aurece kodai mijintane. Ajiya zuciya mai sanyi ya fesar ganin Mahmoud É—in na nuna masa hanyar shiga ciki tare da masa alamun shiga manaâ€.
Murmushi yayi tare dacewa.
“ Thanks amman dai bari in tsaya in gaida big brother, duk da an min iso, gwara in Æ™ara yin Æ™asa da kai ko zan samu a bani itaâ€.
Dai-dai lokacin Fariyda ta fito rike da hand lounge É—inta.
“An mabaka itaâ€.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.