Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 86

“Afwan Abu Zaid duk da dai nasan ka gaji tunda jiya ka dawo Italy so kuma ina son next 2 to 3 weeks ka wuce Turkey dan..”
Sai kuma yayi shiru jin yace.
“Please Yah Amin ka bari sai na huta kafin ka fara min ganar zuwa wata ƙasar kuma”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Ok muje magna ta gaba. Gobe zamu shiga Al'ummah mall, akwai ɗinkunan da tololinmu suka gama zamu ɗanyi pictures and videos na Advent shi yasa ma Hafiz ya kwana a nan dan ba sai munje shagonsa ba a yin hotunan”.

Yana mai jan tsaki yace.
“Wallahi I'm so tired da wannan abun ai ta addabata da ɗauke-dauken hoto da video jaraba, for now dai ya kamata ace an samu masuyin wannan abun a rinƙa biyansu”.
Cikin zuba mishi ido Aminullah yace.
“Abu Zaid ni da nake fama da duk wasu customers ɗin da duk mutanen dake bibiyarmu a shafukan mu na social media bance na gajiba sai kai duk wani rashenmu dake ƙasarnan baki ɗaya fa ni keji da MD ɗinmu na can.”
Ya ƙare maganar yana nuna masa Samsung Galaxy dake gefensa kan iPhone 16 ɗinsa yace.
“Wlh da zaka riƙe wayar nan na wuni biyu da ka gane ina shan wuyan da yaci ka tausaya min.
Customers suna min yawa duk da Hafiz ke ji da su wani lokacin amman ina gasuwa, gashi da yawa ma wasu daga cikin matan fuskar ka suke biyowa a zatonsu da kai suke chart.
Suna ta neman haɗani faɗa da Madam”.
ÆŠan tsaki yaja tare da cewa.
“Kaita blocking ɗinsu a sauƙaƙe ka huta, kainema ke sauraronsu ai da nine da tuni nayi maganinsu, ita kuma waccar abar kamata yayi ka zama na miji a gabanta ka sanar da ita cewa kai mijin mata huɗune dan haka ta Barka ka sarara tunda kai ba ɗanta bane bare tasa maka dokar kula wasu matan”.
Ya ƙare maganar cikin faɗa da gaskiyar maganar zuciyarsa tare da miƙewa tsaye shima Al'amin miƙewa yayi dan jin kiran Sallah.

Bayan kwana biyu.
Zaune yake bisa 3 sitter yayinda itama take zaune gefenshi tana manne a kafaÉ—arsa.
Idonsu duk na kan system nashi.
Hotuna da videos É—in da aka yiwa Mahmoud wanda Hafiz yayi editing nasu ya gama gyara komai ya turowa Aminullah yanzu yasa ya fara buÉ—esu.
Yana farawa ta É—an janye jikinta tare da cewa.
Ni bari inje ciki naji kamar Zaitoon ta tashi”.
Kai gyaÉ—a mata kawai dan ya gane abinda yasa ta tashi.
Shi kuwa posting nasu yayi a dukkan wasu shafukan su, kana ya É—an dudduba shiga da fitan kuÉ—aÉ—en.

Wasu kuÉ—in ya haÉ—a tare da tura su Dubai dan saro sabbinkayansu. Sai kuma ya duba Turkish company da suka magna dasu akan sabbin kayan da suke so.
Suma kuÉ—in ya tura musu kana suka ci gaba da tattaunawa dasu kan yadda aikin zai kasance da tahowar kayansu.

Washe gari da safe.
Tura ƙofar tayi a hankali tare da kutsa kai cikin ɗakin.
Tsaye yake gaban dressing mirror yana dai-dai ta wuyan rigarsa.
Ido ya É—an zuba mata cikin kulawa ya kamo hannunta tare jawota suka zauna bakin gado.
“Ya akayi ne? Me ya ɓata miki rai haka Oum Zaitoon?”.
Cikin yanayin takaici ta rumtse idanunta suke ciko hawayen takaici cikin danne fusatar zuciyarta tace.
“Yah Amin dan Allah kuyi wa Mahmoud aure ko dan Ummi ta huta, ina son Inga Ummi ta huta zuwa yanzu yaci ace bata da aikin komai sai ibada da kula da Abba kawai amman, haka bazai taɓa samuwa ba, indai Mahmoud yana nan”.
Ido ya zuba mata baice ko ƙalaba ta kuwa san wannan shine tsarinsa mutum ne shi mai bawa mutum dama baya taɓa katse mutum in yana masa magna ko korafi sanin haka ne yasa taci gaba da cewa.
“Kai ka sani nice nace Ummi ta daina girki, madadin girki a part ɗinmu nace komai ya koma can zan rinƙa zuwa part ɗinsu inayi mana girki a can, domin taji a ranta bata rasa ya mace a kusa da itaba, ina so Ummi tajini tamkar ni ta haifa ba kai kaɗai ba, ina son Inga ta huta na kyautata mata kamar yadda take sona da kyautata min, dan nima ina son Mamy na ta samu kulawar surkanta.”
Sai kuma ta riƙo hannunsa tana kallonshi da idanunta dake bayyana gskyar abinda take faɗa a bakinta shine a zuciyarta ya sani ya gamsu Fariyda na masifar sonshi da iyayensa tanayi musu biyayyar da yasa yake jin a duniya babu abinda zai raba shi da ita.
Cikin sanyi murya yace.
“Har yanzu baki faɗa min make happening ba?”.
Cikin fidda gaskiyarta tace.
“Kana gani tun da nai sallan asuba na tafi, ba abinda ban shiryaba, wai duk dan Ummi ta huta, da sai ta shiga kitchen da kanta tayiwa yaronnan girkiba.
Amman kamar tsoronsa take wai dole sai tayi masa girki da kanta yanzu haka tana can kitchen tanayi masa wainar masa wai shi yakeso, nace ta bari nayi mishi ta zauna kawai, amman fir Ummi taƙi wai ai in huta kawai ita zatayi masa, wai tasan in yasan ni nayi bazai ciba”.
Ta ƙare maganar hawaye na tsilalowa daga idonta.
Da sauri ya rungumeta tare da cewa.
“So sorry my dear kada kiyi kuka nasan dan Ummi ne kukejin zakiyi kuka. Kada ki damu tasan haka ɗanta yake kuma bashi kaɗaiba dukanmu yaranta muna da ƙyanƙyami Amman na Mahmoud yafi namu yawa, kuma bata son yasan tana bari kinayi masa girkine zai zo ya daina cin abincin gidama gaba ɗaya ne, kuma cin abinci a waje yayi mana illar da bazamu mantaba ne shiyasa take tsoro, so kada ki damu ki haƙura nasan wata rana dole Mahmoud zai fara cin abincinki”.
Da sauri tace.
“No! Ni bana ma son yaci abincina, dama ni bana girki dashi ma, amman dan girman Allah kuyi masa aure kawai ko dan Ummi ta huta, tunda ai dai dole zaici abincin matarsa kam tunda gashi kaima kana cin nawa, dan haka kuyi mishi aure ya ƙare izzarsa da isarsa kan matarsa ya bar baiwar Allah nan ta huta”.
Cikin sanyin jiki Aminullah ya lumshe idanunsa da suka ciko da hawaye murya can ƙasa yace.
“Fariyda ai Mahmoud bazai taɓa yin aureba a rayuwarsa, sai in har shi da kansa ne yazo yace ayi masa aure, kuma hakan bazai taɓa faruwaba dan babu mata a tsarin jadawalin rayuwarsa kana babu aure a cikin ƙaddararsa”.
Da sauri ta zuba mishi idon jin yadda muryarsa ke rawa ga hawaye na silalo mishi cikin sauri tace.
“Akan me? Yah Amin taya zakace haka saboda shi ɗan idone sai abinda yake so za'ayi masa shi baza'a tilasta masaba”.
Da sauri ya fara jujjuya mata kai sai kuma kawai ya miƙe tsaye tare da shiga bathroom tare da rufe ƙofar, kanshi ya kife jikin gini yana maiyin kuka mai sanyin sautin dake cike da rauni da tausayin ƙanin nasa......

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 3
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.