Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 3 of 86

Kusan duk a tare suka miƙe tsaye, da sauri Aminullah ya runggumo Mahmoud ɗin tare da ɗan bubbuga bayanshi yana faɗin.
“Wato kai ba'a isa a hanaka ka hanu bako.
Kai da nace daga Italy ka wuce Turkey kaje ka duba aikin Carpets da blankets da muka bayar, na kuma gaya maka takalman Turkish ɗinnnan sunyi ƙasa sosai, shine kawai sai in ga ka shigo kamar faɗowar yeso”.
Fuska ya ɗan ƙwaɓe tare da janye jikinsa ya isa gaban Abban daya tsareshi da ido yana mai miƙawa Aunty Amina hannu ganin tana miƙo mishi hannun musahaba sukayi cikin sakin fuska tace.
“Autan Ummi kana abinda kake so”.
Fuska ya tsuke lokaci ɗaya ɗan annunrin nasa ya ɓace. Da sauri tace. “Afwan ɗan uwa na manta ne nace Auta ni yanzu Yah Mahmoud zan rinƙa kiranka ma.”
Ta ƙare maganar da iyakar gaskiyarta dan tasan har su Abba sun hana a gaya mishi auta fahimtar ya tsani sunan har ransa sabida baya son ƙaranta.
Murmushi Ummi tayi tana leƙa fuskarsa tace.
“To ka saki fuskar mana tunda ta baka haƙuri”.
Cikin yanayin fuskarsa da bata da yawan fara'a ya gaida iyayen nasa.
Sai kuma ya juyo tare da miƙawa Hibba hannu ya amshi Zaid yana sumbatar goshinsa yace.
“Zaitoon fa”.
Murmushi Aminulla yayi yana kallon tarin son yaran nashi cikin idon ɗan uwan nashi a fili, dan son yaran baya ɓuya cikin idonsa yana murmushi yace.
“Hmmm ka santa ai ita dai bacci bacci”.
Ya ƙare maganar yana kallon Fariyda dake shirya wormas a dinnin table duk abinda ake tana parlour tana ji.
Tsaki ta ɗan ja ƙasan ranta cike da takaicin yadda suke wani riritashi yaro sai faɗin rai da girman kai da isa ta faɗi a ranta cikin jin tsanarsa.
Da ido Aminullah yake nuna mata ƙanin nasa da alamun tai mishi magna mana.
Tsuƙe fuska tayi tare da ficewa daga parlour.
Cikin hikima yabi bayanta.
Aunty Amina kuwa ɗiyarta Hafiza ta kalla tare da cewa.
“Kawowa Uncle ruwa mana da fruits”.
Da sauri Ummi tace.
“Hmmm kin sanshi ai bazaici komai ba sai yayi wanka”.
Cikin kulawa Abba yace.
“Je kayi wanka kazo kaci abinci ko”.
Kai ya ɗan gyaɗa kana ya ɗan harari gefen dinnin table ɗin, yana miƙewa tsaye.
Yana rungume da Zaid ya buɗe ƙofar parlour ya haura upstairs ɗin da zai kaishi sama side ɗinsa kenan.

Fariyda kuwa kai tsaye part ɗin su ta nufa.
Tana shiga Aminullah na sa kai da sauri ta jawo ƙofar baya tana mishi murmushin dake nuna gaskiyar tsananin soyayyar da take mishi na cikin jini da zuciyarta.
Jawota yayi gareshi ya manna bayanta da ƙirjinsa cikin yin ƙasa da murya yace.
“Me yasa bakiyiwa Mahmoud magna ba”.
Tana tsuƙe fuska tace.
“Dani dashi waye babba”.
Cikin sauri yace.
“Shi mana”.
Tana kallon cikin idonsa tace.
“Nifa ka dena cewa yaron nan ya girmeni shiyasa yake ƙara jin kansa, yana wani buɗa min ido kamar wani ubana, ai koma menene ni matar yayansa ne kamata yayi ya girmamani yaron da a kalla ka bashi 10 years”.
Ta ƙare maganar cikin tsanar Mahmoud ɗin har ranta.
Yana ɗan ƙwaɓe fuska yace.
“My love koma dai menene Mahmoud fa ba abinda yake Miki, kin kuma san shine ya dawo daga tafiya wata biyu kenan baya nan ai ke ya kamata ki masa sanu da dawowa ko dan ganin ma hidimar aikin da miji ki ya ɗora masa ne”.
Cikin fesar da numfashi takaici tace.
“Ka dai duba lamarin nan da kyau yaron nanfa ba shike binkaba, kai bafa shi ke bin Aunty Amina bama da take binka, shi ƙaninka nefa na biyu, ko ita Maman Hifiza da take binka ma bata wannan faɗin ran sai shi, Aunty fa take cemin baki cike tunda tasan ni matar yayanta ne”.
Yana kallon ta yace.
“Wlh baki fahimci waye Mahmoud ba in kin gane shi fa mutum ne shi mai sauƙin kai kawai dai baya son rani ne, da kike cewa na bashi 10 years waya gaya miki ni fa yanzu 36 nake da, Amina 32 shi da kika raina ɗin 29 yake dashi fa, ke ɗin kuma dudu 21 years gareki sharu 7 zuwa 8 fa Mahmoud ya fiki dasu, ko ni ɗin ban bashi 8 years ba 7 ne na fishi dashi”.
Tana ɗan janye jikinta cikin ƙara jin tsanar yadda yake kare ɗan uwan nasa, tana mai danne tsanar Mahmoud dan kar mijin nata ya gane tace.
“Lokacin salla yayi”.
Ta ƙare maganar tana barin wurin Allah ya sani ta tsani taji yana yaban halin Mahmoud yaronda gaba ɗaya girman kai da isa ya hana shi murmushi ma a rayuwarsa bare dariya.
“Yau shekarana biyu cib a gidan amman ban taɓa ganin inda yayi murmushiba”.
Tayi magnar a fili lokacin da ta shiga bedroom ɗinta.
Shi kuwa Aminullah kai kawai ya jinjina ya shiga bathroom ɗin parlour yayi alwala ganin magrib tayi.

Zaune suke a dinnin table ɗin.
Aunty Amina, Hifiza da Hafiz tagwayen Aunty Amina wanda suka shigo da Aminullah
Sai Mahmoud ɗin dake zaune a can parlour yasa Zaid da Zaitoon a gaba yaran da bazasu wuce wata 5 ba lumshe idansa yayi tare da buɗewa yana kallon Zaitoon dake ɓangale masa baki tana dariyar yara harda sauti hannunshi ya ɗaura a kanta tare da shafawa yana jin son yaran a ransa.
Wani kallon takaici ƙasa-ƙasa Fariyda ta danna mishi tana mganar zuci.
“Ganin yadda yaran keta kallonshi suna dariya da rarumoshi Amman shi sai wani shafa kansu yake ko suma ɗin bazai iya musu murmushi ba kenan bare dariya, a haka za'a addabeni da kalmar wai ai yana son yarana ya wani tsaresu kamar mugun boss.

“Mahmoud bismillahi kai muke jira”.
Muryar mijinta ya katseta daga mgnar zuci da take yi.
Shi kuwa Mahmoud kai ya ɗan ɗago ya kellesu sai kuma ya ƙara tsuƙe fuska ganin Fariyda ma ta ɗan kalli ta inda yake.
“No I'm okay kuci kawai”.
Da sauri Aunty Amina tace.
“To me kaci tunda ka dawo fa, ko ruwa baka sha ba”.
Yana kallon Zaid dake ƙoƙarin ture Zaitoon yace.
“Ai kin san ba ko wanne jogwalgwalen girki nake ciba”.
Yess tabbas ta sanshi da ƙyanƙyami da zaɓen abinci Amman batayi tunanin har yanzu baya cin girkin Fariyda ba.
Shi kuwa Aminullah Fariyda da ke cillawa Mahmoud ɗin wani irin kallon mai cike da tsana da jin haushi ya zubawa ido, hannunta dake gefenshi ya ɗan shafa yana mai kai abincin bakinsa yace.
“Boɗɗi kinci kyautar sabuwar waya dan girkin nan yayi”.
Murmushi gefen baki tayi tare da ƙara hararar side ɗin da Mahmoud ɗin yake dai-dai lokacin kuma Ummi ta iso gaban Mahmoud ɗin Samira na biye da ita a baya riƙe da tray a gabanshi ta ajiye ta juya ta bar wurin ta koma kan Dinnin table ɗin gefen Fariyda ta zauna tana kallon Aminullah dake tambayarta yaushe ta dawo, ina Goggo Dada.
“An shiga sallan magrib na iso, Goggo Dada tace sai gobe zata dawo”.
“Sai kuma kikaƙi ki jiranta?”.
Cewar Amina da sauri Samira tace.
“Our Aunty ni zan fara shirin zuwa garinmu ne shiyasa jibi zan je, na santa kuma gobenma zatace sai da yamma”.
Kai ta jinjina cikin gamsuwa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.