Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 27 of 86
A can gida zaune gaban Abba yake yayi ƙasa da kansa.
Da sauri ya ɗago kansa ya kalli Mahmafin nasa jin yana faɗin.
“...
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276, mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050 zakuyiwa magna.
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 10
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
“In sha Allah gobe Monday zaka fara zuwa office ɗin ɗan uwanka Aminullah.
Zaka koma mazauninsa
Kayi dukkan aikin da yake yi, idan buƙatar fita waje ya kama sai a wakilta Salim yaje, in Kuma buƙatar tana da yawa, kai zakaje ni da kaina sai in wakilci office ɗin naka kafin ka dawo, duk da naso in huta in bar komai a hannunku amman Allah baiso hakanba, dole time to time zan rinƙa zuwa”.
Kanshi ya maida ya sunkuyar yana mai jin zuciyarsa na suya ganin raunin mahafin nasa cikin sanyi yace.
“Abba me zai hana asa Yah Ahmad a gurɓin Yah Amin, in ya so ni inci gaba da riƙe aikina”.
Cikin murya mai sauƙi yace.
“A'a Mahmoud nafa sanka da gardama. A nan kuma bana son gardama, shi Ahmad zai koma Adamawa ne ya riƙe aikin Salim, shi kuwa Salim zai dawo nan ya riƙe naka aikin, kai kuma zaka riƙe aikin Aminullah.
Dan kafi kowa sanin komai na shi'o'imu koni ka fini saninsu tunda ɗan uwanka na yawan yi maka bayani”.
Kai ya ɗan rusunar cikin gamsuwa da haka kana a hankali yace.
“Ko ranar da zai rasu, muna dawowa masallaci sallan asuba ina shiga dakina ba dadewa ya shigo riƙe da files masu yawa.
Muna zama yace min.
“Tashi in lissafa maka waɗanda muke bi bashi.
Nace masa ya bari sai da rana.
Sai cemin yayi ai lokacin baya nan, dole na tashi ya rinƙa buɗa min Files ɗin da duk muke bin wasu bashi.
Saidai ya buɗa min Files sun kai 17, Sai kuma yace min.
“Ba wanda ke binmu bashi duk jiya na gama biyan kowa, ya kuma ƙara min da cewa.
“Daga wata mai kamwa zamu ƙara ɗan rage farashin mu, yadda bazai ɓatawa abokan kasuwancinmu raiba kuma mu farantawa customers ɗinmu.
Na gama fidda bashi da komai.
Ga kuma wannan File ɗin na jerin lissafin dukkan mallakinmu ne.
Na rage maka wahalar lissafin cire Zakka saura wata uku a cire kaga shiga da fitar watanni ukun kawai zaka yi.”
Ya ƙare maganar cikin turowa Abba himilin Files ɗin.
Cikin sanyi Abba yace.
“Nima yamin bayanin”.
Ummi dake gefene tayi shiru Tamkar bata wurin sai hawayen dake tsilalo mata.
“Allah Ubangijin talikai yayi maka al'barka, Allah ya baka sa'a yasa ka shiga office din lfy ka fara aiki cikin lfy da nasara Allah ya kare mana kai”.
A tare suka amsa da Amin Amin.
Tsaye yake cikin cikin wasu datatstsun suit maroon color mai masifar kyau.
Yayinda long sleeve shirt ɗin cike ta kasance fara.
Sai takalma cover shoe black masu masifar sheƙi.
Sai wani irin ƙamshi mai daɗin gaske da yake bazawa.
Ido suka zaba kishi baki ɗayansu.
Kyau dai iya kyau yayi, sai ramar dake tare dashi da tsananin rashin walwala dake lulluɓe da fuskarsa dama ba wata fara'a bace garesa ga kuma rasuwar Aminullah da ya ƙara maidashi mutum mai tsukekkiyar fuska wanda hakan kuma bai dakushe kyansa ba.
Da Amin yake amsa addu'ar da suke jera masa kana ya juya ya fita.
Hafiz dake riƙe masa da broefcase ɗinsa.
A hankali yayi Reverce ya bar gidan.
Fuskar nan a tsuke yake amsa gaisuwar ma'aikatan nasu.
Duk da bawai ya tsuketa da nufi bane, shi baima san a tsuken take ba.
Yana isa Reception ɗin ya samu Salim.
Da mamaki yake kallonsa.
Sai kuma ya amsa gaisuwar ma'aikatan nasu kana suka wuce office nashi bisa jagoran PA din Yah Amin.
Office ɗin babbane irin na musamman ɗin nan.
Ne a hankali ya lumshe idanunsa dan ƙamshin Yah Amin ɗin da yaji ya daki hancinsa Sai kuma ya buɗesu a hankali dan gizo da idonsa ke masa.
A hankali suka ƙarasa ciki inda a farko yake shirye da manyan kujeru na alfarma set guda sai gefen dama kaɗan inda fridge da show glass ke tsaye.
Daga hagu kuma Babban table ɗin Office ɗin ne mai ɗauke da kujeru biyu ta gaba.
Sai ɗaya a can baya wanda yake ma zaunin Yah Amin din ne.
Sai himilin Files da Documents masu yawa, sai computer dake kai.
Daga sama kuwa Ac ne dake feso sanyi mai shiga rai.
Sai ƙaramin fridge dake gefe cib da cib.
Sai kuma ƙofar toilet ɗin.
Zagaywa yayi ya zauna bayan yayi addu'a kana PA ya zauna kujerar dake fuskantar wacce Salim ke Kai.
Daga nan ya ɗan yi masa bayanin iya abinda ya sani.
Sai kuma ya kalli Salim tare da cewa.
“Muje in kaika Office naka”.
Yana ɗan hararansa yace.
“Waye bai san office ɗin Mahmoud ba, ai ko dan yawan zamansa kullum a rufe kowa zai sanshi ni matsalata kar in zama irin sa ko irin Sulaiman dan in ba aiki ai ba daɗi”.
Kai Mahmoud ya ɗan jujjuya tare da cewa.
“Zaka san baka da wayo in ka fara aiki.
Wallahi gwara maka Adamawa.”
Sai kuma ya kalli PA tare da cewa.
“Bama can za'a kaishi bafa, office ɗin Yah Ahmad za'a kaisa dan aiki biyune nasa, aikin Yah Ahmad da kuma aikin fita duk ƙasar da muke buƙatar kayansu”.
Da sauri yace
“Kasheni zakayi da aikine?”.
Ba tare da ya kallesa ba yace.
“Da kace kai jan wuyane ai, Please kuje inada aiki”.
Daga nan ya fara duba File ɗin farko, ganin hakane yasa suma suka fita.
Bayan kwana takwas
da yamma a hankali ya zame daga kan kujerar da yake ya kwanta tare da lumshe idanunsa murya a sanyaye yace.
“Allah ya jiƙan Yan Amin yasa ya huta, Allah ya bashi ladan aiyukan wahala da ya rinƙayi”.
Goggo Dada dake ajiye masa plate ɗin fruits ne ta amsa Amin ya Allah.
Sai kuma ya miƙe zaune tare da cewa.
“Tunda na fara zuwa in banda salla bana samun hutun da ya kai 5 minute ba”.
Cikin kulawa Ummi tace.
“Sabida aikin ya tarune ai shi yasa, da ka gama dai-dai ta komai zaka samu sakuni.”.
Fork ya soka a jikin Apple kana ya kai bakinsa yana mai gyaɗa mata kai alamar eh.
Jidda ce zaune gefen Mama cikin zafin so da yasa kunya barin idonta tace.
“Mama dan girman Allah ki gayawa Baba ina son Yah Mahmoud tsakani da Allah nake sonsa fa”.
Salim dake shigowa ne yace.
“Kai wannan yarinya akwaiki da jarabar nacin tsiya, wlh ke in mayyace in kin kama mutum sai buzunsa, wato ala tilas dai sai kin famawa iyayenmu tabon ciwon ƙaddarar Mahmoud ko, ina gaya miki ki fita harkar Mahmoud ke ko kunya bakya ji, ga Sulaiman na sonki ke kuma kina batun Mahmoud wlh kika bari yaji hmmmm!”.
Sai kuma ya zauna yana watsa mata kallon gargaɗi,
Mama ce tace.
“Ni wlh har hawa kaina mgnarta yakeyi akan batun Mahmoud”
Cikin sanyin murya tace.
“Nifa Yah Sulaiman bai taɓa cewa yana sonaba, kawai dai muna mutunci yana kirana mu gaisa”.
Fuska a haɗe Salim yace.
“Banza ke sai ya buɗi baki yace miki yana sonki ne, zaki gane tunda kan kifi gareki”.
Tana maraimarace fuska tace. “Dan Allah Yah Salim ka faɗawa Yah Mahmoud wallahi ina sonshi zan iya zama dashi a ko wanne yanayi. Yah Sulaiman ma kuwa a barshi kawai dan wlh ni dai bana sonsa”.
Tsaki yaja tare da miƙewa ya kwanta tare da zaro wayarsa yana faɗin.
“Baki da hankali da ace Mahmoud zai yi aure da daga rasuwar Yah Amin zuwa yanzu da tuni an masa aure ko dan Ummi ta samu madadin Fariyda”.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.