Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 82 of 86

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 42
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

"To Babe sai me dan kinyi aure, ina sonki ina ƙaunarki da aure, gashi da riba zan sameki Babe za'a yarda a bamu su”. A hankali ta ɗan ɗago flowers ɗin daya kawo mata shaƙar ƙamshinsa tayi tare da kallonsa cikin gamsuwa da gskyar kalamnsa cikin son kare kanta dashi daga fushin Allah tace.
"Ina da aure ai”. Da sauri ya zaro idonsa tare da kauda kai yana mai yin istigfari sai kuma yace.
"Fariyda nasan ba ƙarya kikeyi min ba, to meyasa Mahmoud ya barni nazo ina mijinki, meyasa zaki saurareni”. Tana sauƙe numfashi tace.
“Ai shine mijin nawa, da yayansa ya rasu ranar da na fita ta kaba ranar iyayenmu suka ɗaura mana aure”. Cikin kaɗuwa ya kwantar da su Zaitoon da sukayi bacci a jikinsa tare da maida hankalinsa kanta yana mai kauda idonsa daga kallonta.
Gyara zaman tayi tare da fara bashi haƙiƙanin lbrin zamanta da Mahmoud da rashin shirinsu da gabarsu da halin nagartar iyayensa da haƙurin Yah Amin da yadda akayi musu aure ba shawararsu da tashin hankali da har ya kaita ga suma da yadda Mahmoud ya targaɗata da dai duk irin zaman faɗa da gaba da tsana da sukeyi da sanadin zuwansu, da tsarinsu nayin auren a sirri dan gudun kada iyayensu su hana. Numfashi mai nauyi ya sauƙe saboda jin kiran Sallah magrib yace.
"Naji sanyi kuma na gamsu, abu ɗaya ya ɗaga min hankali Yah Mujahid Babe Wlh ina sonki zan aureki, zan riƙe su Zaid dan girman Allah ki mance Yah Mujahid ki tausaya min kada zuciyata ta fashe”. A hankali tace. “Kaje kayi salla”. Kai ya gyaɗa mata tare da cewa. “Sai na dawo mu ƙarasa mgnar”. Daga haka ya fita. Koda aka idar da sallan magrib, Mom ɗinsa ya kira, duk jawabin da Fariyda tayi masa bai ɓoye mata komai da, dan shi itace ƙawarsa numfashi ya fesar tare da hamdala jin Mom na faɗin. "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ma da bazawara ya fara, nima da babanka ya rasu saurayi na aura, kuma shi ya riƙeka Tamkar uba ya hanaka maraici, don haka ina farin ciki da Fariyda da gaskyarta, ka turo min number ta zanyi magna da ita, ta tausaya min ta mance Mujahid. Abu ɗaya shine Mahmoud ya saketa kawai ai bata da idarsa ko? Kuma dole ka janye kanka har sai ya saketa”. Cikin farin ciki yace. "Yess my happiness bata da idarsa shinefa ke dagewa ta yarda dani”. Kiran sallan isha ne yasa su katse wayar.
Koda aka idar da sallan addu'a yayi tayi akan samun cikar burinsa na mallakarta.

Fuska ya taɓe tare da kallon ta a fakaice yadda ta tasa flowers ɗin a gaba kan sallayan. “Ina yake”. Ya tambaya kamar ba daga bakinshi mgnar ta fitoba.
Tana sunsunar ƙamshi flowers ɗin Tace “Yana masallaci”. Kai ya jinjina ya isa gaban gadon inda Zaid da Zaitoon keta sharara baccinsu cikin salama da aminci.
Lumshe idanunsa dake cike da gajiya da bacci kwanaki da ya ƙara sauyasu suka koma tamkar na ɗan maye zama yayi kan kujerar yana magnar zuci yauma ba bacci kenan tunda sunyi baccin yamma.

Yana jin ana Knocking bai kulaba bare ya tashi haka ne yasa ta miƙe ta buɗe ƙofar. “Kinyi mana addu'a ko”. Sa'ad ya faɗa cikin sigar kulawa, hango Mahmoud ne yasa yayi saurin shigowa hannu ya basa tare da mishi sallama hankalinsa na kan yaran ya amsa, sai kuma ya ɗan kalleshi yace. "Baka gajiba kenan 9:00 pm fa, ai gwara kaje kayi bacci ka huta”. Cikin farin ciki yace. "Da so nake mu gama magnar da kai da ita”. Kai ya jujjuya kana yace. "No kada ka damu sai gobe zamu yi magna, ita kuma zaku iya fita kuyi magna dan kada a hana su Zaid bacci”. Cikin gamsuwa da mgnar tasa yace.
“Ngd Big broz sai da safe”. Sai kuma ya kalli Fariyda yace. “Ƙanwata ba rakiya ne?”. Miƙewa tsaye tayi tare da bin bayansa suka fita.

Cike da kunya take kallon Mom Sa'ad ɗin, a video call da Sa'ad ɗin ya haɗasu. “Mom ya kika ganta?”. Murmushin mai cike da jin dadi tayi tace.
"Masha Allah, naga ɗiyata kam Fatabara kallahu feeh ahsanil khaliƙin.” cikin jin daɗi yace. “Mom ya kamar tun yanzu ta fini fada ne”. Da sauri tace.
“Ai kai kam yanzu na yayeka yanzu ta ɗiyata yar Albarka nakeyi, Fariyda Allah yayi muku al'barka”. Murmushin Fariyda ta ɗanyi cike da kunya tace. “Amin ya Allah”. Kai ya ɗan rausayar kana yace. “Mom sai anjima zamuyi magna”. Tana kallon Fariyda tace.
“To sai da safe ko my Daughter”. Tana matsawa daga jikin Sa'ad ɗin tace. “Allah ya bamu alkhairi”. Juyowa yayi ya ɗan kalleta bayan ya katse kiran. Lumsassun idanta ta ɗan juya kana a hankali tace. "Sai da safe”. Cikin kulawa yace.
“Ba don naga bacci ya cika waɗannan kyawawan idanunba da sai ince mu kwana a haka, amman ba matsala gobe 6:30 zan shigo dan 9:00 AM flight ɗinmu zai tashi”. Shiru tayi tana mai ƙara gyara mayafinta da kauda kanta daga ganinsa. Numfashi ya sauƙe tare da ɗan kallonta yaci ga da cewa.
“Ba dan gobe Monday bane kuma ina da ayyuka da yawa a officer da zan ƙara kwana”. Kai ta gyaɗa tace.
"Allah ya kiyaye hanya”. Yana murmushi yace Amin ya ɗaga mata hannu kana ya tafi masauƙinsa.
Daga nan Dannin area kitchen É—in hospital É—in ta wuce, É—an Custard kaÉ—ai tasha kamar jiya ta amso nasu Zaid.
Kan 3 seatter da ya zama tamkar gadonta, ta kwanta bayan ta ajiye ɗan tray ɗin Custard Zaid ɗin da yake cikin ɗan flacks, sabida ganin sunyi bacci shi kuwa Mahmoud, wayarsa ce a hannunsa, flowers ɗin da ta ɗauka kafin ta kwanta ta rungume tana shaƙar ƙamshinsu.
Miƙa ya ɗanyi saboda gajiya da zama da rayuwar kujerar dare da rana in dai yana asbitin to yana gaban gadon, 11:59 pm, wani irin tsumemmen bacci na gasken gaske yakeji na tsawon kwana uku yanzu daren na huɗu bayayi sai da asuba in ya koma gida yayi na 1 to 2 hours sai kuma gobe uwar hakan, ganin Zaitoon ta buɗe ido ne yasashi jawota bakin gadon tare da ɗan shafa kanta a hankali, numfashi ya ɗan sauƙe ganin ita murmushi ma take masa, ganin ta fara mutsu-mutsun ne yasa ya ɗagata dan kada ta tada Zaid. Haka dai a ranar ma ya kwana zaune.
Washe gari da asuba yana fita masallaci ma sauƙinsu ya wuce kamar kullum.
Ita kuwa Fariyda bayan ta idar da salla Custard ɗin da basu sha da darenba ta basu, sannan tayi musu wanka ta shiryasu da kayan da ta ɗauko musu jiya. Ganin suna ta wasa da abu uwan wasan dake kan gadon yasa itama ta shiga tayi wankan ta, kimtsa cikin tattausar jallabiyar mata mai taushi yar cib da jikinta sai ɗan ƙaramin hijjab ta zura a kai wanda iya karsa bisa kafaɗunta.
Tana gamawa Nurses na shigowa, kusan 26 minute sukayi sannan suka fita bayan sun gama musu komai, 7:00 taji ana Knocking, a hankali ta kwantar da Zaid da shima yayi bacci, dan ita Zaitoon tun ɗazu ta meda baccin. Gyara musu kwanciyar tayi, sannan tayi bakin ƙofar.
Cikin mamkin ganinsa da wata flower ƙwaya ɗaya mai ɗan yelwan ganye sai wani irin ƙamshi yake bazawa, mutum dake bayansa riƙe da wasu gift kusan guda uku kwalin ƙasa yafi na tsakiya, na tsakiyar kuma yafi na saman, hanya ta ɗan bashi tare da cewa.
“Barka da zuwa”.
Yana zama bisa kujerar gaban gadon tare da kallon mutumin dake bayan nasa yace.
“Barka dai ɗiyar Mom”. A hankali ta zauna kan kujera tana kallon kwalayen da tuni wanda ya ajiyesun ya fita, bayan Sa'ad ɗin yace ya jirasa.
Numfashi mai sanyi ta shaƙa a karo na barkatai sabida sanyin ƙamshin da flower nan keyi da kwalayen kasu.
“Ya Zaid da jiki?”. Tana kallon ledan hannunsa mai ɗan girma da ya aji a gabanta ta ƙara gyara rufe jikinta fuska ba walwala tace.
“Alhamdulillah da sauƙi sosai, ina gama yau kam za'a sallamemu”. Da sauri yace. “Amman ai ba yanzu zaku koma Nigeria bako?”. Tana amsar ledan tace. "To ban sani ba dai kam”. Time ya ɗan kalla tare da cewa. “Na bata lokaci a srrat mall, dan sayawa flower ta turare, gashi time ɗin tashinmu ya kusa.”
Cike da tsoron fushin Allah tayi ƙasa da kanta
time É—in ta duba a wayarta 8:30 saura awa É—aya kenan tashinsu kai ta kauda ba tare da tace mai komaiba.
"Yah Mahmoud fa, ina son mu gama magna ne fa kan in tafi”. Tana ɗan ƙara jan hijabin jikinta tana rufe dogon gashinta tace. "Bai isoba ..”. sai kuma tayi shiru saboda ganin shigowarsa, da ita da Sa'ad ɗin duk a tare suka ja numfashi mai sanyi Saboda ni'imtaccen ƙamshin turarensa daya danne duk ƙamshin da yake cikin ɗakin.
Gaban gadon yazo ya tsaya gab da jikin kujerar da Sa'ad É—in yake, hannunsa yasa ya fara shafa kan Zaid. Ba tare da ya kallesu ba ya amsa gaisuwar Sa'ad daya tashi daga kan kujerar.
tissue É—in dake gefe ya zaro yasa ya goge kujerar sannan ya zauna ya É—aura kafa É—aya bisa É—aya.
Ido Fariyda ta zuba mishi cikin nazarin da yasa idonta cika da ƙwalla mai zafi wanda ke haɗe da rauni.
Dam'n ta lura ƙiyayya ta kai ƙiyayyar da zai turata wata da kafarta, ya zatayi to ya saketa mana kafin ya sata sauraron wani, So take ta riƙeshi saki to amman furucin Mamynta na bata yafe ta nemi sakiba da Allah ya isa da zata ɗora Mata shi ya hanata cewa ya saketa ya sauƙe mata nauyin igiyarsa dake kanta,
Da ace ya furta mata kalmar saki da nan zai sha mmkin to amman ya zatayi da furucin mahaifiyarta ga kuma gudun saɓawa Allah. Maganar da Sa'ad keyi ne ya katse mata tunanin zuci.
“Yah Mahmoud dama kai nake jira, kasan yau zan juya.” ba tare da ya kallesu ba yace.
“Kada ka damu kaje kawai zamuyi magna a waya, kada kayi missing flight”. Cikin ɗan ƙaguwa yace. “To amman yaushe zaku koma?”. A daƙile yace. “Wannan bai shafe ka ba, in kuna mgna in taga dama zata gaya ma in lokacin yayi”. Yana ɗan kallonta yace.
"Yah Mahmoud a bani number ta”. A gajiye yace. Allah ya tsare hanya. Amin yace tare da kallon Fariyda yace.
"To zan tafi sai munyi mgna”. Allah kiyaye hanya tayi masa, sai kuma ta ɗan miƙe saboda cewa da yayi ba rakiya ne, a ƙalla 11 minutes tayi da fita kafin ta dawo bayan ta ƙara jaddada mishi tana fa da aure a kanta.
A yammacin ranar suka koma masauƙinsu da sharaɗin bayan kwana uku zasu dawo a ƙara dubashi ranar da ya cika sati dayin aikin kenan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.