Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 30 of 86

Yana zama kan kujerar ya juyo tare da kallon Fariyda dake cewa.
“Uncle Salim sanda zuwa”.
Tana musu karan kiransu Uncle ne dan yaranta subi bakinta....

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shadar biyanki ta nan 09097853276 mutanen Niger ku kuma 1000cfa zaku biya ta wurin Hannatou +22790440050*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 11
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set ɗin kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set ɗin hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
Haɗine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.

Idan kin sayi kaya in dai set ɗin kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuɗin Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.
0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

Kai ya jinjina mata tare da miƙa mata hannu ya amshi Zaitoon.
Bayan sun gaisane yace.
“Zaid fa, Mahmoud yace min baida lfy”.
Cikin sauri tace.
“Yana bacci ne, Alhamdulillah jikin fa yayi sauƙi”.
Mamy ce ta fito suka gaisa jin yana tambayarta.
Bayan sun gaisane yace.
“Allah ya ƙara sauƙi ga wannan a saya musu bobo”.
Cikin sanyi Mamy tace.
“Harda shiga ɗawainiya an gode”.
Ita kuwa Fariyda kasa tayi da kanta alamun hawaye take zubdawa ganin haka ne yasa yayi saurin fita.

Bayan mako biyu.
Abba ne zaune dashi da Bapp Lawan,
Bisa alamu maganace mai girma wace ta girgiza Bappa Lawan ɗin Abba yayi masa domin yanayin yadda yayi sujudu shukur zai nuna maka tsananin farin cikinsa.
Sai kuma ya ɗago daga sujjadar tare ƙara godewa Allah.

Zaune suke cikin babban parlour gidan, shugaban tawagar tasu.
Muhajid ne har yau a kiɗime yake ya kalli Uban zugar nasu dake cewa.
“Kai duniya abar tsoroce, rayuwa bata da tabbas, har yau in na tuna Aminullah ya ratsu sai inji kaina na sarawa, lokaci ɗaya jinina ke hawa.
Allah ya nuna mana ƙarfin ikonsa, mu muna nan munata muhawara da zaman meeting muna tsara yadda zamuyi mu kashesa, shi da ƙaninsa sai gashi Allah ya ɗauki abinsa a lokacin da mu kanmu bamu zataba”.
Wanda ke gefensa ne ya fesar da numfashi mai tafe da tsoron Allah da imani yace.
“Dama ita mutuwa ayace mabayyaniya, mu dai Allah ya nuna mana ishara, gashi da bamuyi gaggawa bama Allah ya ɗaukesa, kuma muma bamufi ƙarfin hakaba”.
Wanda ke kallonsa ne yace.
“Ba shakka Allah yana sonmu da rahama da kuma shirya, ya nuna mana kada muyi gaggawa Aminullah dai zai mutu, ya kuma mutun, kuma gawarsa bazata cika ƙasa ba, bare mu mu tabbata. Allah ya somu ya tsaremu da ratayar jinin bawansa mumini Aminullah”.
Wanda tunda suka fara mgna baice komai bane, yace.
“Ni har yau in na tuna yadda lbrin mutuwar Aminullah ta riskemu, muna zaune muna tsara yadda Muhajid zai bawa ƙanwarsa gubar nan a samu yaci ya mutu, sai inga tamkar ban tsiraba.
Yah Allah mun tuba kayi mana gafara da mugun nufin da mukayi.
Allah ya jiƙan Aminullah halinsa na gari ya bisa”.
Kusan duk a tare suka amsa Sai kuma suka kalli wanda ke yawan cewa Mahmoud na burge shi.
Hawayen dake zubo mishi ya sharce tare da cewa.
“Yaron nan Mahmoud yana bani tausayi in na tuna yanayin da muka sameshi ranar da muka je musu gaisuwa, tabbas rashin ɗan uwa yana da zafi wanda ya sanshi ne kaɗai zai gane, yaro duk ya zama tamkar zautacce ba mgna sai ido, gashi ya kasa samun yayi kuka.
Allah ya sani ina son Mahmoud har cikin raina.”
Sai kuma duk suka sauke numfashi mai sanyi cike da nadamar mugun nufin da sukayi da kuma godiyar Allah da ya hanasu damar samun kashe Aminullah har ajalinsa na min'indinllah ya ridkesa.
Sai kuma duk suka kalli Muhajid da ya saki dariya cikin sanyi yace.
“Tabbas bamu kashe Aminullah ba, amman ni farin ciki mai tarin yawa nayi da mutuwarsa, dan dama ni ba a iya kasuwnci ya tsaya min a wuyaba.
Ku kun sani matar tasa ƙanwace gareni. Mahaifinta da mahaifiyata uwa ɗaya uba ɗaya suke, yayan mace da na miji muke da Fariyda sannan duk kun san irin tsananin son da nakeyiwa Fariyda duk family ɗinmu sun san masifar son da nake wa Fariyda tun tana yar ƙaramarta.
Ko mahaifiyata bata da burin da ya wuce aurena da Fariyda, amman Malam ya ɗauketa ya bawa ɗan amininsa sai bina yayi da wai inyi haƙuri, in Raihana tana sona zai aura minta.
Wannan abun shine tabo mafi muni da Aminullah da kawuna suka min.
Sanadin hanani Fariyda har zumuncin iyayen namu ya raunata dan yanzu haka Babana baya barin Ummana taje gidan Malam ko ta'aziya shi bai je musuba, yace shi akaciwa zarafi.
Kuma Alhamdulillah Aminullah dai ya ratsu ya barmin abata”.
Ido suka zuba masa da yanayin yi masa fatan alkhairi. Cikin tsananin zafin son da yakewa Fariyda yaci gaba da cewa.
“Yanzu haka kuma tuni na shirya neman Aurenta har inda zamu zauna nasa an sabunta komai.
Tana fida takaba Ummana da kanta tace zata shawo kan Babana ayi batun aurenmu ko dan ta samu a barta taci gaba da zumunci da yayanta kamar da”.
Babban nasune yace.
“To Allah ya sanya alkhairi yasa sanadin shiryawarsu ne”.
Da Amin suka amsa kana suka rufe taron nasu da tuba da neman yafiyar Allah da mugun nufin su, da yiwa Aminullah addu'a.

Washe gari da yamma. Ɗan guntun murmushi Fariyda tayi wanda iyakarsa kan lips ɗinta, Sai kuma ta sunkuyar da fuskantar dake cike da rauni ido ta zubawa ƙanwar mahafin nata Goggo Abu dake cewa.
“Fariydan Yah Mujahid Allah dai ya nufa shine mijinki na har abada, ƙannen su Zaid na tare dashi”.
Tana zubda ƙwalla tace.
“Aure kam ai na gama shi har abada Goggo, Yah Mujahid kam ga Raihana Malam ya bashi, ya hanata ta saurari kowa fa, yace tana gama karatun ta sai aure”.
Da sauri tace.
“A'a ai kuwa da ya barta ta sauri masu sonta, dan shi Mujahid dama yace, shi dai in ba keba ya haƙura da aure a rayuwarsa shi yasa bai taɓa zuwa zance wurinta ba ko kiranta bai taɓa yiba.
To yanzu kuma tunda da Allah yayiwa mijinki rasuwa yace dama ta biyu ta samu kenan”.
Ido Mamy ta zuba mata cikin sanyi tace.
“Abu ai abun yayi wuri ayiwa Fariyda mgnar aure yanzu”.
Tana kallon matar yayan nata tace.
“To sai yaushe? Haba Maman Nasir ai kuwa aure shi ya dace da Fariyda domin, Muhajid kaɗai zai iya ɗebe mata kemar marigayi ya sama mata natsuwa ya zamewa yaranta uba ya hanasu maraicin, kinga abinda ya dace tana fita takaba kawai a tada mgnar aurensu tunda dama sun fahimci juna.”
Da sauri ta miƙe ta bar parlour tana sharce hawaye.
Ita kuwa Mamy kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Eh to wannan maganar sai ke da Malam zakuyita ni ai kusuɓe ne yasa nasa baki.”
Tana murmushi tace.
“Eh ai in sha Allah tana fita takaba ko da mako ɗaya ne Baban Mujahid ɗin zaizo ya samu Malam da mgnar yanzuma dashi mukazo yazo yi masa ta'aziya ne”.
Kai Mamy ta jinjina cikin mamaki sai kuma ga Mujahid ɗin ya shigo.
Cikin girmamawa ya gaidata kana ya ɗaura da cewa.
“Malam ne yace in kiraki ke da Fariyna kuje ku gaisa da Babana”.
Kai ta gyaɗa mishi tare da miƙewa.
Sai kuma ta fito bayan ta shiga wurin Fariyda.
Ido ya zuba mata tamkar zai mai data cikinsa.
A raunace ta amsa gaisuwar sa kana suka je. Suka gaisa da Baban Mujahid ɗin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.