Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 75 of 86
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 37
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Ido ya rumtse da ƙarfi ya kauda kanshi gefe, yasa hannunsa duka biyu ya dafe gefe da gefen pillow da take kwance a kai, saboda jin abinda take faɗa da kuma yadda tasa yatsarta kan lips ɗinshi tana shafawa tare da yin mgna cikin muryar bacci.
“please Yah Amin ka barni inyi bacci”. Ta ƙare maganar murya can ƙasa maƙoshinta tare da saƙalo wuyansa da hannunta na hagu, na daman kuma dake kan lips ɗin shi a hankali ta fara janshi ƙasa tana motsa lips ɗinta murya a sarƙafe da kasalar bacci tace.
“Yah Amin zo mu kwanta, Please Babe zo mu kwanta pillows ɗin ba daɗi kwanciya”.
Tayi magnar da Muryar da ko shi can ƙasa ya jita, haka yasa Baba Malam bazai jitaba.
“Babe”. Ta kuma kira a hankali ta sake hannunta duka biyu ta kwanta tayi sit alamun taci gaba da baccinta.
Shi kuwa Mahmoud tunda ta kira Babe ɗin ƙarshen ya buɗe lumsassun idanunsa ya watsa mata wani kafurin harara, a ransa ya maimaita Babe, wai Bebe yarinya ta raina kowa wato har shi Yah Amin dinma Babe ma take kiransa dan matsifar rashin kunya da iyayin son girman bala'i.
“Mahmoud”. Baba Malam ya katse matsa mgnar zuci da yake yi da kiran sunansa, haka yasa yayi sauri cusa hannunsa cikin gashin kanta dake baje kan pillow yaja da ƙarfi tare da faɗin.
“Ke tashi baba Malam ke son mgna dake”.
Da sauri ta buɗe idonta gami da miƙewa sunkuye tabi hannunsa da kanta dan jin yadda yake ƙara jan gashin nata.
“Wayyo Allah kaina”. Yarfe hannunsa yayi tare da cewa.
“Malam gata”. Ya ƙare maganar yana miƙa mata wayar tasa, wutan ɗakin ya kunna tare da juyawa ya nufi hanyar fita. A baƙin ƙofar ya tsaya sai kuma ya juyo yana kallonta hannunsa ya harɗe bisa ƙirjinsa ya tsuƙe fuska murya a daƙile yadda ita kaɗai zata iya jinsa yace.
“Kika kuskura kika cewa malam na targaɗa miki hannu, next time karya hannun zan yi, kuma sai na faɗawa Mamy ta gaya mishi zagina kikeyi da tarkacen kawayenki”. Ido ta zuba mishi cike da mmkin ƙarfin halinsa da sauri ta sunkuyar da kanta saboda ganin wani mugun kallon da yake watsa mata.
“Fariyda baccin kikeyi ne?”. Baba Malam ya faɗa, kai ta jujjuya tamkar tana gabanshi murya cike da jin daɗi jin muryar Mahaifin nata tace. “A'a Malam na tashi, ina kwana”. Ajiyan zuciyar jin gamsuwar ƴarsa na cikin ƙoshin lfy ya sauƙe. “Lfy lau Fariyda kuna lfy dai ko ke da yaran da mai gidan naki ko?”. Tana gyara zamanta tace. “Lfy lau Malam ya mutan gida ina Mamy na da Aunty Amarya dasu Sadiq”.
“Alhamdulillah Fariyda duk muna lfy ya Zaid da jikin da sauƙi ko”. Tana mai kallon yadda ya tsareta da idanunsa masu sata yin ƙasa da nata tace.
"A da sauƙi ranar juma'a ma za'ayi aikin”.
“Ba wata matsala ai ko”. Ya tambaya cikin kulawa, tana mai ɗan sauƙe numfashi tace.
“Eh”. Numfashi ya fesar ganin yadda ta nitsu tayi shiru sai kai take gyaɗawa tana mai faɗin.
“To Malam in sha Allah”. Fahimtar kamar nasiha da jan kunne Malam ke mata yasa ya juya ya fita.
Kano.
Sulaiman Zaune a parlour Mama shi da Jidda.
“Yah Sulaiman jiya mafa munyi waya baka cemin zaka zo ba”. Murmushi yayi cikin nitsuwarsa da sauƙin kai yace.
“Nazo ne dan isar da manufata, tunda naga na kasa isar dashi a waya, saboda na lura furta kalmar so kwarjini gareta”.
Da sauri tace.
“Yah Sulaiman banda kwarjinin ma harda bada tsoro takeyi”. Numfashi ya ɗan fesar yacea
. “Kai haba dai Jidda harda tsoro kuma”. Ido ta rumtse ta longwaɓar da kai murya na rawa tace.
“Sosai ma Yah Sulaiman ni dai bayan ƙwarjini harda tsoro da fargaba ta cusa min”. Sai kuma ta ɗanyi shiru tare dasa hannunta tana share hawayen da suka silalo mata, ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe ya ware idonsa a kanta jin tana faɗin.
“Koda yake ni bawai kalmar bace ke bani tsoro, wanda nake so ɗin ne yake yi min kwarjini da bani tsoro, hakan kuma shi ya hanani isar da manufata ta nuna mishi son da nakeyi mishi, son da ya gama rarakemin zuciya”.
Sandarewa Sulaiman ɗin yayi ya kasa faɗin komai sabida fargaba, tana mai zubda ƙwalla tace.
"Naso Yah Salim ya taimaka min ya isarmin da saƙon amman yaƙi”.
Cikin ƙaguwa yace.
"Jidda waye ne shi ɗin? Faɗa min inji wanne mai sa'ar ne”.
Tana mai sunkuyar da kanta ƙasa tace.
“Yah Mahmoud ne, Yah Sulaiman ina son Yah Mahmoud na gayawa Yah Salim sai cemin yake ai Yah Mahmoud bazai taɓa yin aureba.
Na gaji da ɓoyewa na gayawa Mama itama tace wai ai shi baya cikin maza masu iya yin aure. Suka ƙi su taimakawa min har aka aura masa wannan yarinyar Fariyda, a hakan nace ni ina sonshi na cewa Mama ta faɗa mishi ina sonshi, duk sunƙi harda Yah Ahmad duk sunƙi taimaka min. Mama tace bazata faɗa mishiba wai sai dai ta faɗawa Baba, shi kuma ana gaya masa yayi shiru yaƙi cewa komai.
Yah Sulaiman ya zanyi ina son Yah Mahmoud dan girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenmu ka faɗawa Yah Mahmoud ina sonshi wlh shi kaɗai nake gani a matsayin mijin aurena”.
Ta dire mgnar da zamewa daga kan kujerar da take ta durƙusa kan guiwowinta cikin neman alfarma tace.
“Dan girman Allah Yah Sulaiman ka taimaka min wlh zuciyata zata buga in na rasa Yah Mahmoud”.
Cikin sanyin halinsa da murya da taushin zuciyarsa mai cike da kawaici ya kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye, hanki ɗinsa ya miƙa mata, cikin danne soyayyarta da yake dako tsawo shekara ɗaya, cikin jin dashi da Mahmoud duka ɗaya ne a ransa yaji a lokaci guda ya hakurar da ita haƙura na har gaban abadan, cikin sanyin murya yace.
“Nayi alƙawarin isar miki da saƙonki Jidda, kuma in sha Allah zan tsaya iyakar iyawata naga kin mallaki Mahmoud a matsayin mijin aure, tunda shi na mijine Allah ya bashi damar yin mace biyu uku huɗu kafin ɗaya, zan gaya masa kuma zan isarwa Abba ma da muradinki”.
Murmushi mai haɗe da hawayen farin ciki tayi tare da farayi masa godiya da sauƙe ajiyan zuciyar cin nasarar kawar da son da yake mata a zuciyarsa wanda ta fahimci haka tun bayan da Yah Salim ɗinta ya gaya mata cewa Sulaiman fa sonta yake.
Ahmedabad.
A hankali yake goga sabulun a jikinsa yana kewaye gefen kirjinsa na dama. Shyyyt yaja numfashi lokacin da sabulum ya zame yayi kan nimple ɗinsa da Fariyda ta daddatsawa cizo lokacin da yake ja mata targaɗe, gefen lip ɗinshi na ƙasa ya ɗan tauna ya sakarwa kansa ruwa, kanshi ya ɗan sunkuyar ya ƙurawa kan ƙirjin nasa ido, har yanzu shatin haƙorinta nanan ras a kan zagayen ja dake kan nonon, hakan yasa ya ƙarayin jazir ga kumburan da ya ɗanyi saboda maimaita cizon da tayi tayi ba ƙauƙautawa, kumburin ya ɗan tasa dan har jikin nonon ya ɗanyi tim-tim kaɗan ga wani zogin da tun jiya in dai ya taɓa wurin ko ya kwanta a gefen sai yayi ta masa zut-zut shiyasashi kwana a zaune. “Da gaske fa yarinyar nan mayyace, ga abinda tai min zata tsinke min jiki”. Yayi mgnar a zuciyarsa.
Tare da jawo towel ya ɗaura aƙugunsa.
Cikin wasu tattausan rigan bacci AC weather ya saka tare da zuge zip ɗin rigar ya ɗanyi ƙasa dashi ya bar ƙirjinsa a fili saboda ko riga in ya taɓa wurin zafi yake ji, gudun AC ya ƙara, numfashi mai sanyi yaja ni'imtaccen ƙamshin turaren baccinsa da ya fesa ya shaƙa, yana zama kan 3 seatter da shine madadin gado a wurinsa, miƙe sawunsa yayi kan Centre table ɗin dake gabansa system nashi ya ɗaura kan cinyoyinsa tare da fara aikin Companynsu.
Wayarsa da ta kawo haske ya kalla alamun kiransa ko shigowar saƙo, time ya kalla da wayar Fariyda da yake bakin jakar system nashi.
9:45 Pm. “Waye ke kira yanzu kuma”. Yayi mgnar zuci da jawo wayar ganin Ummi ne yasa ya amsa kiran a hankali ya kai wayar kunnensa.
“Barka da dare Ummi bakiyi bacci ba?”.
A daƙile Ummi tace.
“Ina Fariyda”.
A hankali yace.
“Tayi bacci”. Cikin kaurara murya tace.
"Cewa nayi ina take bawai me take yi ba”.
Cikin ƙara jin takaicin yadda kullum akanta Ummi ke iya fushi dashi yace. “Tana bedroom”.
Cikin bada umarni tace.
“Sai ka kai mata wayar tunda ka hallaka mata nata”.
Yunƙura yayi da niyar tashi sai kuma ya koma ya zauna ganin ta fito parlour riƙe da Zaid da yake ƴan ƙanan kuka.
Miƙa mishi Zaid ɗin tayi tare da juyawa zata tafi.
Kan wayar ya buga mata kan yatsunta.
“Washhh Allah na”. Ta faɗa tana juyowa, cikin kallon tsiwa, sai kuma ta amshi wayar jin yana faɗin.
"Ummi gata”.
“Fariyda me yayi miki kuma?”. Tana matse yatsun nata tace.
“Waya ya buga min”.
Kwaffa Ummi tayi da cewa. “Yi haƙuri ko, Allah ya shiryeshi”.
Kai ta gyaɗa tare da cire idanta daga kanshi gani yadda ya tsuƙe fuska da yin kwaffa, kai ya maida ya jingina da jikin kujerar ya lumshe gajiyayyun idanunsa, da kwantar da Zaid kan cikinsa yana ɗan shafa bayansa.
“Ya hannun naki da sauƙi dai kam fatan dai, ba zafin hannun bane ya hanaki bacci.”
Ummi ta tambaya cikin kulawa.
“Alhamdulillah da sauƙi sosai baya min zafi, sai dai hannun ba ƙarfi, ko kaɗan”.
Fariyda ta bata amsa tana mai tsaida idonta kanshi.
Shi kuwa Mahmoud hannunsa ya ɗan kife kan Zaid yana shafa sumar kan Zaid da ta cika mishi kai har ta sunkuyo kan goshinsa a ranshi yake mgnar zuci Zuwa dashi gyaran kai.
Ummi ce ta katse mata zurun da tayi na zuba mishi ido shi da Zaid ɗin da take ganin kamarsu a fili. “To me ya hanaki bacci ke da ba waya ba abokin hira bare ince hira kike”.
Numfashi mai sanyi ta ɗan fesar tana gyara tsayuwanta tace.
“Kan Zaitoon ne ya tsufa, shine na warware mata kitson akan zan mata wani, kuma na kasa sabida hannun ba ƙarfi, ko kai nama bana iya tajewa, tunda abin ya faru ban taje kan ba so nake ma in samu inje a wanke min kan”.
Ummi tace. “Ba matsala gobe zai kaiku saloon ɗin a wanke muku”.
Ido ya buɗe a hankali sabida jikinsa na gaya masa ana kallonsa, da sauri ta kauda kanta daga gareshi lokacin da taga ya buɗe idonsa.
“Mitssssss”. Yaja dogon tsaki tare da sa hannunsa ya jawo gefen rigarsa ya ƙara rufe ƙirjinsa da tunda ta shigo ya rufe.
“Ina Mahmoud ɗin?”. Ummi ta tambaya. Da sauri tace. “Gashi nan”.
Ummi tace
“Bashi wayar”. To tace ta miƙa mishi wayar, amsa yayi yana kaiwa kunne yace.
"Na'am Ummi”. Murya a daƙile cikin bada umarni tace. “In Allah ya kaimu gobe da safe ka kai Fariyda wurin gyaran kai ita da Zaitoon, tunda ka ɓalle mata hannun bazata iya yi da kanta ba”. Cikin sanyi yace. “Ummi ai ban”. A faɗace tace. “Umarnine in kuma ban kai in saka kayi ba, shike nan Mahmoud kayi yadda kaga dama, kaima ga yaran nan ai Allah ya baka zasu saka mana abinda kake mana”. A hankali yace. “Zan kaita, Ummi kiyi min fatan al'khairi akan su Zaid dan Allah karki mana mugun fata kin san sune kaɗai tsammani na a duniya in kin min mugun fata a kansu ya zanyi”. A hankali tace. "Allah ya shiryeka yayi maka al'barka zaka samu ƙarin wasu in sha Allah”.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
“Ummi ta yaya kuke tsammani samun wasu kamar kuna mance baya, lafiyar itace gaba ai”.
Yayi mgnar yana ɗan gyarawa Zaid kwanciya a jikinsa, sheyyyt yaja ɗan numfashi sabida zogin da wurin yayi masa lokaci da Zaid ya mirgina hannunsa kan wurin.
Ita kuwa Fariyda ɗan ƙara matsoshi tayi tare da miƙa mishi hannunta alamun ya bata wayar kar ya katse kiran.
Ko ta inda take bai kallaba sai lumshe idanunsa da yayi yana sauraron Ummi dake faɗin.
“Ai Allah nace Mahmoud kuma shi baya bacci, sannan shi maji roƙon bawane, tunda ka samu lfy ai haihuwar ma bazamu yanke ƙauna ba, Allah zamuyi ta roƙa shine mai bamu dukkan abinda muke nema.”
Shiru yayi ya fesar da numfashi a hankali.
Ummi taci gaba da cewa
“Allah ya yaye maka wannan taurin kan da fushin don yanzu shine babban cutar ka”.
Da Amin Ya amsa jin ta katse kiran ne yasashi juyo kanshi gefen hagu.
“Ɗaukeshi”. Ya faɗa yana ɗan gyara kwanciyarsa.
Tana ƙoƙarin juyawa tace. “Kuka yake tayi min fa ya hanani bacci”. Ba tare da ya kalleta ba yaja gajeren tsaki .
"Ɗagashi”. Ya kuma faɗa a ƙaurare, haka yasa ta sunkuyo kanshi.
Da sauri yasa hannunsa ya damƙe hannunta da ta cusa ƙasan hannun Zaid dake kan ciwonsa.
Ɗago kanta tayi ta kwaɓe fuska saboda jin yadda ya damƙe mata hannun da ƙarfi, ido cikin ido sukayi dashi, janye hannun yayi tsakanin hannun Zaid da ƙirjinsa.
Har lau idonsa na kanta,
Cikin tsoro da fargaban kada ya sake targaɗa mata hannun murya na rawa tace.
“Dan Allah ka sake min hannu karka jimin ciwo wannan ma bai gama warkewa ba kayi haƙuri”.
Ta ƙare maganar da janye idonta daga cikin nasa idanun.
Hannunsa daya riƙe natan ta kalla cike da mmkin ganin yadda hannun ke tsuma sabida zafin famesa da tayi.
Yarfa hannun nata yayi ya komawa ya jingina bayansa jikin kujerar tare da buɗa lips ɗinsa da suke tsuma ya saki wani irin sauti mai sarƙafe da numfashi. “Hashyyyyyyyy”. Yaja numfashi tare da juyowa ta inda take.........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.