Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 80 of 86
Kiran Abba daya shigone ya hanashi maida wayarsa daya fitar daga aljihu dan duba time dan cewa da Dr ɗin yayi in suna so zasu iya tafi dan sai bayan awa uku zai farka kuma Nurses ɗinsu zasu kula dashi da kansu.
Kiran Abba ya amsa ganin ya kusa katsewa.
“Mahmoud ya jikin Zaidu yanzu Malam Ibrahim yazo yake tambayata ko munji labarinku, wai ya kira wayar Fariyda bata shiga, kai kuma baka ɗaga ba”. Cikin sanyi yace.
“Wayar tana aljuhune kuma a silent take ita kuma tata ba charge ne ya mutu shiyasa. Alhamdulillah Abba jikinsa da sauƙi sosai yanzu kam, yana bacci ne sunce sai bayan awa uku zai farka”. Cikin sauƙe numfashi da gamsuwa Abba yace.
“To Alhamdulillah ai hankalinmu ya tashi, ina Fariyda.”
Miƙa mata wayar yayi tare da yin ƙasa da murya yace.
“Kinyi salla?”.
Jikinta ta ɗan duba tana amsar wayar tace.
“Banyi ba, ba hijab”. Ta ƙare maganar tare da amsar wayar tayiwa Abba sallama.
Shi kuwa Mahmoud Zaitoon dake bacci ya ɗauka tare da fita daga ɗakin.
Cikin sanyi tace.
“Abba ɗazu kam naji tsoro, amman yanzu kam Alhamdulillah, yana baccine”.
Cikin girma yace to ga Malam.
“Yanzu dai kinyi shiru ko”. Baba Malam ya tambaya cikin kulawa.
“Malam nayi shiru munatayi masa addu'a, kuma Alhamdulillah ya samu sauƙi sosai”.
Daga nan dai sukayi sallama.
Juyowa ta ɗanyi jin an buɗe ƙofar an shigo wani Dr ne da Nurses ɗaya suka shigo yan dube dube sukayi kana suka fita.
Kan 3 seatter ta koma ta zauna tare da amsa kiran Ummi.
“A yanzu kam Alhamdulillah Ummi gashi nan ma kin ganshi bacci yakeyi”. Kai Ummi ta jinjina tare da miƙawa Goggo Dada da sauri Aunty Amina ma ta dawo gefen Goggo Dada.
“Aunty Amina ya gida, ina Hagiz, naji Huzaifa ma ya dawo ko”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Ba wannan ba ya jikin Zaid ina Mahmoud”. Ɗan murmushi tayi tace ya fita da Zaitoon.
Zaid kuma da sauƙi, naga missed calls ɗin ki a wayata. Shine ya karɓe shiyasa ban ɗagaba ban bi bayan kiranki ba”. Ɗan murmushi tayi tare da cewa. “Ni dai yanzu ta jikin Zaid nake”.
Nuna mata Zaid dake bacci tayi daga nan suka ɗanyi hira daga bisani sukayi sallama.
Kano
“To Alhamdulillah yanzu dai anyi aiki, kuma jiki da sauƙi, dama Salim shi ya hana asa ranar bikinsu da Salma sabida wai yafi son sai anyi wa Zaid aiki, yasan ba daɗe zasuyi ba zasu dawo in dai anyi aikin, sai asa bikin yadda sai sun dawo”. Abba ya dire mgnar yana mai kallon aminin nasa, cikin gamsuwa Malam yace.
“Yanzu kam ai sun kusa dawowa in sha Allah, dan haka musa bikin zuwa daya ga watan goma”. Kai Sulaiman dake gefe ya ɗan gyaɗa tare da cewa.
“Yau saura kwana sha huɗu kenan”. Kai Malam ya jinjina masa alamar eh.
A hankali ta juyo jin an buɗe ƙofar.
Zaitoon ne ta shigo da gudu, rungumeta tayi tare da ɗan kallonta, fes da ita sai ƙamshi take yi kayan jikinta ta kalla alamun yayi mata wanka ya shirta sab cikin kekkyawar rigarta, bag ɗin hannunsa ya ajiye tare da ɗan isowa bakin gadon.
Numfashi mai sanyi ta fesar tana shaƙar ƙamshin jikinsa, sai kuma ta ɗan kalli tattausan yadin dake jikinsa fari ƙal mai ɗinkin hafl jomfa ɗan cib-cib jikinsa rigar mai gajeren hannun sai hula damanga blue wanda yazo iri ɗaya da kalliyar rigar Sai takalmin sawunsa suma blue ne, wani irin ƙamshi mai sanyin daɗi yake bazawa, nazartar shigar tasane yasa ta tunowa yau ɗin jumma'a ne, wanda yayi dai-dai da cika sati uku da baro gida Nigeria.
Bag ɗin ta ɗauka ta shiga bathroom ɗin.
Sai kuma ta fito tana kallonsa, shi ko Mahmoud tunda ya shigo ko inda take bai kallaba bare yayi mata magna, ajiye jakar tayi tare da cewa.
“Banyi salla bafa”. Jin bai ce komaiba bai kuma kalleta bane yasa ta kuma cewa.
“Banyi sallan bafa, gashi har 12:15 pm”.
Ba tare da ya kalletaba yace. "Dama can bata dameki ba ai”.
Da sauri tace. “Kamar ya bata dameni ba, rashin abin rufuwane fa ya hanani salla, kaje kayi wanka ka canza kaya kuma baka kawo min hijjab ba”.
Kanta ta kauda ganin kallon daya watsa mata, ya ɗore da cewa.
“Ni ɗan aikenki ne? In sallar ta dameki, ai ga hanya gacan Taxi a waje kije kiyi salla ki ɗauko hijjab in bata damekiba ki zauna, dama jahannama tana buƙatar abinci kuma da irinku masu wasa da salla zataci ta ƙoshi, kamar yadda Allah yayi mata al'ƙawarin ƙoshi ranar gobe alkiyam”.
Daga nan ya jawo Zaitoon ya koma kujera suka zauna. Cikin tura baki ta nufi hanyar fita tare da faɗin.
“Da kuma mazinata ba, masu yaɗa fasadi a ban ƙasa”.
Da sauri ta ƙarasa fita tare da jan Kofar saboda ganin yadda ya juyo.
Kano.
Dawakin dakata.
Mama ce zaune gaban Mala hadi Jidda na gefenta.
Idonsu kab na kan Tray yashin dake gabansu wanda yake wasu rubuce-rubuce bisa ƙasan.
Wani irin makirin murmushi yayi tare da cewa.
“Ba gaibu muke ganiba, Allah ne yake lamun ce mana, muga abinda ba kowa ke ganiba, muma har mu lamuncewa wasu su gani leƙo nan kan Tray nan da kyau”. ya faɗa tare da ƙara tura musu Tray gabansu.
Wani irin nannauyan numfashi Jidda ta sauke tare da ƙara sunkuyowa saboda ganinta ras a cikin yashin Tamkar TV sai kuma Mahmoud dake rungume da ita ta baya wanda ita kuma take rungume da jariri.
Wani irin murmushi Mama tayi tare da cewa.
“ikon Allah Mahmoud harda haihuwa ma zai yi kenan”.
Dariya yayi tare da cewa.
“Kuma da Jidda zai haihuba”.
Da sauri Jidda tace.
“Amman a nan yayi babba bai kai haka girma bafa”. Cikin sauri yace.
“Ai nace muku auren ba yanzuba zai iya kai shekara ɗaya biyu zuwa uku kafin ayi auren”. Cikin sauri tace.
"Zan jirashi wlh in dai zan mallakeshi zan jirashi”
Sai kuma ta ƙara leƙa Tray da sauri ta zuba wa fuskarsa ido, gil hoton ya ɓace ɓat.
Suna fita gidan Mujahid na parking a ƙofar gidan.
“Nace maka kada ka damu Fariyda fa matar kace, tabbas zaka aureta, kai dai ka jira dawowarsu kawai zaɓin aurenta yana kanka harda rabon yara maza hudu a jere a tsaka ninku”.
Ahmedabad.......
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 41
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Ahmedabad.
A hankali yake ɗan shafa kan Zaid ɗin da ya wuni bacci, har bayan sallan isha ya farka, kasan cewar allurar baccin bata gama sakinsa ba, yasa jikinsa yake a mace, sai ya ɓuɗe idon ya kuma lumshewa.
Da taimakon ɗan ruwan da ke saƙale a jikinsa ya hana yunwa tasiri a kansa duk da yanzu 24 hours cib kenan baici ko sha wani abin ciba. Gyara riƙo wayar dake hannunsa yayi yace.
“Eh idonsa biyu tunda ya farka bai maida baccinba”. Sai kuma ya ɗan yi shiru na kusan 56 seconds, numfashi ya ɗan fesar yana gyara zamansa kan lutsumemiyar kujerar 1 sitter dake bakin gadon.
“Eh mu yanzu 11:30 pm”.
A hankali ya kamo hannun Zaid ɗin da ya ɗagashi sama zai sauƙeshi dai-dai kan bendegin dake liƙe da ɗan plaster a wurin da akayi masa aikin.
Meda hannun yayi gefe, sunkuyowa yayi ya ɗan sumbaci goshinsa, dariya mai ɗan sauti yayi wanda yasa Aunty Amina dake waya dashi cewa. “Shine yake dariya ko Zaitoon?”. Cikin ɗan fara ƙosawa da surutun yace. “Shine saida safe”. Daga nan ya katse kiran.
Yana ajiye wayar kan gadon kiran Bappa Lawan na shiga.
Cikin gajiya da kasala ya ɗauka, maganar 4 minutes kusa kana sukayi sallama. Baki ya taɓe tare da kauda kai daga kan Fariyda da takeyi sallan isha, time ya duba ganin har kusan sha biyun dare kenan.
Ita kuwa Fariyda koda ta idar kan kujerar 3 seatter ɗin ta koma, ɗaga Zaitoon tayi a hankali.
A kan ɗam gadon ta kwantar da Zaitoon ɗin can gefen Zaid ɗin, hulan kanta ta gyara mata, Sannan ta juya ta koma kan kujerar ta kwanta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.