Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 79 of 86

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 40
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Innalillahi”. Ta faɗa da ƙarfi cikin tsananin rawan jiki da tashin hankali ta buɗe ƙofar ta fitowa da sassarfa kiciɓis tayi da Mahmoud da Dr Zara da Nurses guda biyu. Cikin haki da firgita ta kamo hannun Mahmoud ta jawoshi gami da yafito Dr ta juya ciki tana jan hannun Mahmoud cikin rawan muryar da hakin tace.
“Zaid Zaid!! kazo kaga yadda Zaid ɗin mu yake yi”. Da sauri ya fizge hannunsa ya wuceta, yabi bayan Dr Sara da Nurses ɗin da suka nufi cikin ɗakin da gudu.
Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un shine Abinda Mahmoud ɗin ke faɗi yana jingina jikin gini sabida jin sawunsa suna gab da zubar dashi ƙasa dan tashin hankali da ya diro masa in one minute na ganin yadda Dr Zara ke rikice a kan Zaid ɗin.
Ossigin ɗin da ta mannawa Zaid ɗin a hanci ya zubawa ido sai kuma, ya kalli yadda ta juyo a zafafe tana cewa ɗaya Nurses ɗin ta kira mata Dr Imran Patel ta Telephone ɗin dake maƙale a gefen.
Sai kuma ta kalli É—aya tare da faÉ—a mata sunan allurar da take son taje pharmacy É—insu ta kawo mata.
Ƙirjinsa ta kuma fara ɗan daddan nawa.
Fariyda kuwa tunda ta shigo ta tsaya a bakin ƙofar bata shigoba bata kuma fitaba.
“Yah salam”. Shine kalmar da Dr Zara ta faɗa dai-dai lokacin da taga Numfashin Zaid ɗin yayi ɗib.
Wani irin ƙarƙarwa da tsuma Mahmoud ya fara Fariyda kuwa da sauri ta nufi bakin gadon.
Kamo hannunta yayi tare da jujjuya mata kai, cikin wani irin gigitaccen yanayi ta faɗa jikinsa ta rungumeshi da ƙarfi, cikin tsuma yasa hannunsa duka biyu ya rungumeta cikin jikinsa
Ƙara matseta yayi cikin jikinsa tare da fara jujjuyawa kansa da ƙarfi gami da taune lip ɗin shi.
É—imautaccen runguma suka yiwa junansu.
kuka mai cike da sassayan sautin dake bayyana zafin raunin da zuciya da jikinta yayi Fariyda ta saki.
Shigowar Dr Imran Patel da wasu nurse ɗin ne yasa Dr Zara sauƙe ajiyan zuciya da ɗan ja da baya, cikin zafin nama da ƙwarewa Dr Imran ya dawo inda take, duƙufa yayi kansa ya fara ƙoƙarin ceto numfashinsa daya ɗauke cak.
Ita kuwa Dr Zara alurar da ta aika a kawo mata ta karɓa ta haɗa ruwan, cikin sauri ta dawo gefen Dr Imran ɗin ta miƙa masa allurar tana faɗa mai sunan allurar.

Ita kuma Fariyda kuka mai sassayan sauti take yi tare da fara mgna cikin raunatacciyar murya.
“Zaid ɗinmu ya mutu ko? Ya tafi ya barmu ko?”.
Da sauri yasa hannunsa duka biyu ya tallabo fuskantar idanta dake kwaranyar da hawaye ya kalla, tare da fara jujjuya mata kai sai kuma ya sake rungumeta ya manna kanta bisa ƙirjinsa kanshi ya sunkuyar dai-dai kan kunnenta cikin ɗimuwa yace.
“Farriyyha bai mutuba, ke uwace ki daina faɗin zai mutu, kiyi ta masa fatan waraka, zakisa zuciyata ta buga in kina faɗin ya mutu, shine madadin Yah Amin ɗina ina tsoron rasashi.” wani sabon kuka ne ya taso mata saboda jin yadda Doctors ɗin keta muhawarar yadda numfashinsa zai dawo duk da da Indiancin suke yi ɗan surkawa da suke yi da turanci kaɗan yasa ta fahimtar abinda suke faɗin.
Wani irin ƙarƙarwa sawuta ya farayi mata tam kar mazari haka ne yasa ta fara zamewa tanayin ƙasa, da sauri ya tallabeta tare da haɗeta a jikinsa. A hankali ya ɗan ja sawunsa da sukayi masifar nauyi, a gefen Zaitoon dake ta bacci ya zauna tare da ita a jikinsa, a hankali ta ɗan juyo kanta jin ƙara ya fara ƙeeeyyy ƙeeeyyy kamar na ɗazun.
Cikin rawan jeki ta zaro wayarta dake jikin a'jihun rigarta, layin Baba Malam ta kira ba tare da sanin abin cewa ba.
Cikin sa'a bugu É—aya ana biyu ya É—auka.
Sunkuyowa yayi kanta jin tana magna cikin rawan murya.
“Baba Malam Zaid na ba lfy, kasa minshi a addu'arka, anyi masa aiki tun ɗazu aka fito dashi, jikinsa ya rikice baya ko numfashi fa Malam ya mutu ko?”.
Tayi magnar ba tare da ta amsa sallamar da mahaifin nata yayi mataba. Jin yadda take cikin ruÉ—anine yasa Baba Malam É—in yin gyaran murya tare da cewa.
“Ba komai Fariyda in sha Allah Zaid zai samu lfy, zan mishi addu'a, amman addu'arki tafi tawa tasiri a kansa a matsayinki na uwa a gareshi, ki daina kuka kiyi masa addu'a.”
Mahmoud kuwa bayanta yake É—an bubbugawa a hankali, har lau idonsa na rufe tsoron buÉ—esu yake, saboda baya son ganin yadda Zaid É—in ke kwance kamar gawa, uwa uba ga kumburin da cikinsa yayi.
Cikin rawan murya tace.
"Allah ya bashi lfy Baba Malam zan mishi addu'a, Allah ya rayashi ya zamewa babansa al'wadussaliha. Allah ya rayashi ya zamewa ƙanin mahaifinsa ɗan da Yah Amin ke cewa nasane ya meye masa gurɓinsa”.
Cikin sanyin jiki Baba Malam yace.
"Amin Fariyda yanzu kune ina? Ina Mahmoud ɗin?”.
Da sauri tace.
“Muna asbiti, gashi nan Baba Malam”.
Da sauri ta miƙa masa wayar amsa yayi gami da yin sallama.
“Ya jikin Zaid ɗin Mahmoud”. Cikin rauni yace.
“Malam sun mishi aiki, amman baya numfashi fa, tun ɗazu, suna kanshi”.
Cikin basa ƙarfin guiwa Malam yace.
“Ba komai Mahmoud kuyi ta masa addu'a kaji ko, ka ɗaure zuciyarka ka taushin Fariyda ta bar kukan nan”.
Cikin sanyi yace.
“Malam itace ke tayar min da hankali kukanta na tayar min da hankali ina tsoron rasa Zaid.”
Cikin sauƙe numfashi Baba Malam yace.
“In sha Allah Zaid zai samu sauƙi zaka rayu tare da ɗanka, kuyi ta masa addu'a kaji ko”.
Kai ya gyaÉ—a sai kuma ya fara jero masa addu'a jin haka ne yasa baba Malam katse kiran.

A hankali ta ɗago kanta cikin sanyi ido na zubda ƙwallan murya can ƙasa tace.
"Kayi masa addu'a Malam yace addu'armu tafi tasu ma karfi a kansa”.
Ido cikin ido ya tsura mata sai kuma ya É—an lumshe É—imautattun idanun nasa kana a hankali ya buÉ—e su kan gashin girarta da ya haÉ—e har dai-dai tsakiyar tsinin hancinta wanda yake sak irin na Kajol, ido ya zuba mata ba tare da yace mata komai ba.
Idon ta É—an fidda tare da fara jijjiga kafaÉ—arsa.
“Numfashinsa ya dawo ne?”. Dai-dai lokacin kuma Dr Imran Patel yayi nasaran ceto numfashinsa Zaid kusan duk a tare sukace.
“Alhamdulillah”. Da sauri ta miƙe tsaye, da nufin zuwa bakin gadon hannunta ya riƙo tare cewa.
“Please ki bari suyi aikinsu, zo ki zauna muyi masa addu'a”.
Da sauri ta dawo ta zauna gefensa tare da fara jero addu'a.

Kusan awa biyu su Dr Imran sukayi a kan Zaid, su duba nan su gwada can su matsanan su ja can, su mai wannan allurar su É—aura mai wannan ruwan.
Allah cikin ikonsa ya farfaɗo numfashinsa ya dawo dai-dai bayan yayita sakin iska akai akai cikin ikon Allah cikin ya saɓe ya koma dai-dai.
Allurar baccin da sukayi masa ya taimaka ƙwarai wurin samun nitsuwarsa.

Numfashi mai sanyi suka fesar a tare ganin Doctors ɗin sun fita cikin murmushi da basu ƙarfin guiwa da tabbatar musu yanzu babu wata matsala.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.