Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 60 of 86
Wannan na tafiya ba dadewa, wasu Flight Attendance É—in biyu suka iso, É—aya na É—auke da tray da cups É—in drinks and water, ko kallonsu Mahmoud baiba, ita kuwa Fariyda cikin ranta take mgnar zuci.
“Yau dai zanga ta kan Æ™yanÆ™yami bazanci kazaba sai kaza, bazanci a plate da spoon É—in kowaba sai a nashi, zanga uwar da zata maka yadda kakeso kake baza isa da iko a gidanâ€.
Tana cikin magnar zucin nema bata san sanda ya sallamesu bama, da harara da girgiza kai.
Jim kaɗan da tafiyarsu wannan ta farkon ta dawo ɗauke da tray da baby food kusan kala uku-uku a cikin yan bowl da spoon da ɗan towel sai kuma bobo shima ɗaɗɗaya, gyara zama tayi tare da ajiye Tray akan Table seat ɗin. Da sauri Zaitoon ta fara juyi. Cerelac ɗin da taga hardashi a abinda suka kawo ɗin ne, ta fara bawa Zaitoon ɗin. tana kallon Mahmoud dake ce mata, har su sauƙa baya bukatar komai. kai ta jinnina tare da tambayar Fariyda, cikinta ta ɗan shafa dan a lokacin dai bata jin yunwa shiyasa tace, bata bukatar komai sai ta gama dasu Zaitoon. daga nan ta juya ta tafi.
Zaid dake ta miƙa tare da son juyowa ta kalla, ɗan ɗago kanta tayi ta kalli Mahmoud da ya kamata ya taimaka mata wurin basu abincin.
Ga mamakinta ya maida kanshi gefe ya lumshe idanunsa da alamun kuma tuni ya maida baccinsa, ganin hakan ne yasa ta taɓe baki tare da hararansa, kana ta fara bawa Zaid ɗin a haka har ta gamaba basu, abinda zasu iya ci, tissue ɗin dake gefen tray ta ɗauka tare da goge musu bakinsu, kana ta ɗauki bobon nasu tasa a jakarta, dai-dai lokacin kuma wata Flight Attendance ɗin tazo ta fara tattare komai da suka kawo na passengers dake ɗin.
Wayarta ta ɗan ɗaga dan duba lokaci tana maida ganinta kan Zaid da shima tuni ya maida baccinsa tana gyara zamanta tare da kishingiɗa ganin ƙarfe 7:00 pm ne yasa ta lumshe idanta tana faɗin.
"Mutum kamar toy yanzu ido buÉ—e anjima kaji yayi bacci bazai bari yayi mai isarsa ba, masifa tasa ya farka da bala'i.
Shafa ƙan Zaitoon tana mai lumshe idanta sabida so take tayi bacci tunda yanzu ne ma suka yi rabin tafiyar abinda ya rage nema ya ɗan fi yawa, baby blanket taga ana miƙo mata lokacin data buɗe idon ta jin ana mata magna, amsa tayi tare da rufe Zaid dake cikinta, da sauri ta kuma janye hannunta tana tsuke fuska, tsaki yaja tare da cewa.
“Bana son kallon mayaitar nan fa, kina hanani bacciâ€. Da sauri tace.
“Nifa Zaid nake rufe waâ€. Ta Æ™are maganar tana rufe Zaitoon ma da É—aya tattausan baby blanket, tsaki yaja tare da maida idonsa ya lumshe ya rungume Zaid É—in ya haÉ—e da blanket É—in, ajiyan zuciya ya sauÆ™e dan sai yanzu yajishi É—an dama-dama duk dai bawai ya jisa comfortable bane, a haka dai cikin rashin jin daÉ—in bacci yayi awon gaba dashi.
Itama bata san sanda baccin ya sureta ba.
Can cikin baccin taji kamar ana taɓata, sai kuma ta ɗan fara buɗe idonta dan jin yess taɓata akeyi, da sauri ta buɗe idon ta, Flight Attendance ɗin forkoce ke taɓata tare da cewa mata, ta tashi yanzu zasuyi landing a Ethiopia Addis ababa.
Cikin sanyi ta gyara zamanta da kyau tare da É—an maida kanta ta jingina ta lumshe idanta, dan wani irin bacci ne mai nauyi ke danneta, dan rashin yin baccin rana da batayi ba.
Shi kuwa Mahmoud kanshi ya É—an mirgina hagu da dama dan wuyansa da yayi masa tsami.
A hankali ya maida numfashi tare da sauƙewa dai-dai lokacin da suka dira a Ethiopia, jim kaɗan da sauƙarsu aka buɗe marfin jirgin tare da sanarwar fita.
A hankali ya miƙe tsaye tare da zaro travelling box ɗinsa mai masifar kyau daga samansu.
Sai kuma ya ɗan ajiyeshi kan seat ɗin daya tashi, baki ya taɓe ganin bacci ta maida bata ma san sun sauƙanba, a hankali ya sunkuyo kanta, seat belt ɗin jikinta ya ɗan sake, hakan ya bashi damar ɗaga Zaitoon daga jikinta.
Zaid da tun ɗazu suka farka a tare ne, ya ajiye kan travelling box ɗinsa ai kuwa ya ɗale gam ya zauna tare da riƙe hannjn, sai kuma ya ɗago Zaitoon ya saɓata a kafaɗa tare da tsallaka Fariyda ya juya ya nufi hanyar fita.
A hankali ta buɗe idonta saboda jin ana tashinta daga baccin cikin sauri ta miƙe tsaye, jin ba Zaitoon a jikinta, kanta ta juya ido ta zare ganin baya kan seat ɗinsa.
“Innalillahi to tafiya yayi dasu ya barni ina bacciâ€. Ta faÉ—a tare da jawo hand lounge É—inta, tare da saÉ“a hand bag É—inta a kafaÉ—a, ta nufi hanyar fita da sauri. Ido ta fara rabawa lokacin da ta sako kanta wanje a hankali take taka steps É—in jirgin tana sauÆ™a tana kuma Æ™ara ware idanunta.
Da sauri ta fara bin bayan waɗanda ke gabanta, cikin jin ƙunci da tafasa a zuciyarta.
Ta lumshe idanta dake cike da ƙwalla shar suka zubo bisa ƙuncinta dai-dai lokacin da ta shiga
Arrival É—in ganin bashi ba alamarsa, da sauri ta fara zazzagaywa tana É—an dubawa, inda luggages É—in mutane keta juyawa ta nufa nan ma, bashi.
Wani irin rauni da ƙuncine yasata zama a gefen wata mata tare da riƙe kanta da hannun duka biyu.
Sai kuma ta sauke hannun tare, da É—aukar wayarta ta cireta a Airplane, da sauri ta bude data tare da shiga WhatsApp, kan number Ummi ta shiga da sauri har jikinta na rawa, voice tayi mata har guda biyu.
Zata fara na uku ne kuma ta juyo da sauri tana kallon matar data iso kusa da ita yanzu.
“Har yanzu kina nan ne? Naga twins naki da mijinki sun fitaâ€.
Da sauri ta kalli wannan matar da ta zauna kusa da Mahmoud a Abuja tana sharce hawayenta tace.
"Ta ina sukayiâ€. Ido ta zuba mata cikin son fahimtar yanayinta sai kuma ta É—an kalli ta inda taga Mahmoud ya nufa.
Jakarta da ta iso kusa dasu tasa hannunta ta É—auka tare da cewa.
“Mu tafi ta nan ya fita.â€
Da sauri tabi bayanta.
“Iya karku Ethiopia ne?â€.
Matar ta kuma tambayarta.
“No zamu wuce Indiaâ€.
Juyawa tayi ta É—an kalleta kana tace.
“Kuma Transit ne kenan, nima India zan wuce har kolkata kufa.â€
Tana jin wasu hawayen na ciko mata ido tace.
"Ahmedabad zamu jeâ€.
Tana ɗan ƙara kallonta tace.
"Kinga gacan Bus É—in da zai kaimu hotel É—in masauÆ™imu, transit É—in namu 21 hours ne.â€
Sai lokacin ta kalli time 10:45 Pm.
Tsorone sosai ya rufeta lokacin da suka isa jikin Bus É—in dake dauke da tambarin Golden Tulip Addis ababa hotel.
Sai kuma ta É—an tsaya tana kallon matar da har ta kutsa kai cikin bus É—in da yafi kama da train sabida girmansa da kyansa.
Tsorone ya rufeta duk da matar batayi kalan muguntaba to amman ai ba'a gane mugu a ido.
“Ki shigo mana baki Ga hadarin dake gab da sauÆ™owa baneâ€.
Da sauri ta É—an É—aga kanta, sai kuma ta kalli mafi akasarin passengers É—in flight É—in nasu duk suna shiga.
Wayarta ta kalla jin shigowan saƙo, location hotel ɗin da Bus ɗin ke tsaye gabanta ya shigo mata.
Haka yasa ta kutsa kai ciki.
A hankali suka fara tafiya tana bin bayan matar, dan seat É—in forko-forkon duk da mutane a kai.
“Yauwa ga mijin naki nan da yarankiâ€.
Matar ta faÉ—a mata tare da nuna mata gefen damanta, inda Mahmoud É—in ke zaune kujerar jikin window Zaitoon na rungume a jikinsa Zaid kuma na kan kujerar,
Sunkuyowa tayi ta daga Zaid É—in tare da zama inda ta É—agashi.
Cikin takaici da tsiwar data kori tsoron da take cikin tace
“No ba mijina bane, Æ™anin mijinane baki ganshi yarâ€.
Da sauri tayi shiru ba tare da ta ƙarisa ba ta runtse idonta da ƙarfi dan jin yadda yasa kafarsa ya take yan yatsun ƙafarta harda murzawa.
Da sauri ta buÉ—e idonta tana kallonshi, shi kuma matar da ta zauna a bayansu yake sauraron abinda take faÉ—i.
"Wannan É—in ne yaro, to ke kuma sai ace miki jaririya kenanâ€.
Cikin sanyi ta fara yarfa yatsun hannunta tare da kallonsa.
“Allah ya iâ€.
Sai kuma tayi shiru jin ya kuma ƙara murza mata yatsun ta da Boot ɗin dake sawunsa.
Jan Bus ɗin da akayi ne yasata janye ƙafarta da ƙarfi tare da yin mutsu-mutsu da bakinta.
“Rashin kunya zakayi min neâ€.
Da sauri tace.
“Dabaka tada ni ba ai an tadaniâ€.
Wani irin mugun kallo ya watsa mata tare da yi mata kallon nan na cewa.
“Ni mai gadinki ne, da zan rinÆ™a ta dake daga baccin asarar da kikeyiâ€.
Cikin ƙasa-ƙasa da murya tace.
"Ai kai ma kayi baccinâ€.
Tai magnar yadd bazai jitaba.
Numfashi mai sanyi ta fesar tare da ware idonta tana kallon cikin babban birnin Ethiopia da yayi masifar sakar mata salama.
Tabbas Addis ababa duniya ne.
Da sauri ta É—an janye kanta lokacin da ya juyo kansa kanta tare da watsa mata kallon.
“Ke ki dena min kallon maytar nanfaâ€.
A hankali tace.
“Nifa ba kai nake gani ba, garin nake ganiâ€.
Dan sarai tana gane me yake nufi a kallon nasa duk da ko ƙala baice mataba tunda suka kama hanya.
A kufule yaja tsakin da yasata jingina kanta da jikin kujera.
11:00 Pm tayi musu a cikin Reception ɗin hamshaƙin hotel ɗin da yake tamkar rana.
Da É—an saurin take bin bayansa rungume da Zaid shi kuma ya É—aura Zaitoon kan trollingnsa yana turawa.
Room key ɗin da ya karɓa wanda na card ne ke hannunsa, ita kuwa rike da jakarta da hand bag ɗinta.
lifter suka shiga, tare da É—an yin yan danne danne a jiki.
Jim kaɗan ƙofar ta buɗu, wani corridor ne mai girma, sai kofofin ɗakuna dake fuskantar juna.
Number É—akin ya duba kana yasa card É—in ya buÉ—e.
Yana gaba tana biye dashi a baya.
Cikin wani irin yanayi mai cike da sa'ada ta sauƙe numfashi lokacin da ta shiga Tsakiyar ɗaki. Single room ne, sai bathroom.
Two bed ne a ɗakin masu masakaicin girma, shimfiɗine na alfarma fari ƙal a jiki gadon da pillows da tattausan duvet da ya amsa sunansa, sai Wordrobe a cikin corridorn dake hanyan toilet ɗin.
can gefen sai TV da fridge.
Kanta ta É—an sunkuyar lokacin da ta taka carpert É—in dake tsakiyar É—akin.
Yah Salam shine Abinda ta furta tare da kallon.
Zaitoon da ya ajiye kan gado, sai kuma yaja box É—in nasa yayi cikin corridorn É—in.
Yana shiga ya É—an juyo yana kallon cikin É—akin yess na cikin É—akin baza suga na cikin corridorn É—inba sai dai in mutum ya taso ya dawo bakin wurin ne.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.