Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 22 of 86

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 moniepont sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276. Mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna.

By
"GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 9
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set ɗin kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set ɗin hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
Haɗine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.

Idan kin sayi kaya in dai set ɗin kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuɗin Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.

0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

Da sauri ya amsheta daga jikin mahaifiyar tasu, cikin abin bai gaza 3 minute ba ta farfaɗo ta hanyar bata numfashinsa cikin ƙwarwarsu ta likitoci.

Sai kuma ya kalli Amina da dake kuka tamkar zata shiɗe.
Cikin sanyi Yah kalli Barrister da yayi gyaran murya tare da fara maimaita.
Allahummma gafirlahu warahamhu.
Da ƙarfi-ƙarfi cikin ikon Allah duk sai suka kama.
Shiru parlour ya ɗan nitsu.
Sai ajiyan zuciya da ake sauƙewa.
Dai-dai lokacin kuma Baba Malam ya shigo tare da bappa Lawan
Ahmad dake gefenshi yacewa.
“Ɗauko min ruwan sanyi”.
Yana sharce hawaye ya ɗauko masa gorunan ruwan sanyi.
Da kanshi ya bawa Fariyda da ta fara wani irin numfashi.
Amsa tayi tasha kurɓa uku. Amina ya bawa, sai kuma ya miƙawa Ummi.

Idonshi ya zuwa Mahmoud da bai amshi goran da yake miƙa masaba kuma baice masa komaiba illa addu'a da yaketayiwa ɗan uwansa.
Sunkuyar da kai Baba Malam yayi murya na rawa ido na zubda ƙwalla yace. “Kuyi haƙuri Mahmoud muyi haƙuri, Allah ya jiƙan Aminullah yasa mutuwa hutune a garesa.”
Dai-dai lokacin kuma Mama da Jidda suka shigo.
Suna shiga Jidda ta rungume Aunty Amina tare da fashewa da kuka. Da sauri Baba Malam ya miƙe ya kamo hannun Mahmoud tare da jawoshi suka fito. Bayan Goggo Dada ta amshi su Zaitoon.
A hankali Dr Nasir da Barrister da Ahmad suka mara masu baya.

Suna fita, Baba Malam ya ajiye shi kusa da Barrister, kana Ahmad da Nasir suka zauna gefenshi.
Cikin sanyi Baba Malam yace.
“Lawan muje ayiwa gawar sutura ko”.
Ido na zubda ƙwalla shina ya miƙe suka fita.

Bayan an gamawa gasar duk abinda ya dace kamar yadda shariya ta tsara.
Aka ajiye ta a wurin ajiyar gawa na cikin masallacin.
“Ko zamu kai gawar Mahaifiyarsa da matarsa su kalleshi”.
Bappa Lawan ya faɗa yana kallon time ƙarfe ɗaya da kwata.
Kai Baba Malam ya jujjuya tare da cewa.
“Kai gawar cikin gidan zai ƙara hargitsasu gashi maƙota da yan uwa sun cika gidan”.
Da sauri Malam liman ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Gaskiya kam zasu rikice”.
Sai kuma duk suka kalli cikin Masallacin jin man ladan ya kira sallan azahar.

A can cikin gida kuwa dai-dai lokacin.
Sulaiman da Salim suka shigo a tare.

Gaban Abba dake Al'wala Sulaiman ya dire guiwowinsa yana kuka tamkar mace.

Salim kuwa gaban Mahmoud ya wuce yana zuwa ya rungume shi da ƙarfi tare da fara jujjuya kai gami da faɗin.
“Mahmoud kayi? Mahmoud ka zubda ƙwalla”.
Amman ina kamar ma ba dashi yake yi ba, sai addu'ar da yake mai-mai tawa, kukan da Salim keyine ya sashi fara rawan jiki tare da fara mai-maita.
“Allaahum-maghfir lahu warhamhu, wa 'aafihi, wa'fu 'anhu, wa 'akrim nuzulahu, wa wassi' mudkhalahu, waghsilhu bilmaa'i waththalji walbaradi, wa naqqihi minal-khataayaa kamaa naqqaytath-thawbal-'abyadha minad-danasi, wa 'abdilhu daaran khayran min daarihi, wa 'ahlan khayran min 'ahlihi, wa zawjan khayran min zawjihi, wa 'adkhilhul-jannata, wa. 'a'ithhu min 'athaabil-qabri wa 'athaabin-naar.”.
Jin hakane yasa Salim fara bin bakinsa kana suka tashi domin yin al'wala.

Bayan anyi sallan azahar ne, aka sallaci gawar Aminullah da ya samu hallarta dubban al'ummar Annabi na birnin Kano da kewaye yan uwa da abokan arziƙi
Ƙarfe biyu dai-dai aka kaishi makwancinsa, kansa suka dawo zaman karɓan gaisuwa.
Duk da girma da fadin farfajiyar Saida ya nemi gazawa masu shigowa.

A ranar dai haka aka wuni zuciya cike da ƙuna.

Washe gari da safe
Salma ce zaune bisa kujerar table ɗin dake kitchen kuka takeyi har yanzu cikin sanyi ta kalli Miminta murya na rawa tace. “Mimi shekaran jiya uwar hakafa duk muna tare da Yah Amin, Mimi naji tsoron duniyar nan ba komai bace”.
Cikin rauni Mami tace.
“Salma yi haƙuri kizo ki tayani mu ƙarasa aikin nan in samu in tafi gidan gaisuwar nan.”
Tana mai share ƙwalla tace. “Mimi nima yau kam zanje”.
Ta juye kunun data dama cikin wani babban kula tace.
“Ki bari sai gobe kuje dan su Raihana ma basu jeba dan sune a gida”.
Tana kuka tace.
“To zan tafi wurinsu tunda Yau Aunty bazatajeba.”
Kai kawai ta gyaɗa mata.

A can gidan kuwa Raihana da Zainab da Humaira ce sukayi zuru-zuru dasu ba kowa a gidan sai su sune sukayi abinci mai yawa da masa da kunu suka bada Sadiq ya kai.

A anan gidan su Ummi kuwa.
Mahmoud dai har yanzu bai cewa kowa komai ba.
Koda gaisuwa aka zo masa da ido yake amsawa ko kai sai addu'o'in neman yafiya da gafarawa da yakeyiwa ɗan uwansa.

Fariyda zaune a ƙasa gaban Ummi da Mamy.
Shigowa Sulaiman ne yasata zuba masa ido tun jiya da suka iso basu shigo gidan ba sai yanzu.
Da suka shigo da manyan kulolin abincin da Abida matar Ahmad ta iso dasu.
suna haɗa ido da Sulaiman sai kawai ta kife kanta dan tuno sun da yake kiranta.
Ta Yah Amin mutukar raba.
Kuka mai sanyi Sulaiman ya fara.
Cikin rawan murya tace.
“Ayyah Sulaiman kaga mutuwar tayi gaggawar rabamu ko”.
Kai ya fara jujjuya mata tare da miƙewa ya fice.
Da sauri Salim ma yabi bayansa, ita kuwa lips ɗinta da suke kumbura sukayi jazir tsabar cizasu da takeyi Cizawan ta kuma yi da ƙarfi.

Yayarta Adda Nana dake gefentane tace.
“Kiyi haƙuri Fariyda in sha Allah Yah Amin yana cikin rahamar Ubangiji kiyi masa addu'a ki dena magana”. Aunty Saddiqa da itama jiya tazo daga Yola.
A hankali ta fara jujjuya kai tare da fara addu'a.
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَعَافِهِ، وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدْ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَما نَقَّيْتَ الثَّوْبُ الأَبْيَضَ مِنَ الدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَاراً خَيْراً مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلاً خَيْراً مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجاً خَيْراً مِنْ زَوْجِهِ، وَأَدْخِلْهُ الْجَنَّةَ، وَأَعِذْهُ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ وَعَذَابِ النَّارِ
Domin shi kadai take yi taji sanyi.

Washe gari da yamma ranar sadakan Uku.

Su Salma ne a durƙushe gaban Ummi sunayi mata gaisuwa sai kuma suka kalli Fariyda data zuba musu ido ba magna sai lips ɗinta da take motsa wa tare da jan carɓi.
Ina Salma kam da Zainab sun gaza danne kansu ganin yadda cikin kwana uku Fariyda ta zama tamkar ba itaba saboda ƙuncin zuciya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.