Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 41 of 86

Washe gari da safe Abba ne zaune a parlour, Mahmoud na gefen damansa Ummi da Goggo Dada na gabansu.
Hafiz kuwa na can gefe kan 3 seatter su Zaid nata yawo a tsakiyarsu wanda tunda suka dawo Goggo Dada keyi musu komai suna nan fes dasu sai ƙamshi sukeyi cikin shigarsu Pink collar.
Abba yace.
“Kunyi magna da Ahmad ko Mahmoud?”.
Yana ɗan Sipping tea ɗin ya gyaɗa masa kai ya gyara zama tare da ajiye cup ɗin yace.
“Eh munyi magna, yamin bayanin suna buƙatar kayayyaki gadaje, kujeru, tv stand, Dinnin tables da dai sauransu”.
Abba da ya zuba masa ido jiran ya kai ƙarshen mgnar ne yace.
“To kai zakajene ko a online zakayi komai”.
Mahmoud yace.
“A'a zanje Italy don Sulaiman ma yace suna buƙatar kaya.
Kuma muma nan stores ɗinmu sunyi ƙasa sosai”.
Goggo Dada tace.
“Ai dai kam zuwan zai fi, dan zuwa da kai yafi saƙo”.
Ummi tace.
“Allah ya bada sa'a ya taimaka”.
Amin sukace tare da zuba mata ido jin abinda take cewa ne yasa Mahmoud zaro ido tare da gumtse tea ɗin dake bakinsa.
“Hakama yayi sai ka shirya tafiyar da matark.....

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 16
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Wani irin tarine mai ƙarfi ya sarƙafe mishi wuya saboda kwarewar da yayi da tea ɗin dake bakinsa Goggo Dada tace.
“Subahanallah sannu”.
Abba kuwa Ummi data zuba mishi ido ne ya zubawa ido in seconds sai kuma ya maida ganinsa kan Mahmoud da har yanzu yake tarin.
“Sannu”.
Yace tare da sa hannunsa yana ɗan shafa bayansa.
Murmushi mai tafe da kwaffa Ummi tayi ta miƙewa ta bar warin.
Ajiya zuciya mai nauyi ya sauƙe gami da bagarar da magnar da baya mararin sake jinta a rayuwarsa ya kalli Hafiz yace.
“Kaima ka kusa barin wannan jarabar ɗauke-ɗauken hoton zan fara fita da kai, dan kasan komai zaka taimaka mana wurin samun sauƙin aiki kana gama karatun ka zaka dawo business”.
Da sauri yace.
“To Uncle ai ko yanzuma a shirye nake muje ko ina, amman dai ayi haƙuri a barni in tafi da Camera ta”.
Kamo Zaitoon da ta iso gabansa yayi da cewa.
“Fasata ma zanyi, dan so nake ka zama na miji ka daina lauyewa kana abu kamar mace”.
Shiru Hafiz yayi dan yasa in yana mgnar zai iya fasa Camerar a yau ɗin nan ma.
A can kitchen kuwa Maman Samira ne da Fariyda suke haɗa breakfast ɗin.
Wuraren sha ɗaya na safe. Kwance take kan 3 seatter dakin Goggo Dada Game take yi a wayarta wanda shine ya hanata yin bacci da take taji kafin tayi wanka.
Da sauri ta miƙe jin kaman muryar Amina.
Kofar fita ta nufa, sai kuma tayi sauri dafe ƙofar tare da kallon Hafiza data rungumeta cikin farin ciki tace.
“I miss u so much my Aunty”.
Murmushin tayi.
“Miss u too Hafiza”.
Ƙarasowa cikin parlour tayi tana kallon Amina kan kujerar dake bayanta ta zauna tace.
"Sai yau aka tunamu”.
Amina na jawo Zaitoon dake zirga-zirga a gabanta tace.
“Ai wai barinku nayi ku huta gajiyar biki kafin inzo”.
Fuska ta tsuke tayi kamar bata jitaba ta kalli Ummi dake cewa.
“Bakiyi baccin bane?”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Eh naga lokacin ɗaura lunch ma ya kusa”.
Da sauri Hafiza tace.
“Kalli My Aunty Mom ta hutar dake shiga kitchen yau”.
Ta ƙare maganar tana nuna mata wormas ɗin dake kan Dinnin table.
“Ai kuwa mun gode. Samira kicewa Mamanki ma ta huta”.
Sai kuma duk suka kalli Amina dake cewa.
“Ikon Allah ashe tafiya kam ta nuna”.
Tayi magnar tana kallon Zaid dake tahowa wurin Fariyda tare da fara miƙa mata hannun alamun so yake ta ɗaukeshi, cikin yanayin farin ciki daya dawo musu Goggo Dada tace. “Ai saura mu fara batun yayaye ne ya rage”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Alhamdulillah ai munji daɗi, har Mahmoud ranan saida ya kai min su wai inga tafiyarsu in yaga suna tafiya daɗi har murmushi yakeyi”.
Taɓe baki Fariyda tayi tare da tsuke fuska aranta take faɗin ko taya suke gane yana murmushi.
Sai kuma ta ɗan sunkuyo ta kalli Zaid dake jan tattausar Abayar jikinta.
“Ɗaukeshi mana Fariyda wata kil bacci zai yi”.
Hannu ɗaya tasa tare da kamo shi da nufin ɗagashi da sauri ta janye hannun tace.
“Kai Zaid kayi lukuti hannun nan kam bazai iya ɗagaka ba”.
Cikin kulawa Ummi tace.
“Fariyda ko dai hannun nan bai gama warkewa bane, naga ɗaga yaran dashi yana ɗan baki wuya”.
Kai ta jujjuya tace.
“A'a Ummi ya warke ba zafin komai kawai dai hannun ne ba ƙarfi”.
Goggo Dada tace.
“Ai sai a hankali zai zama dai-dai”. Amina tace.
“Afwan Fariyda am naso inzo dubaki da hannun da Hafiz ya gaya min to kuma nima lokacin zazzaɓi ya ɗan sani gaba”.
Tana kallon Hafiz dake ce mata.
“Aunty Fariyda albishir”.
Goro tace tana maida hankalinta kansa tana kuma cewa Amina.
“Alhamdulillah hannun da sauƙi, ya naki jikin”.
Ido suka zuba wa Hafiz dake cewa.
Oum Zaitoon albishir fa nace Miki amman baki kulaba".
Hankalinta ta maida gareshi da cewa.
"To goro fari ƙal”.
Da sauri yace.
“To zakije Italy”.
Tana ɗan shafa kan Zaid dake kan cinyarta yana lumshe ido alamun bacci zai yi tace.
“Italy kuma”.
Kai ta gyaɗa mata ba tare da ta kula da kallon da Goggo Dada take maiba yace.
“Eh Italy dai”.
Tana tsareshi da ido tace. “Yaushe kuma ni da waye”. Cikin murmushi yace. “Wata ƙil nan da sati biyu, ke da Uncle Mahmoud mana zaije sari shine Ummi tace dake zai tafi”.
Wani irin yanayin mai cike da damuwa, tashin hankali ne suka bayyana kan fuskarta tuni idonta ya sauya launi sun fara shegin hawaye tayi ƙasa da kanta tana jujjuya kai alamun a'a bazata jeba.
Da sauri Amina ta ɗakawa Hafiz ɗin duka a baya tare da cewa.
“Dan Allah yanzu waya tambayeka, kai dai a dole ka zama faɗi ba'a tambayeka ba”.
Goggo Dada ce tayi saurin cewa.
“Yoh mgnar Hafiz ai ji kawai zakiyi Fariyda amman yarda ba dole ba”.
Ummi dake ta dalla mishi hararane tace.
“Ai ni nan gaba in ina wuri ya zauna korarsa zanyi, nima cewa nai da an yaye su Zaitoon ne zasu tafi tare”.
Ajiya zuciya mai ƙarfi ta sauƙe murya a sanyaye tace.
“Ni kam ko an yayesu ma bana son zuwa ko ina, in zauna daku yafi min daɗi Ummi”.
Murmushi Goggo Dada tayi tace.
“To ai shike anan ba inda zakije”.
Dai-dai lokacin kuma Zaitoon ta juya ta nufi bakin ƙofar parlour da ɗan saurinta tanayi tana dariya tare da ɗaga hannunta saboda hango Salim da Mahmoud da suka shigo tare, cikin kulawa Salim yace.
“Yess my baby girl tafiya fa ta nuna”.
Gyara zama Fariyda tayi ganin Zaid ya zame jikinsa ya sauƙa da ɗan gudunsa ya nufi inda suke saboda jin muryar Mahmoud ɗin dake cewa.
“Zaid”.
Ido Salim ya zuba mishi ganin sun wuceshi da gudu, ɗan rage tsawo Mahmoud ɗin yayi tare da ware masu hannunsa a tare suka abka jikinsa.
“Wai har yanzu suna ƙiuya ne”.
Salim ya tambaya yana zama kusa da Ummi Hafiz yace.
“A'a basa ƙiuya, kawai dai in sunga Mahmoud ne basa zuwa gun kowa sai shi”. Goggo Dada ta faɗa
Hafiza ce tai kwaffa tare da cewa.
"Allah ko Mom Hafiz bazai taba sauyawa ba”.
Harara ya watsa mata tare da kai hannu zai dake ta da sauri Amina tace.
“Bana so ya kana namiji zaka dakar min ƴa”.
Sai kuma ta juyo ta kalli Mahmoud daya wuce dannin area dasu.
Kujera yaja ya zauna ya ɗaurasu kan table ɗin suna fuskantar juna.
“Fariyda je ki sa mishi abinci”.
Amina ta faɗa tana kallon Salim dake gaidasu Ummi.
Yi tayi kamar bata jita ba sai cewa tayi.
"Ya zazzaɓin naki?”.
Tana miƙewa tsaye tace.
“Alhamdulillah Fariyda am”.
Tana ɗan kallon ta tace.
“Wai yau naji ba auti sai Fariyda Fariyda ina karar taki ta tafi ne”.
Kallon Fariyda tayi cikin kiyasta shekarunta tace.
“Ai Aunty kam kuma ya wuce ki, tunda yanzu dai ke matar ƙani ce ba kamar da da kike matar yayaba”.
Ta ƙare maganar tare da kallon Salim dake cewa Fariyda.
“Oum Zaid ya hannun”.
Ba yabo ba fallasa tace.
“Da sauƙi”.
Da sauri Hafiza tace.
“Wai Aunty Fariyda faɗuwa kikayi ne hannun ya targaɗe?”.
Kai ta jujjuya alamar a'a.
Ummi tace.
“Mu ma har yau mamakin abinda ya targaɗa mata hannun na muke tace ba faɗuwa tayi bacci tayi ta farka da hannun a gurɗe”.
Ido Amina da ta isa gaban Mahmoud ta zuba mishi tana tuno kalmar da ya faɗa mata ranar da aka dawo da Fariyda washe gari da yaje yana mata masifa.
“Bayan targaɗata sai na kakkaryata na watsa a dozbin”.
Cikin yin ƙasa da murya yadda shi kaɗai za jita tace.
“Kai ka targaɗata ko?”.
Fuska ya tsuke tare da hararan cikin parlour yace.
“Ko zaki rama mata”. Yayi mgnar tare da miƙa mata hannunsa, kai ta jujjuya tace.
“Na isa Oga Yah Mahmoud”.
Sai kuma ta juyo cikin parlour tace.
“Bimillah Salim iso kuyi breakfast”.
Da sauri ya miƙe yana cewa.
“Dama kuwa da nufin cin abincin Mahmoud nazo shiyasa ma ban tsaya naci na Mama ba, dan yau girkin Ummi zanci”.
Tana jamai kujerar zama tace.
“Yau kam nawa nema, dan dama na gayawa Ummi karsu masa komai zan kawo mishi”.
Chips ta zuba musu tare da sa musu pepper meat ɗin jijiya da ɗan jan nama da yayi lugun da ɗan yaji sai isashhiyar albasa , tea ta haɗa musu Salim cup ɗaya shi kuwa cup biyu.
tsai kuma ta buɗe ɗaya kular doya ne da kwai.
“Ga wannan in zaku ƙara”.
Ta faɗa tare da maida marfin ta rufe, ta dawo cikin parlour.
Ganin Fariyda ta miƙe ta nufi bedroom ɗin Goggo Dada ne yasa.
Ita ma tabi bayan Ummi suka shiga ɗakinta gefen Ummin ta zauna kana a hankali tace.
“Ummi har yanzu Fariyda a ɗakin Goggo Dada take ne?”.
Cikin sauƙe numfashi tace. “Eh”. Amina tace.
“To Ummi ai da sun koma part ɗin Yah Amin ɗin tunda Abba yasa an gyara komai”.
Tana ɗan juya kai tace.
“Ai shi kanshi Abbanku yayiwa Mahmoud mgnar ya koma part ɗinsu Aminullah ɗin tun bai san za'a aura masa Fariyda ba, yace wlh shi bazai iya ba a barshi inda yake. To kuma itama Fariyda da Goggo Dada ta gwada ce mata ta koma can kuka tai tayi tace baza iyaba”.
A sanyaye tace.
“To Ummi su koma part ɗin Mahmoud ɗin mana tunda komai nasa irin na Yah Amin ɗin ne, sai a zuba musu komai na buƙata”.
Kai ta ɗan kawar dan kar Amina taga hawayenta tace.
“Ai yace shi in da yake ɗin nan saman nan ya ishesa ba inda zai koma”.
Tana mai fesar da numfashi tace.
“To ai sai a maida Fariyda ma sama wurinsa tunda 2 bedroom ne harda ƙarin ɗan madaidaicin na uku duk da ya kashe ɗaya ya medashi wurin motsa jikinsa Amman ai ɗaya inda Fahiz yake kwana ko Sulaiman in yazo da Salim ma in yazo ai ɗakin ras yake.
In yaso shi Hafiz sai ya koma ƙasan part ɗin Yah Amin ɗin ko Sulaiman ma in ya dawo sai ya sauƙa a nan.
Cikin gamsuwa da shawarar ta tace.
“In sha Allah zan gayawa Abbanku”.
Tana miƙewa tsaye tace.
“Ta haka ne kawai zasu san eh fa lallai su ma'auratane, ba abokan gaba ba, dan na lura ko magna basa yiwa juna”.
Ɗan tsaki Ummi taja tare da cewa.
“Shi ƙanin naki uban taurin kai ko kallonta ma yanayi ne, itama ko ta kanshi bata bi, na lura ta saki ranta ne ganin ba wani haɗata dashi a kan komai zaman sukeyi kamar da da Aminullah ke raye, kai gwarama da ɗin suna faɗa yanzu ko ba mai cewa ɗan uwansa ko ƙala”.
Kai ta kaɗa tare da cewa.
“Ai a maidata sama kawai a ƙaƙaɓa mishi ita ta nan ne zasuyi su gama gabar suyi faɗa har su shirya in Allah ya nufa duk da ni dai nasan hakan da wuya.” cikin sanyi Ummi tace. “Ni kaina na gamsu lamarinsu ba sauƙi a ciki, shiyasa kawai nake addu'a in al'khairi Allah ya daitata in ba alkhairi bane Allah ya kawo mafita”.
Daga nan ta fita.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.