Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 84 of 86
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAR MAKAFI*
Page 43
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Riƙe numfashinsa da kansa da yake wani irin sarawar da ya hanshi buɗe idonsa bare ya iya wani abu sai nannauyan baccin da baiyi na tsawon kwanaki huɗun ne ya danneshi.
A hankali take murza tafi hannunta kan tattausar fatar bayansa, kanta ta kuma ƙara mannawa kan faffaɗan ƙirjinsa tana shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikinsa, cikin baccin da ya ɗan fara saketa ta fara mutsu-mutsun tashi jin tamkar an ɗaureta a jikinsa ne yasata ɗan buɗe kyawawan idanunta da suka sauya launi na musanman mai cike da bayyana sirrin cika lfyar ta.
Kai ta juya daga gefen daman ƙirjinsa zuwa hagu tare da jawo hannunta ɗaya ta dawo dashi kan ƙirjinsa dai-dai kan nimple ɗin data ciccije ranar da yayi mata gyaran targaɗe ta dire hannun ta fara ɗan jujjuya hannun da ɗan bubbugawa kaɗan-kaɗan saboda har lau jikinta ba kuzari. Sassayan cikin fesar da sassayan numfashi mai cike da rogowar baccin da har yanzu bai ishesa ba ya ɗan fara motsa idonsa, sai kuma ya ɗan juya kai daga dama zuwa hagu, a hankali ya buɗe kwayar idanunsa da har yanzu basu gama washewa ba, saima jirkiɗewa da sukayi suka bada wani launi na musanman mai zafi, numfashi yaja ya sauƙewa da sauri saboda ganin inda yake cikin bedroom kuma akan gado, kanshi ya ɗago ya kalli jikinsa inda yake ɗan kishin ƙiɗi da kan gadon yayinda sawunsa ke miƙe, sai kuma yayi saurin kallon kan ƙirjinsa, a hankali yasa hannunsa ya yaye Duvet ɗin.
“Dib! Dub. Shine sautin da zuciyarsa ya bada, da sauri yasa yatsunsa biyu, zip ɗin rigar tasa ya fara zugewa da sauri.
Lip kanta ke manne bisa ƙirjinsa sai gashinta daya zubo kan fuskarta da ƙirjinsa sai ɗan lip ɗinta na sama da take tsotsa ta ciki ta turo na ƙasan like jaririya. Ido ya zuba mata kamar yadda ta zuba mishi, sai kuma tayi saurin miƙewa zaune saboda jin yadda ya hankaɗata gefe tare da watsa mata wani irin kallo jiki a narke ta miƙe ta dira daga kan gadon.
Hmmmmmm ta sauƙe numfashi mai ƙarfi tana sa hannunta kan mararta da taji kaso 80/100 na ciwon ya tafi.
Wuyan rigarta ta fara gyarawa tana tattare gashin kanta ta fara naɗeshi ba tare da ta ƙara kallon ta ida yake ba.
Shi kuwa Mahmoud cikin baƙin cinkin ganin haske alamun tuni gari ya wayene ya sashi wucewa bathroom Yana mai faɗin.
“Innalillahi, Astagfirullahâ€. Ya rinÆ™a mai-maitawa har ya shiga bathroom É—in saboda ganin irin makarar da yayi har lokacin salla ya tsere masa da awa É—a cib uwa uba yanayin da ya kwana.
Gaban mirror dake bathroom ya tsaya cikin tsananin kaɗuwa da nazari ya zazzaro manyan idanunsa baki ɗaya ya zuba su kan fatar jikinsa yana tuna a yadda yayi bacci abinda yayi masifar kiɗi mashi da hautsuna tunaninsa, sai kuma ya fara shafa duk fatar jikinsa dan neman abinda ke faruwa dashi muddin fatar wani ya taɓashi shafawa yayi tare da kwaɓe fuska ganin ba komai ba ƙaiƙayi ba ƙuraje, cikin tsananin ƙuncin zuciya ya yi alwala, ba tare da ya tsaya wanka ba dan ganin lokacin salla zai tsere masa, yana fita parlour ya wuce ya shimfida sallaya ya kabbarta sallah.
Yana fita, Fariyda ta buÉ—e idanunta da tunda ta tashi zaune bata buÉ—esu ba sai da taji fitarsa, bathroom É—in ta shiga dan yin alwala.
Bayan ta idar da sallane ta manna kanta jikin gado ta fara shafa mararta dan tuno irin azabar da ta sha daren jiya, flacks ɗin dake gefenta ta jawo sabida tuna tana sha jiya ta fara samun sauƙin suka da murɗa da marta keyi sai kuma sanyin daya gigitata.
Fiye da rabin cup É—in tasa ta fara Sipping tea É—in a hankali, ido ta lumshe saboda jin tsami da É—anÉ—anon lemon ya fito yaji meÉ—eu cikin shayin.
A hankali ta miƙe tsaye bayan ta shanye.
Bathroom ta wuce, wanka tayi tare da kimtsawa cikin tattausar Turkish pallazo da yar top mai guntun hannun red color mai ratsin fari, robar wondon ta É—auran kan rigar kasancewarsa mai fadi sai ya zama kamar belt ta saka hula bayan ta gyara gashinta.
Turarukan da Sa'ad ya bata jiya ta jawo ta fara fesasu ɗaya bayan ɗaya. Numfashi mai sanyi ta shaƙa tana ci gaba da fesarwa saboda ni'imar ƙamshin har lumshe ido tayi.
Gefen gadon da su Zaitoon ta nufa cikin mamkin yau har yanzu basu farkaba, labulayen dake zage da gadon nasu ta yaye, ido ta zuba musu ganin har lau bacci sukeyi kamar yanzu dare yayi.
Bakin gadon ta dawo ta zauna.
Mahmoud kuwa tunda ya idar da salla yayi Azkarul Sabah, har yanzu a tsaye yake a tsakiyar parlour tamkar an dashi, sai idonsa da yake rumtsewa ya kuma buɗewa cikin hautsunewar halittun jiki da cushewar tunani na tarin baƙin cikin inda bacci ya ɗaukeshi a jikin wannan abar in ya tuno matar Yah Amin ne sai kuma yayi ta istigfari dan gani yake tamkar saɓo yayi.
A hankali ta shigo parlour ta nufi fridge.
Cikin yanayi na ƙuncin zuciya ya shiga bedroom ɗin meda ƙofar yayi ya rufe, ya wuce bathroom, fushin nasa ƙara dukan ƙirjinsa yake a duk sauƙan da ruwa yake yi a jikinsa a haka dai yayi wanka.
Yana fitowa parlour ta koma ciki.
Kimtsawa yayi cikin jallabiya Black blue mai ƙyalli.
Kan kujerar baccinsa ya zauna ya kunna TV ya fara kallon Wrestling.
Ita kuwa Fariyda tana shiga ta samu su Zaid sun farka wanka tayi musu ta shiryasu ta fesa musu biyu daga cikin turarukan da Sa'ad ya saya musu.
Miƙewa tayi tare da sasu a gaba dan tafiya dasu Dinnin area dan suyi breakfast a kuma samu a share musu ɗakin.
Suna fitowa parlour da gudu Zaitoon ta nufi wurin Mahmoud É—in tana gwarancin kiransa Appiy! Appiy cikin É—an sauri-sauri kaÉ—an Zaid ma ya mara mata baya, yana faÉ—in Appey da mgnarsa da tafi ta Zaitoon fita sosai.
Hannun ya buÉ—e musu gami da É—an sunkuyowa, a tare ya rungumesu kana ya koma ya zauna dasu, sumbatar goshinsu yayi yans kallon Zaid yace.
" Hello my Son ya jikin da sauÆ™i ko?â€. ÆŠan guntun sakin fuskarsa yayi saboda murmushin da Zaid yayi.
“Alhamdulillah jiki da sauÆ™i koâ€. Ya kuma faÉ—a cikin jin sanyi zuciyarsa da ganin yaran ya sakar masa jin daÉ—i.
Gefen da suke ta matso ta miƙawa su Zaid ɗin hannu tace.
“Kuzo muje kuyi breakfastâ€. Suna Æ™ara maÆ™alÆ™ale wuyansa ya É—an kauda kansa daga ta inda take cikin tsanar ganinta a harzuÆ™e yake mgna cikin bada umarni yace.
“Ke kada ki sake fesa wannan turaren bokayen, dan zai sama yarana mura, suma kada ki sake fesa musu wannan bana so, in abunsu ya Æ™arene ki gaya min, basu rasa komaiba basa buÆ™atar taimakon waniâ€. Cikin tura baki tace.
“Wannan É—in ne turaren bakoye lallai ma kam, ni dai ina son abuna, in ma su baza'a saka musu ba, ni dai kam zan sa nawaâ€.
Yana sauƙe su Zaid ɗin yace.
“Okay kisa É—in ki ganiâ€. Kamo hannunsu tayi ta juyawa ta fita dasu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.