Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 81 of 86

Shafa kanshi yaci gaba dayi a hankali yana mai lumshe idanunsa da bacci ya fara birkita musu launi, saboda rashin baccin daran jiya ga wanin yau É—in duka baiyi bacci ba.
Da sauri ya ɗago kansa daya jingina akan gadon, saboda jin kukan Zaitoon, ɗagata yayi cak ya ɗaurata kan ƙirjinsa da ɗan bubbuga amman ina sai mutsu-mutsun takeyi.
Cikin baccin daya fara saceta, taji ya ajiye mata Zaitoon kan bayanta haka yasa tayi saurin juyowa, ɗan tsaki taja tare da rungumeta, ta fara ɗan jijjigata saboda kukan da take yi. inda yake ya dawo ya zauna ya ɗauki wayarsa ƙarfe ɗaya harda kwata , gyara zama yayi kawai ya fara karatun Alqur'ani mai girma.
Ɗan gajeren tsaki Fariyda taja, lokacin da ta farka saboda ɗan motsin Nurses da suka shigo ƙarfe biyu dai-dai dan yiwa Zaid ɗin allurarsa da kuma sa masa wani ruwan.
Numfashi ta fesar lokacin da suka fita, ta miƙe zaune ido ta ɗan zuba mishi yana zaune kas a wurin da alamu ko tashi bayayi ba idonsa kab na kan Zaid ɗin da yake ta subaɗun balonkwacensa da dariya-dariya murmushi-murmushi baki ta taɓe ganin yana tayiwa Zaid ɗin tofi hankali tace.
“Yau dai kam bazanyi bacci kenan”. Ko ta inda take bai kalla ba, haka kuwa daren ranar ma suka kwana ba bacci kamar jiyan gwara ita tana ɗan yi kaɗan kaɗan.

Bayan anyi sallan asuba daga Masallaci masauƙinsu ya wuce, yayi wanka ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wonɗo milk color masu taushin gaske.
Numfashi mai cike da gajiya ya fesar tare da jan ƙofar ya kulle lokacin da ya fito, wayarsa dake Vibrating ya zaro ganin Yah Ahmad ne yasashi amsawa daci gaba da tafiya.
"Alhamdulillah Yah Ahmad jiki da sauƙi sosai”.
Dinnin area É—in hotel É—in ya nufa, breakfast yayi Sannan ya tafi asbitin.

Ƙarfe tara dai-dai ya iso asbitin. Yana shiga Fariyda ta miƙe ta ɗauki Zaitoon suka fita, dan zuwa suyi wanka su kuma yi breakfast.
Fitansu ba jimawa Dr Imran Patel ɗin ya shigo tare da rakiyar Nurses guda uku, ɗaya daga cikinsu riƙe da wani ɗan tray mai ɗan karen kyau da ɗam bowl na yara da marfinsa sai spoon ɗin dake naɗe cikin tissue sai kuma ɗan ƙaramin tea battle shima da marfi.
Murmushi Dr Imran din yayi ya miƙawa Mahmoud ɗin dake riƙe da Zaid ɗin hannu duka gaisa ya kuma miƙawa Zaid ɗin alamun yazo. Maƙe kafaɗa Zaid ɗin yayi tare da manna kansa bisa ƙirjin Mahmoud ɗin, murmushi Nurses ɗin sukayi shi kuwa Dr Imran sunkuyowa yayi ya ɗauki baloon da ɗan ƙaramin ball ya miƙa masa a hankali ya miƙo hannunsa dan karɓa ɗagashi yayi cak, kan gadon ya zaunar dashi tare da sakeshi yana kallon Mahmoud dake tambayan zai iya zama ne.
Kai ya jinnina masa alamar eh, amsar tea battle ɗin yayi ya bashi da sauri ya buɗe mishi baki, murmushi sukayi ganin yadda yake zuƙan tea ɗin da ba madara a ciki.
Fes ya shanye iya ɗan tea ɗin da dama dai-dai wanda suke buƙatar yasha aka saka, sai kuma ya fara gyatsa.
“Alhamdulillah”. Shine Abinda Dr yace tare da yiwa Mahmoud bayanin aikifa yayi kyau, sai kuma ya bashi Tray yace bayan awa ɗaya a bashi Custard ɗin dake cikin bowl ɗin da yake da ɗan riƙe zafi.
Daga nan sukayi masa duk dube-duben da zasuyi masa.
Suna fita kiran Mamy na shiga wayarsa ganin ba sunane yasa ya zuba wa wayar ido, to waye kuma ya faɗa a ransa, ganin kiran ya katsene ya maida idonsa kan Zaid da yake miƙo masa hannun da sauri ya ɗaukesa tare da ajiyesa kan cinyarsa bayansa manne da ƙirjinsa.
Shigowar kiran a karo na uku ne yasashi É—agawa.
“Assalamu alaikum Mahmoud Mamy ke magna”. Cikin girmamawa yace.
"Afwan Mamy ina tare da Zaid ne shiyasa ban ɗaukaba, Barka da rana Mamy ya gida”. Cikin jin dadin yadda yayi mata magna a mutunce tace.
"Lfy lau Mahmoud ya jikin ɗan naku, yanzu mukayi waya da Fariyda tace ita tana gida kai ke tare da shi”. Cike da kamala yace. “Alhamdulillah jiki da sauƙi sosai Mamy, ɗazu ma munyi waya da Baba Malam ai”. Mamy tace.
"Allah ya ƙara sauƙi ga Nana”. To yace kana suka gaisa da Adda Nana ta tambayi ya jikin.
Numfashi ya sauƙe bayan yayi sallama dasu.
Daga jiya zuwa yau har ya gaji da amsa kira.

Ƙarfe biyu dai-dai Fariyda ta shigo Zaitoon na gaba tana baya.
Ganin Dr Zara na cikene yasa ta ɗan matso bakin gadon da mmki take kallon Zaid da Dr Zara ta tsaidashi tana musu bayanin, zuwa dare su riƙe hannunsa yayi tattaki.
Murmushin da yake mata ne yasa ta shafa kansa.
Mumbai cikin takaici Sa'ad ya shiga ɗakinsa tare da fara kiran Mahmoud babu ƙaƙƙautawa, hakan ne yasa Mahmoud da yake bawa Zaid Custard ɗin da yaƙi sha ɗazu sai yanzu ɗaukar wayar.
“Afwan Yah Mahmoud na dame ka, ko wlh nayi missing flight ne duk raina ya ɓaci hankali na ya tashi, shiyasa nace bari in faɗa maka kada kujini shiru, sai gobe Sunday in sha Allah uku dai-dai zamu sauƙa Ahmedabad.“
A taƙaice yace.
"Okay Allah ya kaimu, sai kazo”. Daga haka ya katse kiran yaci gaba da bawa Zaid Custard ɗin.
Daren ranar ma dai haka suka sake kwanan zaune ba bacci saboda rigimar Zaid da Zaitoon wanda kwana biyu basu sake sunyi wasaba.
Sai kusan ƙarfe huɗu sukayi bacci.
Al'wala yayi ya tafi masallaci daga nan ya wuce masauƙinsu, Saida ya dawo Fariyda ta tafi, sai uku dai-dai ta shogo ɗakin.
A hankali ya sake jan dogon numfashi tare da shaƙan ƙamshin turaren da ta shigo da shiɗin, numfashi ya fesar yana ƙara jan numfashi na biyu, wanda tun ana forkon ya gane turarensa ta fesa tabbas wannan ƙamshin turarensa.

Cikin yanayin gajiyar asbiti da rashin isasshen bacci ta iso gaban gadon inda yake zaune yana ɗan riƙe hannun Zaid yana tattakawa a hankali, gami da sake hannunsa yana ɗan tafiya shi kaɗai.
“Waya baki izinin taɓa min box na?”. Da sauri ta kalleshi sai kuma ta cire kai ganin kamar ba shi yayi magnar ba.
“Waya baki damar taɓa min kayana”. Tana gyara mayafin tattausar Abayar ta mai ɗan karen sulɓi coffee color da tayi Rollin kanta dashi tace.
"Ni ko kallon kayanka banyi ba toma me zanyi da taɓa kayanka?”. Cikin kafeta da ido yace. “Satan turare mana! In ba satar ba da fitsara me kika iya”. Cikin ƙarfin hali tace. "Da yake kai kaɗai ne mai turare ai dole kace na fesa ma naka”. Murya a kausashe yace. “Ƙarya kikeyi, turarena kika fesa, ke in banda sakarci waya ce miki ana satan turare, nace waya baki izinin taɓa min kaya da fesa min turare”. Cikin yin ƙasa da kai da murya tace. "To ai nawa ya ƙarene shiyasa”.
Cikin tsuƙe fuska yace.
"In ance miki jahannama na jiran irinki kiyiwa mutane rashin kunya, a ina aka halatta miki baza irin wannan ƙamshin ki fita dashi waje, ki sani yau sai kiyi wankan janaba kafin kiyi salla dan ke hanyarki ɗaya da mazinata”. Cikin wani irin kallon mai tafe da takaici ya kalli wayarsa saboda kiran Sa'ad daya shigo amsa kiran yayi.
Ita kuwa Fariyda zama tayi bisa 3 seatter tana tura baki.
Location ɗin Asbitin da room number da suke duk ya tarkata ya turawa Sa'ad da tuni sun sauƙa a Ahmedabad ba.
Kiran sallan la'asar da akayi ne yasashi barin É—akin. Ana idar da sallan ya dawo ciki.
Tana kan sallayan kauda kai yayi yana faÉ—in.
“Ki shirya Sa'ad yazo”. Tana kallonsa tace. "Yana ina?”. Ba tare da ya kalleta ba yace. “Ban sani ba”. Ƙofar ɗakin ya nufa jin ana Knocking buɗewa yayi tare da ɗan ja da baya.
Sa'ad ne da rakiyar wata nurses da alamun ita ta nuna masa É—akin da suke É—in.
Flowers É—in dake hannunsa ya zubawa ido sai kuma yace.
“One minute”. Daga nan ya maida ƙofar ya rufe.
"Gashi ya iso”. Gyara mayafinta ta farayi tare da cewa. "To me zan ce masa”. Wani irin kallon da yayi matane yasa tayi ƙasa da kanta.
Cikin sanyi ta kuma cewa. “Ni ban san me zance masa ba, ina tsoron Allah”. Cikin tsura mata ido yace.
“Okay nine bana tsoron Allah kenan?”. Da sauri ta jujjuya kanta a hankali tace. “In ni nayi magna dashi ai zunubi za'a rubuta min”. Numfashi ya ɗan fesar a hankali yace. “Kada ki damu ai ni na baki izini”.
Tana ɗan gyara mayafin jikinta tace. “To zaka bani key mu tafi ne”.
Fuska ya tsuke ciken daƙile murya yace.
"Dan kin samu kina shiga inda nake ne kike tunanin ko wani Tom and Jerry ɗin ke shiga min wurin zamana ne.” tace.
"To a ina zamu zauna”. Yana shafa kan Zaid da Zaitoon yace.
"In kunga dama ku hau sam kwano ku zauna, ko ku nemi wuta ku shiga ciki ku zauna, wannan matsalarku ce. Ni zan tafi in kinga dama ki shigo dashi in kinga dama ki barshi a tsaye har tsayuwarsa ta ƙare, turarena kuma da kika fesa zanyi mgninki”.
Daga haka ya juya ya fita.
Cikin sauri Sa'ad É—in ya bashi hannun tare da sakin fuska yace.
“Barka da yamma babban Yaya ya jikin Zaid”. Yana janye hannunsa yace.
“Barka da zuwa ka isa tana ciki, ni zan ɗanje pharmacy”. Cikin zumuɗi yace to kana ya kutsa kai ciki.
Shi kuwa Mahmoud yayi tafirsa.
A parlour ya zauna tare da miƙe sawunsa kan Centre table.
Wayarsa dake ta Vibrating tun yana hanya ya zaro, Salim ne a kufule yace.
"Wannan kiran mafarautan duk na menene?”. Dariya Salim yayi tare da cewa. "Abu da yawa ne, na farko dai nasan Sulaiman ya gaya maka ansa ranar bikinmu nanda mako biyu”. A gajiye yace. “Allah ya nuna mana lokacin, number 2 fa, dan bacci nake son yi, yau kwana biyu banyi bacci ba”. Cikin dariyar keta Salim yace.
“Yau naje Abuja kawai ina sauƙa Airport sai ga Idaya”. Da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafe ƙahon zuciyarsa da ta fara bugawa da sauri-sauri a hankali lokaci ɗaya yaji jikinsa kamar ƙaiƙayi yake masa haka yasa yace.
“Innalillahi sai akayi ya”. Salim yace. “Wlh fasa tafiyarta tayi, dama wai Lagos zata wuce, tana ganina ta rinƙa bina har saida muka zo masauƙina tare da drivernta”. Da ƙarfi ya rumtse idanunsa kana ya buɗe. Salim yaci gaba da cewa. "Wlhi ta bani tausayi dole yasa na bata phone number ɗinka da address ɗin gida, nadai ce mata kana Ahmedabad”. Cikin tashin hankali yace.
“ Innalillahi Salim Idaya ka bawa digit ɗina harda ƙarin Address ɗinmu”. Yadda yayi mgnar ne yasa Salim yin shiru.
Shi kuwa Mahmoud kai ya jijjiga cikin tarin baƙin ciki ya katse kiran, yana ajiye wayar kiran idaya na shigowa da sauri yayi blocking ɗin ta.
A can asbitin cikin mutunta kai da kiyaye haƙƙin igiyar auren dake kanta da gudun saɓawa Allah Fariyda ta gyara zamanta tare da gyara rufe jikinta duka, cikin nitsuwa ta kalli Sa'ad da ya karɓi wayarsa da ya bata sukayi magna da Mom ɗinsa.
Shafa kan Zaitoon yayi tare da sumbatar goshinta cikin tsananin son yarinyar yace.
"Wannan daga gani yaran Big broz ne ko?”. Kai ta girgiza masa alamar a'a. Yana ƙara kallonsu yace
"Ba yaransa bane? Naga Zaid yana masifar kama dashi, gwara Zaitoon tana ɗan kama dake”. Tana miƙa masa Zaid dake hannunta ganin ya miƙa mata hannunsa alamun ta bashi Zaid ɗin, cikin jin dadin ganin yadda Zaid ɗin da yar tafiyarsa ta fara miƙewa sosai alamun aikin ya fara sauƙi sosai, cikin kiyayewa take kallon Sa'ad ɗin jin yana cewa
“Babe ina son yaran nan sun shiga raina, da zamu samu a bamu su ina so, kafin muma Allah ya bamu namu”. A hankali tace. “Ai yanzu ma namu ne”. Yana sunsunar wuyan Zaid yace. “To ina Mom nasu da Dad ɗinsu”. A hankali Tace. "Dad ɗinsu ya rasu 9 Mounts ago”. Cikin sanyi yace. "Yah Salam, Allah sarki rayuwa, kenan marayu nema Allah ya jikansa ya rayasu bisa imani, Ayyah bazasu tuna Dad nasu ba, suma zasu tashi kamar yadda na tashi maraya nima ina da 1 year Dad na ya rasu shiyasa ni kaɗai Mom ke da ni dan data ƙara aurema bata haihuba, sun ban tausayi Babe dan Allah a bamu su in munyi aure wlh ina sonsu”. Sai kuma ya zuba mata ido ganin tana zubda ƙwallan cikin sanyi da so na gskya yace. "So Sorry kiyi masa addu'a, ina Mom nasu?”. Kanta ta nuna da babban yatsarta kana a hankali tace. “Nice Mom ɗinsu Yah Amin shine Dad ɗinsu, shine babba akan big broz da kake cewa”. Numfashi mai sanyi ya fesar ido cike da hawaye yace. "Allah Ubangijin talikai yayi min gata da sa'a irin na Yah Amin nima in samu ki haifa min twins in munyi aure”. Tana mai share ƙwalla tace. “Nace maka fa nice Mom ɗinsu ina nufin nayi nayi aure kuma yaranane”. Cikin yi mata wani irin kallon yace......

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.