Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 43 of 86

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA

Kai ta jingina da jikin ƙofar tare da lumshe idonta.
“Ko na mishi magna ma ba kulani zai yi ba, kuma in sha Allah zan je”. Ta faɗa cikin ranta tare da ɗan kasa kunne jin alamun buɗe gate.
Shiru tayi a wurin har Saida taji ya fita Baba idi ya maida gate ɗin ya rufe.
Da sallama ta shiga tare da ɗan sake fuskantar tana zama gefen Ummi tace.
“Ya barni”.
Cikin jin daɗi Ummi tace yauwa ɗiyata ai kinga haka yafi ko, ko gaba duk inda zakije ko me kike buƙata naki ko na yaranku shi zakiyiwa mgna ko”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“To. Bari inje in shirya”.
Goggo Dada ce data zuba mata ido cikin son nazartar yananinta data kasa ganewa tace.
“Bari in canzawa su Zaid kaya ko”.
Juyowa tayi ta kalli Zaitoon dake cikin wata riga mai masifar kyau red color mai ɗan ratsin blue sai blue jeans kanta ta kalla ganin kitson da Samira tayi mata da ribbons masu collas sosai tayi kyau.
Sha Zaid jeans ɗin ne a jikinsa da riga red color da ɗigon blue.
“Ai wannan ɗin ma yayi ba sai an canza ba”.
Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin Goggo Dada.

Kai Ummin ta juya tana kallon ƙofar parlour Jin ana Knocking.
Mama Samira dake gyara dinnin table ɗin da sukayi breakfast ta kira tare da cewa.
“Buɗe ƙofar na”.
Da sauri ta nufi bakin ƙofar.
Fuska ɗauke da murmushi ta ɗan ja da baya, ganin Saddiqa da Aunty Jamila da Hajja inna.
“A'a sannunku da zuwa ku iso ciki”.
Murmushi Aunty Jamila tayi tare da bin bayan Hajja inna.
Kana Saddiqa ta mara musu baya.
Ummi na ganinsu ta miƙe tsaye tare da cewa.
"A'a lale marhabin da zuwa Hajja inna”.
Da sauri Goggo Dada tace.
“A yau manyan baƙi ke garemu kenan, sannunku da zuwa ku iso”.
Murmushi Hajja inna tayi tare da zama bisa kujerar da Ummi ke nuna mata.

Saddiqa kuwa Zaitoon ta miƙawa hannu aiko tana dariya tazo.
Aunty Jamila kuwa hannun tasa zata ɗauki Zaid da sauri ya koma gefen Goggo Dada.
“Kaji ɗan nema wato ni bai sanniba”.
Ta faɗa tana zama.
Dariya sukayi ganin ya koma bayan Ummi yana leƙosu in an miƙo masa hannun sai ya maƙe kafaɗa.
Maman Samira ce ta dire Tray ɗauke da drink and bottle water sai cups uku.
Sai kuma ta kalli Ummi dake cewa.
Yauwa duba a fridge ɗin Dinnin nan kamar akwai fura da nono maza kawowa Hajja inna”.
Da sauri ta juya.
Goggo Dada ce ta kallesu tace.
“Da kun yi tsaɓani da Fariyda dan yanzu take shirin tafiya”.
Kallonsu suka maida kan Fariyda data fito cikin wani dantsatsen lice white and orange color mai taushi da sheƙi doguwar rigar ta zauna ɗas a jikinta. Mayafin ta rataye a kafaɗa sai handa bang nata.
Turus tayi tare da cewa.
"Laa Aunty Saddiqa kune sannunku da zuwa Aunty Jamila.”
Ta ƙare maganar tana ƙarasowa cikin parlour gefen Hajja inna ta zauna tare da cewa.
“Sannunku da zuwa, Bismillah kusha ruwa”.
Saddqa data zuba mata idone tace.
"Lallai amarci yayi rana”.
Ta faɗa yadda bazasu jita ba.
Aunty Jamila dake gaisawa da Ummi da Goggo Dada da suka zame kasa suma suka zauna kan carpert ya rage Hajja inna ce kaɗai a sama.
“Na duba fa Nonon nan ya ƙare, sai na Mahmoud ne kaɗai ya rage maman Samira”.
Ta faɗa tana rusunawa kusa da Ummi da sauri Goggo Dada ta tashi tare da nufar dinnin area ɗin.
Yayinda su kuma suke gaggaisawa.
Fridge ɗin ta buɗe yess babu sai iya sauran nasa robobi uku kacal.
Ɗaukowa tayi tare da kawomusu shi.
“Kai aiko naji daɗin nonon nan miƙo min Fariyda”.
Goggo Dada ne tayi saurin miƙa mata bayan ta balle marfin, amsa tayi tare da fara sha sai kuma ta kalli Fariyda tace.
“Yau dai na ƙwace miki fadar ni zan shanye damun mijin naki”.
Dariya su Ummi sukayi ita kuwa hannun Saddiqa da Aunty Jamila taja tare da cewa.
“Mu isa ciki”.
A parlour suka bar Hajja inna da su Ummi keta hidima da ita tanata sa musu al'barka,
Abba ma har nan yazo ya gaidata.

Su kuma bedroom ɗin Goggo Dada suka tafi inda Maman Samira ta kawo musu dukkan abin buƙata.
Haka dai suka wuni hira da ciye-ciye wanda Goggo Dada da kanta ta shiga kitchen ta taya maman Samira aikin.
har akayi sallan magrib suna gidan.
"Gsky dai wannan tsarin naki sam baiba Fariyda shifa zaman aure ba wasa bane, ba kuma ra'ayi bane, ko abinda aka ga dama za'ayi ba abinda Allah da Manzonsa sukace shi za'ayi”.
Aunty Jamila ta faɗa cikin tsareta da ido. Saddiqa kuwa numfashi ta fesar kana a hankali tace.
“Zancen Allah ma ta takura baiwar Allah nan fisabilillahi bawai baki da wurin zamaba kizo ki takurawa mata a ɗakinta, ai tunda ance aure to mgna ta ƙare, wlh kara Goggo Dada take miki, ke ko kunya ma”. Kai ta ɗan ɗago ido cike da ƙwalla take kallonsu murya can ƙasa tace.
“To ina zan zauna in ba nan ba, ni wlh bazan iya zama a part ɗinmu da Yah Amin ba, nasan zanyi ta yi masa kuka madadin addu'a”.
Da sauri Aunty Jamila tace.
“Sama zaki koma inda mijinki yake, naji yadda Aunty Amarya tai ta yabawa mana tsarin wurin.”
Da sauri tace.
“Na shiga uku ai zai kasheni”. Ta faɗa ba tare da ta kuma cewa komai ba, haka sukaci gaba da faɗansu yana shiga ta dama ya fita ta hagu haka dai har aka kira sallan isha bayan sun idar ne suka ɗan ci abincin da Samira da ta dawo gidan Bappa Lawan ta jera musu shi kasan cewar a ƙoshe suke kaɗan sukaci su fito.

A parlour suka samesu zaune.
Danderun jan nama da Goggo Dada tayi matane a gabanta, tare da bread ɗin alkama, sai ɗaya gefen kuma tuwon semo da miyar ɗanyen kuɓewa ne.
Gefenta suka zauna Saddiqa na mata tsiya.
“ke kin ganki wlh kici a hankali kada ki kasa tashi, yanzu mukayi waya da Sadiq ya iso zamu tafi”.
Gyara kallabinta tayi tare da miƙe ƙafa tace.
“Wa ni ai ba inda zan tafi sai mijin Fariyda ya dawo na ganshi, dan Aminullahi na sani shi wannan ban sanshi ba”.
Dai-dai lokacin kuma Hafiz ya shigo rataye da jakar Cameransa”.
Fariyda ne ta ɗan yafaci Saddiqa tare da cewa.
“Dan Allah jata mu tafi”.
Tayi magnar ƙasa-ƙasa tana kallon Hafiz da ya juya baya yana cewa.
“Bismillah Sadiq ka iso mana”.
Sannu da zuwa su Ummi sukayi masa.
Sai kuma ya kalli Hajja inna dake cewa.
“Yauwa taho ku ƙarasa min abincin nan ni kam Alhamdulillah ciki ya cika”.
Ummi tace.
“Ba abinda kikaci na kirki Hajja”.
Tace. “Ai Alhamdulillah yanzu dai a kira min shi Mahamudun tunda shi baije gaisuwar surkaiba bare ta kakannin yanzu sai a kira shi tunda gani nazo har gida”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Hafiz je ka duba ko ya dawo, kace yayi baƙi a parlour yazo suna sauri”.
Juyawa Hafiz ɗin yayi tare da cewa.
“Eh bai dai dade da dawowaba”.
Tana afa goronta a baki tace.
“To kira woshi dai kazo kaida saddiƙu ku suɗe min kwano”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Sadiq fara suɗewa kafin inzo”.
Yana murmushi yace.
“Aunty Fariyda zanci wannan amman a samo wani plate ɗin ba anata za'a saminba”.
Plate dake gefe ta jawo ta fara sa mishi danderun tare da kallon Hajja inna dake mitar yaƙi yaci a plate ɗinta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.