Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 14 of 86
Ƙugu ya riƙe cike da mamakin ganin yayi bacci.
Yess ya sanshi in baccinsa yazo bai jira.
Sunkuyowa yayi kanshi a hankali ya gyara masa kwanciyar tare da ƙara masa gudun AC.
Kana shi kuwa yaje yayi alwala yazo yayi nafilfilinshi.
Sai karfe ɗaya dai-dai ya haura kan gadon kefensa ya kwanta cike dajin wani irin farin ciki na musamman yau Mahmoud zai kwana a part ɗinsa a ɗakinsa kan gadonsa.
Zasu kwana tare bayan wata bakwai dan lokaci da Fariyda ta haihu yaje side ɗin Mahmoud sun kwana a ɗakinsa.
Addu'a yayi tare da shafawa Mahmoud ɗin kana yayiwa kansa.
Ranar Alhamis bayan la'asar duk suna zaune a mean people.
Suka shigo parlour daga parlour Abba yana gaba Abba na biye dashi a baya.
Da sauri Hafiz ya miƙe tare da amsar jakar hannunsa.
Shi kuwa Aminullah cikin mamaki ya zuba mishi ido ganin ya fito da alamun tafiya.
Gefen Ummi ya zauna tare da gyara net ɗin wuyansa cikin neman nasara yace.
“To Ummi zan tafi”.
Da sauri tace.
“Tafiya kuma to zuwa ina?”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“Yanzu dai Abuja zan wuce, in sha Allah gobe da sassafe jirginmu zai tashi Abuja to Istanbul”.
Wani irin murmushin mai cike da mamaki Ummi Goggo Dada Hafiz da Samira sukayi.
Fariyda kuwa dake jera abinci bisa Dinnin table baki ta taɓe.
Yah Amin kuwa ya jujjuya kai yayi tare da cewa.
“Kayi sauri kada ka makara”.
Murmushi Abba yayi tare da cewa.
“To dama kasan zai tafi ne?”. Yana miƙewa tsaye yace. “A'a kawai dai nasan bazai bari inji Istanbul ba, dama Dubai ne nan nasan bazai damu ba saboda ba sanyi.”
Kanshi Ummi ta ɗan shafa tare da cewa.
“To Allah Ubangijin talikai ya kaika lfy Babana.
Allah kuma ya dawo da kai lfy, Allah yasa zuwan naka shine mafi alkhairi.”
Cikin jin dadin addu'arta yace.
Amin daga nan
Duk akayi ta mshi fatan isa lfy.
Aminullah da Hafiz suka rakashi Malam Aminu Kano international airport.
Ƙarfe shida dai-dai jirginsu ya tashi zuwa Abuja.
Washe gari da safe jirginsu ya ɗaga zuwa Istanbul....
Ranar Sunday da safe.
Da sauri Fariyda dake kwance gefen Aminullah ɗin ta miƙe zaune jin yadda ya farka a firgice tare da dafe ƙahon zuciyarsa yana furta.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun”.
Sai kuma ya juyo gefen damansa tare da fara lalubar wayarsa dake ƙasan pillow.
Cikin mamakin yadda yake a gigice da alamun da mugun mafarkine ya farka.
“Yah Amin lfy? Meke faruwa?”.
Yana manna wayar a kunnesa yace.
“Mahmoud Fariyda ɗan uwana, tunda ya tafi mabuyi magna dashi ba, yanzu kuma nayi mafarki mai muni a kansa”.
Ya ƙare maganar cikin mabayyanin tashin hankalin da ya raunata zuciyarsa, matsowa gareshi ta ƙarayi tare da riƙo hannunsa da ya dafe ƙirjinsa yana faɗi mata.
“Kinga yanzuma layinsa baya shiga, gashi baya online”.
Cikin tausasa murya tace.
“Yah Amin mafarkifa ba gsky bane, yaron da ka sanshi da bahagon hali wata ƙil kawai baccin gajiya yakeyi ya kashe phones ɗinsa”.
Da sauri ya ɗan ture ta tare da sauƙowa kan gadon yana faɗin.
“Baki san halin da na ganshi cikin mafarki bane, shiyasa kike faɗin haka”.
Ya dire mgnar yana ƙoƙarin danne hawayensa dake silalowa.
Sai kuma ya nufi Bathroom al'wala yayi kana ya fito ganin lokacin yin walaha nafila yayi kana ya ɗaura da karatun Alqur'ani mai girma Sannan yayiwa ƙanin nashi addu'ar neman kariya.
Duk tana kwance gefensa tana ganinsa.
“Ki tashi ki samu Samira kuyi masa ayi sadaka yau ɗin nan”.
Tana miƙewa zaune tace.
“Shekaran jiyafa akayi sadakan nan”.
Yana tsuke fuska yace.
“Ok jumma'ace kaɗai aka ware ranar sadaka”.
Cikin sanyi tace.
“A'a bari inje zamuyi”.
Daga nan ya fita, shi kuwa cikin gida ya shiga a dinnin table ya samu Ummi da Goggo Dada suna cin abinci.
“Ummi kunyi waya da Mahmoud kuwa yau?”.
Kai ta ɗan jujjuya mishi tare da cewa.
“A'a....
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa, mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 6
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
“A'a ba muyi magna ba, amman yanzu ma yayi waya da Abbanku na barsu ma suna mgna”.
A hankali ya koma ya zauna daga yunƙuran tsoro da yayi, sassayan numfashi ya sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah, ni tunda ya tafi bamu yi magana ba, shiyasa nake tambaya”.
Ya ƙare maganar cikin hikimar ɓoye tashin hankali da mafarkin da yayi ya sashi, saboda gudun tashin hankali iyayensun.
“Eh haka naji yana gayawa Abbanku, yace waryace yake kashewa dan ya fison ya gama, komai cikin mako biyu ya dawo.”
Yana amsar cup ɗin tea da Goggo Dada take miƙa mai yace.
“Eh lallai kam nima saida ya tafine na fahimci yana da mahimmin aikin da yake yi, shiyasa yayi ta kafewar bazai jeba, kashe wayarma bai rasa nasaba da wannan aikin”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Allah dai yayi muku al'barka ya baku sa'a a cikin dukkan lamuranku”.
Ringing ɗin da wayarsa tayi ne ya sashi zaro wayar yana amsawa da.
“Allahummah Amin Ya Allah”.
Sai kuma ya kalli Goggo Dada yana faɗin.
“Gashi nan ma shike kira”. Kai ta jinjina tare da cewa. “Dan halal kenan yaƙi ambato”.
“Yah Amin kana lfy”.
Ya faɗa bayan ya amsa sallamar Yah Amin ɗin nasa.
Kai ya jinjina tamkar yana gabansa kana yace.
“Ba komai Mahmoud sai daga baya ne, ma na fahimci aikin ke gabanka.
Amman please dan Allah ka kula, Allah ya baka sa'a”.
Ya dire mgnar tare da miƙewa ya bar parlour baki ɗaya.
A ƙofar shiga part ɗinsu yayi kiciɓis da Fariyda dake cikin wata tattausar Abaya mai masifar sulɓi da ƙelli Royal Blue color, duk da faɗinta ta koma ta lafe a ƙirar jikinta mai jan hankali, tayi rolling kanta da gyalensa fuskartan nan ta fito a 0 hannun shi nadama yasa ya jawota jikinsa tare dayi mata, wani irin rungumar dake nuna tsananin soyayyar su
Sai kuma ya maƙale wayar da kafaɗarsa tare dasa hannunsa ya tallabo fuskantar.
Gashin girarta dake kwance lib tamkar wanda aka zana shi, yatsarsa manuniya ya ɗaura kan tsakiyar girar nata dake haɗe kan tsakiyar gocinta.
A hankali ya fara yin ƙasa da yatsarsan har ya iso kan tsinin hancin nata.
Numfashi ya shaƙa da sanyin yanayin da ƙamshin jikinta ya dirar masa, lips ɗinta da suke ƙyalli ya kuma ɗan shafawa.
Murya can ƙasa maƙoshi yace.
“Fatabarakallahu feeh ahsanil khaliƙin.”
Sai kuma yayi saurin cewa. “Eh ina jin ka”.
Saboda jin Mahmoud ya ɗan tsagaita daga bayanin sabon aikin da aka miƙa masa.
Ita ma Fariyda ido ta zuba mishi, surar halitta launuka kyan da Allah yayi masa take kallo.
Wani irin kyau na musamman taga yayi mata wanda ta gaza janye ƙwayar idonta daga kallonsa.
Hancinta ya ɗan lakace tare dayi mata raɗa a kunne.
“Yah dai ko ranki ya biya ne, inje inbiya bashi”.
Murmushi mai cike da kunya tayi kana ta janye jikinta.
Da sauri ya jata tare da cewa. “Zo nan”.
Allah ya sani shi yama mace yana waya da Mahmoud ɗin.
Shi kuwa Mahmoud tsaki yaja tare da katse kiran.
Kana ya koma ya kwanta dan baccin da baiyi daren jiya daya kwana aiki ne yasashi lumshe manyan idanunsa, in seconds yayi baccinsa cike da salama...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.