Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 50 of 86
Bayan kwana takwas.
Abba ne zaune gaban Baba Malam, yana isar da manufar zuwansa.
Cikin jinjina kai Baba Malam yace.
“In sha Allah zanyi magna da Sani ya tuntuÉ“i Æ´ar in dai babu wanda ta tsayar takeso sai ya fara zuwa, in Kuma akwai wanda yakeso sai yazo akwai wacce zamu nuna masa in tayi masa, dan mu kam Allah yayi mana arzikin Æ´aÆ´a mata mazan ma Alhamdulillahâ€.
Cikin gamsuwa Abba yace.
“To sai naji kaâ€.
Da yammacin ranar Hafiz ne zaune a parlour riƙe da wayarsa video call sukeyi da Mahmoud dasu Zaid Zaitoon ce keta rakaɗi da tafi da Balankwace shi kuwa Zaid shiru yayi ya zuba wa Mahmoud ɗin ido tare da manna kansa bisa ƙirjin Hafiz.
“Hafiz ya naga Zaid kamar ba lfy?â€. Ya tambaya cikin kulawa da fargaba, yana gyara zaman wayar tasa yace.
“Eh ai jiya ciwon cikinsa ya kuma tashi kwana yayi kuka, yau tun safe ni da Aunty Fariyda muka koma asbiti an canza masa wani mgnin, yanzu da ya shane yayi shiruâ€.
Cikin murya mafi ƙololiwar damuwa yace.
“Amman da sauÆ™i yanzu koâ€. Kai ya gyaÉ—a masa, sai kuma ya miÆ™awa Goggo Dada dake cewa.
“Da sauÆ™i sosai fa, yanzuma dan bacci yakeji shiyasa ka ganshi hakaâ€.
Numfashi mai tsawo ya fesar a hankali yace.
“Na kusa kammalawa dai in dawoâ€.
Ummi tace.
“Allah ya bada Sa'aâ€.
Amin yace tare da É—aga musu hannun alamun bey a tare duk suka É—aga masa hannu suna murmushi.
Cikin sanyi Salma ta kalli Mamanta tare da gyaÉ—a mata kai.
“Na gane shiâ€.
Zama ta gyara tare da mata bayanin da mijinta yayi mata kamar yadda sukayi da Baba Malam, ta É—aura da cewa.
“Yanzu ya kika gani, zaki saurari Salim ne ko har yanzu kina kan bakarki na son Mahmoud?â€.
Cikin sanyin murya ido cike da hawaye tace.
“Mimi ina son Mahmoud son da banayiwa ko wanne É—a namiji irinsa Amman na yafewa yar uwata Fariyda dashi, dama ance imanin É—ayanmu baya cika har sai ya sowa É—an uwansa abinda ya sowa kansa. Mimy tunda aka aurawa Mahmoud Fariyda na haÆ™ura dashi na ciresa a tsammanin mijin aure, zan Æ™are rayuwata da yi musu fata da addu'a zaman lafiya, abubuwan da nake gani tare dashi na farin cikin zaman aure Allah ya kasantar dashi kan yar uwata kuma Aminiyata Fariydaâ€.
Sai kuma tayi shiru saboda rawan da muryata ya tsananta, kanta Mimi ta fara shafawa tare da cewa.
“In sha Allah bazaki taÉ“eba tunda kika tsarkake zuciyarki akan yar uwarkiâ€.
Salma tace.
“Ni yanzu kunyar Fariyda nake jima Mimi na yadda nai ta nuna mata ina son Mahmoud a baya, da na sani da ban faÉ—aba ko dan kar zuciyarta ya tsargu dani akan mijinta. Shi yasa gwara in saurari Salim in Allah yayi miji nane shi zata fi samun nitsuwa dani, ni kuma ko ba komai na samu kekkyawan kuma É—an uwan Mahmoud mai masifar kama dashi zumuncin Æ´aÆ´ana dana Fariyda ya Æ™ara Æ™arfi na gefen uwa da Ubaâ€. Cikin gamsuwa Mimi tace.
“Hakan shine dai-dai kuma in sha Allah zan gayawa Babanki ya gayawa Baba Malam an bashi izinin Allah ya tabbatar muku da alkhairiâ€.
Amin tace tana rufe fuskarta.
Washe garin ranar Fariyda ne tsaye a tsakiyar parlour nasa, tunda ta dawo sama tsakaninta da parlour wucewa sai yau yanzu da ganin kamar parlour yayi ƙurane yasa ta ɗan tsaya tana ƙare masa kallo, idonta ta tsaida kan Dinnin area a hankali ta nufo can Zaid da Zaitoon na biye da ita a baya, show glass irin mai two door ɗin nanne tsaye gefen dama can hagu kuma Fridge sai kuma washing hand baby ɗin, Dannin table ɗin nasa ta ƙarewa kallo, sai kuma ta matso kusa da fridge ɗin ganinsa a kunne.
A hankali tasa hannunta ta buÉ—e cikin mmki ta zubawa drinks É—in dake jere a step É—in farko mai binsa sa kuma fruits ne da suke nan ras.
Sai na ukun da yake É—auke da wasu ganyayykin da ta kasa gane na meyene tana dai ganin kullum dasu ake tafasa masa tea, kuma tea É—insa ba'a haÉ—awa da kowa, ba mai shan tea É—insa sai Yah Amin shima zata iya irga sau nawa taga yasha.
Na huɗun ta ɗan leƙa inda taga wasu gorunan maganin da yafi kama dana gargajiya ko Islamic.
Baki ta ɗan taɓe ganin yadda komai yake reras tamkar an barsu dan jerene, Admiral da taga sunfi yawa a cikin fridge ɗin ne, yasa tai niyar zare ɗaya har ta kai hannunta ba tare da ta taɓa ba kuma ta janye tare da juyawa ta jawo hannun Zaitoon dake ƙoƙarin haɗa kanta da show glass ɗin da ta ganshi killace da duk abubuwan buƙatarsa kama daga plates, bowls, mugs, set spoon, sai tissue da kuma wasu ƴan mitsi-mitsin towel masu taushi da sauri ta jasu suka bar wurin.
Ƙofar da ta hango can da ɗan nesa a gefen dama ta leƙa da sauri ta fito ganin corridorn cike da duhu.
Gefen hagu ta ta murɗa handle ɗin, kitchen ne mai zaman kansa wanda babu wani abun buƙata na aiki da babushi a ciki.
Jan ƙofar tayi ta rufe da mmkin ganin kamar ba'a girki a ciki kuma akwai abubuwan buƙatar dake nuna ana ƴan ƙananan abubuwa a ciki, ɗaya ƙofar dake daga bakin ƙofar parlour ta buɗe ganin bathroom ne yasa ta rufe yana nan komai fes-fes a ciki.
Kofar dake can ɗan nesa dashi kaɗan ta kalla ɗakin da ya maida gim ɗin ne, shima na tayi rufe, kan tv ɗinsa ta sauƙe idonta.
Sai kuma ta nufi wurin a hankali ta kunne socket É—in.
Ai kuwa tana kunna wa TV ya kawo rimot ɗin shi ta ɗauka tare da ɗan ja da baya fuska ta ƙwaɓe gani tashar Football ne akeyi aiko, sauya tashar tayi, Wrestling akeyi ƙatti nata kimar juna, tsaki taja ganin duk channels ɗin nasa suk ba na zaman lafiya a fili tace.
“Dama wannan ta ina za'a samu abun arziki a TVnsa ai sai masifa yaÆ™i da É“aÆ™ar mgnaâ€.
Ta ƙare maganar tana ci gaba da dudduba channels ɗin wani tsakin taja tare da cewa.
“Bashi da abin gani sai Football wrestling sai boxing duk abun mugunta shine nasa, ayi mutum da baƙar zuciya kamar rainon fir'aun..†sai kuma tayi shiru ba tare da ta ƙarasa magnar ba, ganin ta shigo sahun MBC tafiya ta rinƙayi dai har ta dawo kan Arab Channels.
Juyowa tayi ta kalli su Zaid jin yadda suke ta sowa da zagaye tsakiyar parlour suna cike da nishaÉ—i, da sauri ta koma baya ganin ta wuce Zee world murmushin mai cike da jin daÉ—i tayi, ranbanta da bibiyar su tun kafin rasuwar Yah Amin wanda da kuma sune abin kallonta, number channel É—in ta duba tare da jinjina kai, dan a parlour su Ummi in banda su Afirka tv 3 tabsir da qur'an ba abinda suke kallo.
Zama ta gyara tare da kishingiÉ—a kan kujerar tana kallon su Zaid da wasan ya koma a kwance alamun bacci ya fara kawo musu hari.
Lumshe idonta tayi tare da buÉ—ewa hawaye na cikowa ganin film É—in Kal hoo naa hoo akeyi.
Haka nan taji mood É—inta na sauyawa tunanin Yah Amin ya dawo mata.
Buga ƙofar da taji ne ya sata ɗan juyowa tare da ɗan maida hankali duka kan ƙofar ganin an turo ƙofar, da sauri ta miƙe tsaye cikin mamaki ta zaro ido ganin Yah Mujahid tsaye bakin ƙofar parlour ya zura hannunsa cikin aljuhun rigarsa yanayi mata wani irin kallo mai bayyana tsananin so da ƙauna mai zafi murmushi ya sakar mata tare da ƙarasowa ciki da sauri ta matsa ganin yadda ya........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.