Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 54 of 86

Ƙarfe ɗaya dai-dai ya fito.
Masallaci ya wuce bayan anyi sallane ya wuce gidan Amina a can yaci yayi ƙat ya dawo dana dawowa.

Washe gari da safe zaune suke a parlour Abba suna shan tea kamar kullum, Salim ya shigo bayan sun gaisa ne shima an bashi tea ɗin suka ɗanci gaba da hirar kayansu da suka iso da wanda basu iso ba. Sai kusan ƙarfe sha biyu suka fito sama suka haura tare.
“Ka shirya da yamma zaka rakani zance dan an min izinin fara zuwa tuni mun fara sabawa”.
Yana zama kan kujerar yace.
"Bazan jeba”. Da sauri Salim yace.
"Dan Allah kayi haƙuri muje ka ganta, kaga zaɓina”.
Yana danna remote ɗin tv yace.
"Wlh bazan jeba, banza mai ƙaramin kai kaje ka nemi matan da suka cika mata mana yan 28 to 30 dai-dai da kai ka tsaya neman yan 20 years in Banda nema mana raini me hakan”.
Kai Salim ya girgiza cikin takaici yasan tunda ya rantse to bazai je ɗin ba hararansa yayi yace.
“Ina da 30 kuma in aure yar 30 a wannan kam bazata saɓu ba, gwara dai hakan sune dai-dai damu ko ba komai mun bawa matanmu 7 to 8 years ai haka shine cib da cib”.
Shi dai baya ma jinsa dan tashi ma yayi ya haɗa PS5 ɗinsa kana ya dawo ya zauna tare da miƙawa Salim ɗaya yace.
“Mu muga game”. Cikin takaici Salim ya miƙe tare da cewa.
“Anƙi a buga ɗin bazan yiba sai kayi kai kaɗai”. Baki ya taɓa ya fara buga game ɗin, har yaje bakin kofa sai kuma ya leƙo yace. “Sai yaushe zaka fara fita office ba tare da ya kallesa ba yace.
“Ban sani ba, in dawo daga tafiya ko kwana biyar baiba kana kira min office”.

Bayan kwana biyu da dare zaune suke Hafiz ne ya miƙa mata wayarta tare da cewa.
“Gashi ana kiran ki”.
Fariyda tace.
“Waye”.
Tana amsar wayar tayi picking call ɗin da sauri ganin Salma ce.
“Hello Fariyda ya gida ya twins namu da jiki”.
Tace. “Alhamdulillah jiki da sauƙi”.
Salma. “Yanzu muka iso gidan Aunty Aisha shine nace bari in taɓoki, dan yau kwana zamuyi aikin suna, kuma akwai magna sosai”.
Cikin zaƙuwa da mararin shiga yan uwa tace.
"Ayyeh kunji daɗin ku, kwana zakuyi”.
Salma tace.
"Ai dai kam gwara mu more kafin muma mu shiga daga ciki a fara hanamu kwana a unguwa bare ma my man naga da zafinsa”.
Da sauri tace.
“Hmmm Kice akwai labari kenan a ina yake? Waye shi me sunansa?”.
Tana dariya tace.
“Sai kin zo zan gaya miki”.
Daga nan ta katse kiran.
Ummi tace.
"Batun sunan Aisha ko”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa. “Su kwana ma zasuyi”.
Ummi tace.
“Ki tambaya kema in an barki sai ki tafi gobe da sassafe.”
Shiru tayi cikin nazarin ta yayama zatayi tambayar ita da ba mgna sukeyi ba, iya tsawon zamanta a gidansu sawon shekara biyu da watanni ma sau huɗu sukayi mgna shima biyu faɗane, ɗaya ne na farko da suka gaisa nan ma ita ta ɗaga mishi gaisuwa, kuma ranar da shi da kanshi yayi mata magna shima tambaya ne randa Aminullah yayi acsident in da yake ce mata ke ina Yah Amin?.

Hannu tasa ta amshi Zaid da Samira ta shigo da shi yana tsala ihu da cilla ƙafa.
Goyashi tayi Amman a banza.
“Yau kuma ciwon cikinsa ya motso kuma”.
Goggo Dada ta faɗa ita kuma Ummi Mahmoud dake parlour Abba ta kira ta faɗa masa, da sauri yazo ya ɗaukesa shida Goggo Dada suka tafi asbiti.
Bayan awa biyu da tafiyarsu suka dawo rungume dashi yayi bacci.
Gefen Ummi ya zauna tare da jungina kansa jikin kujera.
"Me sukace yau kuma”.
Goggo Dada tace.
“Sunce fa dole sai anyi masa tiyata an cire masa ciwon in ba haba ƙara girma zatayi tayi, kuma zata shafi lfyarsa”.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Innalillahi yaro ƙarami da tiyata”.
Hafiz ne yace.
"To ai Ummi gwara kawai ayi masa muma an yiwa ɗan bappanmu Musa kuma ya warke shi tun bai wuce 2 Mount bana akayi masa”.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da cewa.
“Zan fita waje dashi akwai wani babban likitan yara ɗan India Dr Imran Patel da Dr Fadil ɗin ya bani labarinsa yace babban Dr yarane number ɗaya a duniya”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Hakan yayi gwara ku kaishi can ɗin”.

Washe gari da safe misalin ƙarfe tara da rabi.
A hankali ta ajiye wayar tare da jin kalaman Mamy na ƙara dawo mata, ga kuma ƴan uwa dake can cike a gida suna ba ita.
A parlour ta tsaya tana kallon ƙofar parlour don taji motsin an buɗe, to fita yayi kenan ba shigowa ba. Ta faɗa a saman lips ɗinta.
Sai kuma ta kuyo da sauri jin sautin rufe fridge.
Fitowa yayi ya nufi tsakiyar parlour ba tare da ya kalli ta inda take bama da sauri ta ɗan bi bayansa tace.
“Good morning”. Bai kulataba saima fara shan fruits ɗin sa daya ɗauko yayi matsowa ta kumayi cikin ɗan ɗaga murya kaɗan tace.
“Ina kwana”. Fuska ya taɓe tare da cewa.
“Ni mate ɗinki ne da zaki gaisheni, ni zaki nunawa munafurci............

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276 mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 23
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Kai ta jujjuya a hankali ba tare da ya kalleta ba ya kuma cewa
“In banda munafunci dama kina gaisheni ne?”.
Still kai ta girgiza har lau dai bai kalletaba yace.
“To munafuncin me ya saki gaisheni?”. A hankali tace
“Dama Mamy nane tace bata yafe min ba in fita bada izinin kaba, to kuma yau ana sunan Aunty Aisha ta haihu ne nake son zuwa”.
Ko ƙala bai kuma ce mata ba, kusa 3 minute tana tsaye ganin yadda yayine yasata cewa.
“Inje ne?”. Miƙewa yayi tsaye ya nufi kofar fita ba tare da ya kalli ko ta inda take ba, ya sauƙa ƙasa ƙasa wurinsu Ummi da plate ɗin fruits ɗin.

Tsayuwa tayi a wurin ta rasa abin yi, sai kuma ta juya tayi cike ido cike da ƙollan baƙin ciki a fili tace.
“Allah sarki Yah Amin na bawan in sha Allah kana cikin aljannatul Firdausi da yardar Allah yadda kake da sanyin hali haka makwancinka yake.“
Wayarta dake ringing ta ɗauka gani Aunty Saddiqa ke kiranta.
“Ayyah mutanen Kano kunji daɗi ku kam da bakuyi auren nesa ba komai kuna tare, mu kuma yan nesa sai dai muga hoto, nasan yau gidan Aisha kamar zai fashe naga tuni Rashida ya fara sa hotuna a status”.
Cikin takaici tace.
“Nima ban jeba”. Ceke da mmki Saddiqa ta tambaye ta meya hanata zuwa, nan ta bata lbrin yadda tayi da Mamy da shi duka da yadda sukayi yanzu cikin sauri tace.
“Tunda kikace ya sauƙa ƙasa ai kawai yi maza ki bishi a baya ki ƙara tambayarsa a gabansu Ummi na tabbatar zasu sa baki ya barki tunda Allah ya baki iyayen miji na gari ba irin namuba marasa kirki”.
Cikin sanyi tace.
“Ni bana son wulaƙanci ne da raini”.
Cikin faɗa Saddiqa tace.
“Kije ki tambaya in kina son zuwa, in bakya so kuma shike nan, ni sai anjima bazanyi ta jin kina saɓon Allah ba wai mijinki kike cewa raini hmmm”.
Daga nan ta katse kira.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.