Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 57 of 86
3,383,496, duk mutum ɗaya in business seat in zamuyi transit a Ethiopia kenan. In Kuma first class ne 5,365, 161, duk mutum ɗaya, kuma kaga Zaid da Zaitoon ɗinma dole kuɗin seat za'a biya musu sannan azo a ƙara wata kuma, ai abin zai yi yawa, wannan fa iya zuwane inaga an haɗa dana dawowa, da kuma kuɗin aiki, masauƙin, abinci, zirga-zirga. Banda na nan Kano to Abuja da kuma Mumbai to Ahmedabad Ai abin zai yi yawa ko Abba?”.
Murmushi Abba yayi tare da cewa.
“In dai Zaid ya samu lfy ai ko billion muka kashe ba asara a ciki Mahmoud, to kuma yanzu kai in an barka sai ka tafi ba tare da uwarsu ba, kuma kace harda ita Zaitoon ɗin zaka tafi, bakama tsoron ka shiga komar tuhuma Ethiopia ko India ɗin akan ina ka samo yaran ina uwarsu”.
Kai ya ɗan sosa tare da cewa.
“Abba ai duk inda na shiga dasu a duniya ana ganinsu an san jininane, bafa wata matsala tafiya da itanema matsala kam”.
Cikin tsareshi da ido da fahimtar tabbas har cikin ƙoƙon ransa ne baya son duk wani abu da zai alaƙantashi da ita cikin girma yace.
"Ai raino dole saida uwa Mahmoud”.
Da sauri yace.
“Abba zan iya musu komai fa”.
Abba yace. “Kuma kai ka gamsu katafi ka bar matarka a gida Abbana”.
Da sauri yace.
"Nifa banda buƙatar ta kusa dani dan na tsanet”.
Sai kuma yayi shiru dan mgnar kamar kubce mishi tayi.
Shi kuwa Abba cikin bada umarni yace.
"Kamar yadda Umminku ta faɗa maka Mahmoud dole da Fariyda zaku tafi India kuyi transit a duk inda kuke so ka kama duk irin hotel ɗin da kakeso kuci duk abinda kuke so ka kashe koma nawane bamu da asara tashi kaje na sallameka kaje ka haɗa shirin tafiya da Fariyda dan kafarka kafarta”.
Fuska a cunkushe ya miƙe tare da cewa.
“To Abba”. Sai kuma ya zauna jin Abba na cewa.
"Amma ka bincika nagartar asibitin da doctors ɗinsu ko?”.
Kai ya gyaɗa masa tare da cewa.
“Eh Abba shi mai asibitin ma musulmine Dr Imran Patel, sannan ƙwarerren likitan yarane yana da matakin karatu MBBS sunan asibitin nasa Om family care hospital.
Kuma yana da gwararrun likitoci na musamman wanda su fannin yara kawai suka karanta”.
Kai Abba ya jinjina cikin gamsuwa yace.
"To ba matsala aje aci gaba da shiri da Fariyda”.
Rai a ɓace ya fice.
Washe gari Mimi da amaryarta suka zo duba Zaid da jiki da suka koma ne suke faɗawa su Salma ai za'a fita India da Zaid da sauri Salma tace.
“Mimi harda Fariyda za'aje”.
Hararanta tayi tare da cewa.
“A'a dake za'aje ta yama zaki tambaya ai dai kin san dole aje da ita.”
Da sauri tace.
“Kuma da Mahmoud zasu tafi”.
Mimi na fita tace.
“Eh”.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
“Allah sarki yar uwata Fariyda ko ba komai nayi farin ciki abinda nake harin ban samu ba yar uwata zata samu, ya Salam inama in zama ƙuda in manne a jakarsu.
Tabbas yanzu Fariyda zata gane waye Mahmoud zako taga abinda yasa nake cewa shi na musamman ne kuma na dabanne na tabbatar za'a buga show a India”.
Sai kuma kawai ta kira Raihana dasu Humaira da Zainab tace su shirya jibi ko gobe suje su duba Zaid da jiki.
Mahmoud ɗin ne zaune a parlour ya gama cika duk wani abu na tafiyar Fariyda ta online cike da takaici.
Ya koma tattaunawa da hukumar shiga da fita na asibitin kasan cewar muddin mutum daga wata ƙasar yazo suke bawa mutum masauƙi a cikin hotel ɗinsu dake manne da asbitin kana harda Restaurant a ciki wanda duk abinda kakeso zasu kawo maka, kawai dai ajihunka ne zaiji.
Tammayar da sukayi masa da yarane yan shekara nawa mata ne ko maza.
Ya amsa musu sai kuma ya kalli tambaya ta biyun
Matarsa?.
Ido ya runtse tare da rasa ta yadda zai am musu wannan tambayar tasu.
Da sauri ya buɗe idonsa
“Ina har abadan haka bazai faruba ta yaya matar Yah Amin zata amsa sunan matarsa.
yatsarsa ya kai da nufin danna no kawai rashin sani ya danna yes da dama suna kasan tambayar.
Ummi ta kalli Mahmoud dake zaune yasa abinci a gaba ya gane sarai ba Ummi bace tayi, duk da bawai an sa garlic ɗin bane.
“Fariyda ki shirya kafin ku tafi kije ki wuni a gida ko”.
Cikin jin dadi tace.
“To Umma ngd Allah ya ƙara girma da nisan kwana”.
Amin tace tana kallon Mahmoud ɗin.
"Me kasa abinci a gaba kai shiru, ba kaine da kanka kace ayi maka miyar ganda na dinner ba.
Anyi maka kuma kayi zuru kaci kada yayi sanyi”.
Kai ya jinjina cike da gudun ɓacin ran mahaifiyar tasa yace.
“A ajiye min sai da safe zanci, yanzu a ƙoshe nake naje gidan Maman Hafiz naci a can”.
Kai kawai ta jinjina ta bar wurin dan tunowa da shawarar Goggo Dada na adena matsa mishi da faɗa kan Fariyda zai ƙara tsanarta ne.
Washe gari ta shirya taje gida wuni.
Raihana dake ajiye mata aloƙwai-loƙwai da tayi musune tace.
“Dafa yau zamuje gidanki sai Humaira tace mu bari sai gobe yau tana da baƙo”.
Murmushi tayi tana jan robar yajin kusa tana kallon Mamy dake cewa.
“Yaushe ne tafiyar taku kam”.
Tana gyara zamanta tace.
“Naji dai Ummi na cewa Goggo Dada ranar Sunday zamu tafi Abuja da safe, to India ne dai ban san yaushe za'a wuceba”.
Raihana ce tace.
“Kenan yau saura kwana uku.
In sha Allah gobe zamu zo mu wuni”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Allah ya kaimu”.
Da Amin suka amsa Aunty Amarya ce ta shigo riƙe da Zaid tana faɗin.
“Malam yace kije ku gaisa.”.
Zaune take gefen Malam ɗin bayan sun gaisa ya gama mata tammaya akan tafiyar tasu ya ɗaura da faɗin.
“To Fariyda am Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy yasa ayi aiki a sa'a ya bawa ɗanki lfy, ki kiyaye zamanki da mijinki ki sani shine sama dake aljannarki tana ƙarƙashin digaduginsa kada ki sauya daga biyayyar da kikeyiwa Aminullah yadda yake a wurinki shima Mahmoud haka ne yi nayi bari na bari, kada ki yarda ki kwana da fushinsa da fushinsa yana haɗe da fushin Allah, da tsinuwar mala iku da kuma rashin yafiyata”.
Cikin zubda ƙwallan take kyaɗa masa kai har dai ya gama kana ta koma cikin gida.
Da dare Hafiz yazo ya ɗauketa.
Washe gari da rana. Wuraren ƙarfe ɗaya
Suna zaune a parlour Mahmoud ɗin hirarsu sukeyi na ƙawaye kuma ƴan uwa iminai Salam tace.
“Bari mu gama cin abinci muyi salla wallahi nice nan zan shirya miki akwatin tafiyarki”.
Kai ta jingina tare da cewa.
“Nifa da ni kaɗai zanje ko da wani da nafi farin cikin tafiyar nan”.
Da sauri Salam tace.
“Hmmm ji nake mar in shiga zuciyarki in sauya miki tunaninki,
dan ni kaɗai nasan irin tsarin shigar da nakeso kiyi tayi a can shigar tada zaune tsaye”.
Murmushi i Zainab tayi, Raihana kuwa kanta ta kauda kamar bata wurin dan ta fi kowa sanin irin tsanar dake tsakanin Fariyda da Mahmoud ɗin.
Humaira ce ta kalli lips ɗin Fariyda da take motsa wa sai kuma ta kalli gashin girarta a hankali tace.
“Wlh in kuka haifi yaro ke da Mahmoud dole zaifi su Zaid kyau, saboda kyau da kyau ne zasu haɗe a jinin babyn”.
Harararta tayi tare da ƙara musu vegetables kan ɗanwaken da sukeci, ga tv dake aiki an saki waƙoƙin Film ɗin Fanaa na Amir Khan.
Da sauri suka juyo suna kallon bakin ƙofar parlour jin an tura ƙofar.
Tsaye yake cikin wasu datatstsun suit masu masifar kyau milk color.
Fuskar a tsuke yake kallon yadda suka hautsina masa parlour sai tashin cabeji da albasa da ɗan tunatar da yake tashi da ɗan hamami st............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.