Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 39 of 86
Ƙarfe huɗu dai-dai Goggo Dada ta tashi da mamki take kallonta tana zaune riƙe da hannunta.
Tana mai taune lips ɗin.
“Kin tashine Fariyda”.
A hankali tace.
“Ehh.”
Allah da ikonsa ta samu zogin ya lafa, sai lokacin bacci ya ɗauketa.
Ƙarfe takwas dai-dai ta fito parlour riƙe da ɗan kwalinta.
Da sauri Samira tayi kanta da nufin rungumeta sai kuma tayi sauri zare ido tare da cewa.
“Innalillahi Aunty Fariyda me ya samu hannunki”.
Da sauri Ummi da Goggo Dada suka ƙaraso wurin tallabo hannun Ummi tayi. ɗan ƙarfi ta saki wani irin ƙara.
Cikin kaɗuwa Goggo Dada tace.
“Innalillahi A'a karyewa tayi ne.”
Da sauri Ummi ta kamo hannunta mai lfyar ta zaunar da ita bisa kujera.
Sai kuma ta kalli Samira da sauri tace.
“Samira yi maza ki kira mana babanki, yazo ya duba mata hannun nan, kam karaya ne ko me?”.
Da sassarfa ta nufi waje.
Goggo Dada kuwa zama tayi kusa da ita tare da cewa.
“Sannu Fariyda am yaushe kikaji ciwon nan faɗuwa kikayi ne”.
Ba tare da ta jira cewar ta ba ta maida dubanta kan Ummi dake yiwa hannun kallon tsoron yadda ya kumbura.
“Ko zaki gayawa Abba ne mu tafi asbiti”.
Ummi tace.
“Ai baya nan yaje asbiti dubiya, jiya jumma'a bai samu yajeba shine yau ya tafi da Hafiz”.
Sallamar Baba idi ne yasa Ummi miƙewa tsaye tare da amsa sallamar da bashi izinin shigowa.
Duk abinda sukeyi yana zaune a dinnin area yasa Zaitoon da Zaid a gabansa kan table ɗin plate ɗin abincinsa na gabansa yana ci, su kuma suna rungime da gorunan bobo suna sha.
Ɗan gutun tsaki yaja jin yadda Fariyda ta kuma sakin ƙara.
“Gocewar ƙashine ba karaya ba, yayi tsamine shi ya jawo kumɓurin da yawaitan zafin”.
Baba idi ya faɗa tare da gyara zamansa a ƙasa.
Goggo Dada tace.
“To Alhamdulillah da sauƙi tunda ba karaya bane yanzu ya za'ayi”.
Baba idi ya kalli Samira tare da cewa.
“Je ki ɗauko min jakar fatar nan”.
Da sauri ta fita kanshi ya maida kan Ummi dake sharcewa Fariyda zufa dake karyo mata.
“Eh ba matsala in sha Allah zan ja mata targaɗen yanzu, sai dai kam dole zataji zafi dan yayi tsami”.
Cikin tausayawa Ummi tace.
“Oh Yah Allah sannu Fariyda am faɗuwa kikayi ne?”.
Kai ta jujjuya mata alamar a'a ba tare da ta kuma cewa komaiba.
Amsar jakar yayi daga hannun Samira.
Kana ya buɗe tare da ɗauko wani goran man shanu.
“Sauƙo ƙasa ki zauna ko”.
Ya faɗawa Fariyda yana ɗan ƙara matsawa.
A hankali ta zame ta zauna a ƙasa tare da jingina kanta a sawun Goggo Dada.
Hannunsa yasa tallabe hannun nata, da sauri ta rumtse idonta tare da yarfa ɗaya hannun tace.
“Washhhhh”.
Kusan a tare suka fara mata sannu.
Da sauri Ummi ta kauda kanta tare da miƙewa ta koma can gefe saboda ganin yadda ya fara jujjuya hannun tare da murɗawa a hankali.
Wani irin gigitaccen ƙaran mai bayyana azabar da takeji ta saki da ƙarfi tare da cakumo sawun Goggo Dada lakacin da taji ya fizge hannun da masifan ƙarfi har saida ya bada sautin ƙas....
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin ne 1k ne zaki turo ta nan 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276 mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 15
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗine 1k zaki turo ta nan 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa, mutanen Niger ku kuma 1000cfa ne +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*
“Wayyo! Wayyo!! Wayyooi!!! Allah na wayyoo Mamy na, Ummi hannun zai ɓalle Goggo Dada kice ya sakeni wayyoo”.
Kar-kar jikinta ke rawa tamkar mazari, duk da sanyin weather ɗin farkon damuna da ɗan AC da ke aiki bai hanata jiƙewa da zufa.
Ummi kam tuni ta bar wurin dan bazata iya ganin abin tausayin nan ba. Goggo Dada kuwa tuni idonta ya cika da hawaye.
Sai kuma Samira dake.
“Sannu Aunty Fariyda Baba kayi mata a hankali fa”.
Ƙara jan hannun yayi a ƙaro na biyu tare da fizgeshi.
Ihun da ta saki tare da miƙewa tsaye da fitsarin da ya ɗan subce mata duk a tare suka taho mata.
Da sauri Goggo ta yunƙura dan kamo hannunta ta zaunar da ita. Yana haɗa jakar tasa yace.
“A'a barta ai na kammala, yanzu man shanun nan za a rinƙa shafawa hannun safe da yamma na kwana uku shike nan”.
Wani irin kallo ya watsa mata lokacin da ya iso tsakiyar parlour rungume dasu Zaitoon kan kujera ya zaunar dasu yana watsa mata kallon da yasashi ganin karkarwar da jikinta keyi da zufar dake tsatstsafo mata sai kuma idanunta data zare
Ƙasan sawunta ya kalla.
Baki ya taɓe tare da tsuke fuska sai kuma ya kalli Goggo Dada tare da cewa.
“Goggo Dada sai ku samu a wanke muku gidan nan baki ɗaya, yarinya duk tabi ta barbaɗa mana najasar fitsarin a gida.”
Daga haka yasa kai ya fice.
Ita kuwa Fariyda da sauri ta sunkuyar da kanta cike da tsoro tabbas kuwa fitsarin ya ɗan ɗisa kaɗan-kaɗan.
Hamdala tayi ganin ba gaurayen jini kasan cewar daran jiya ya dawo mata ɗan ɗis-ɗis zai rinƙa zuwa mata sai bayan 24 hrs ne zai fara zuba da yawa.
Wani irin kunya ne ya rufeta wanda ke tafe da tsanarsa da ganin asalin muguwar zuciyarsa.
Goggo Dada ne ta bishi da kallon mmki dan shi tama mance yana gidan ashe duk abin nan da ake yana nan amman ko ƙala bai ceba.
Shi kuwa Baba idi yi yayi kamar baiji abinda Mahmoud ya faɗa gabanta ya tsaya tare da cewa.
“Ɗaga hannun mu gani”.
Da mamaki take kallon hannun nata ganin ta ɗagashi cak ba zogi.
“rufe tafin hannun ki buɗe mu ganin”.
Nan ma tayi ba matsala.
Ɗorashi a kanki ki maidashi baya ki dawo dashi gaba mu ganan”. nan ma ba matsala, murmushi tayi tare da sauƙe ajiyan zuciya kana tace.
“Baba idi Ngd wlh ya warke kaɗan-kaɗan nake jin zafin sai nauyi kaɗan”.
Kai ya jinjina cikin gamsuwa yace.
"To Alhamdulillah suma duk zasu bari yanzu yi kamar zakici abinci da hannun mu gani”.
Da sauri ta gwada ba matsala.
Goggo Dada da Ummi da jin shirune yasa fitowa suka hada baki wurin cewa.
“Kai Alhamdulillah Barka, sannu Fariyda, Allah ya kiyaye gaba”.
Amin tace tare da juyawa ta nufi ɗakin Goggo Dada tana cewa.
“Yanzu kam bari inje inji wanka”.
Murmushi sukayi tare da yiwa Baba idi godiya.
Kana ya juya ya fita yana.
Allah ya tsare gaba.
Samira kuwa moping ɗin wurin da Fariyda ta tsaya tayi.
Kai Goggo Dada ta jinjina tare da kallon Zaid da yayi bacci a zaune kwantar da shi tayi ta sauƙo da Zaitoon da take wasanta.
“Kai Babana dai halinsa sai shi duk abin nanfa da akeyi yana nan amman ko ya kula kamar ma daɗi yaji dataji ciwon”.
Ummi tace.
“In nace muku ya iya mugunta ai bakwa yarda kuyi ta kareshi”.
Ita kuwa Fariyda wanka tayi sosai duk da dai tana bin hannun a hankali bayan ta fito ne.
Ta kalli Samira data shigo mata da akwatunanta ta jerasu gefe gado sunyi reras.
Kan kujera ta zauna tare da jawo hand bag ɗinta ta fidda manta ta ɗan shafa tare da shafa kulacca sannan tasa Samira ta ciro mata wata tattausar Egypt Abaya yar cafal dai-dai da cikinta.
Tabi bayan Samira data fita tana ce mata.
“Ummi tace in kin gama ki fito kiyi breakfast”.
Da yamma cin ranar gab magrib.
Da sauri Daddyn Hafiz ya shigo cikin parlour Amina, zaune ya sameta ta tallabe haɓarta tayi gum tana kallonshi yana surfa mata faɗa tamkar zai kai mata mari, da alamu kanta yake son sauƙe fushinsa da fusatarsa da iyayensan suka rakito.
“Ba wani kin sani ɓoye min kikayi, da yake kin iya munafurci.
Ta yaya zakiji suna batun wai za'ayi min aure ki gagara faɗa min. Auren ma a rasa da wacce za'ayi min a duk faɗin duniyar nan sai waccar abar.”
Yana mgnar ne da iyakar gskyarsa da ɓacin rai fuskar nan tai jazir dan zafin zuciya.
Daddyn Hafiz ne ya ɗan dafa kafaɗarsa tare da cewa.
“Kayi haƙuri Mahmoud zauna muyi magna nasan zaka fahimceni in kaji manufar yin aure”.
Kanshi ya jujjuya ido cike da ɓacin rai yace.
“Nace musu ina buƙatar mace a rayuwata ne? Ban gaya musu bafa, ko sun manta matsala tace Daddy Hafiz, ba mace a ƙaddarata kuma sunfi kowa sanin hakan tunda duk abinda ya faru ka sani sun sani, ajema ace inada damar yin aure a rayuwata nifa namiji ne ta yaya zasu auramin duk karikicen da suke so.
Nafa tsaneta! Bana sonta! Ba kuma zan taɓa sonta ba har gaban abadan! Tunda kuma ta yarda aka aura min ita wlh zata yabawa aya zaƙinta! Jikinta zai gaya mata bayan targaɗe sai na karairayata na watsa a dozbin”.
Da sauri y kalli Amina dake cewa.
“Wlh kada ka ɗauki alhaƙinta itama Fariyda bata so, bata sani bama akayi auren nan yadda baka saniba itama bata saniba, wlh ita da taji wai an ɗaura mata aure da kaima har suma tayi”.
A fusace yace.
“To ai da mutuwa kawai tayi ma ba sumaba, kinga da ta mutu da kowa ma ya huta, zata wani suma ta farfaɗo dan munafurci to wlh bata kai ta haɗani da iyayena ba”.
Ya ƙare maganar tare da watsa mata kallon takaici dan gani yake ta sani ta ɓoye mishi.
Da kyar Daddyn Hafiz ya zaunar dashi tare da miƙa mishi ruwan da Amina ta ajiye masa, amsar goran yayi tare da ajiye wa, sai kuma ya miƙe tsaye ya nufi hanyar fita da sauri Daddyn Hafiz ya mara masa baya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.