Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 69 of 86

A garding É—in hotel ya zauna kan kujerun dake jere. Kanshi ya É—aura kan tafukan hannunsu daya shimfiÉ—e ta baya bisa kujerar da tafi kama da gado.
Nazari yake yi da tunanin mafitar da ya yake a ransa duk da rashin abokin shawara, yess ba abokin shawara tunda bazai taɓa zuwarwa Abba da wannan mgnarba numfashi mai nauyi ya fesar tare dayin mgna a saman lips ɗin shi.
Da Salim ya kamata yayi shawara amman yasan banzan bashi da sirri, Sulaiman ne ya faÉ—o masa a rai, da sauri ya buÉ—e idonsa jin sautin wayarsa, ga mamakinsa Sulaiman É—in ne.
Ido ya zuba wa wayar har kiran ya katse bai É—aukaba yana nazarin ta ina zai fara gaya masa, tabbas yasan Sulaiman yana da nitsuwa da fahimtar kuma in ya gargaÉ—eshi bazai faÉ—aba dan shi mutum ne mai sirri.
Ganin kiran ya kuma shiga ne yasa yayi picking call É—in.
Cikin sanyi Sulaiman yace. “Kun isa lfy, ya Zaid da jiki”. Yana mai ɗan nazari yace.
“Alhamdulillah“.
Yana ɗan miƙewa kwance yace.
“Ina Madam”. Cikin sauƙe numfashi yace.
“Tana ciki”. Sai kuma ya ɗan ja tsaki ganin kiran Sa'ad ya kuma shigowa a wayar Yah Amin ɗin.
“Lfy kuwa naji kana tsaki?”.
Sulaiman ya tambaya cikin nitsuwarsa da sanyin hankali, kai tsaye yace. “Wani yarone muka haɗu dashi a Airport yana son wannan yarinyar shine ta bashi number ya Amin yake ta uzzura min da kira tun ɗazu nace masa bana gida”. Cikin zare ido da sauri Sulaiman yace.
“Bazaka ci ubansa ba”.
Yana gyara zama yace.
“Akan me zanci ubansa?”.
Cike da mmki yace.
“Akan matarka mana da yace yana so, shi mahaukacin inane”. A kufule yace.
"Kaine dai mahaukacin da kake kiranta matata, shi da hankalinsa, ta yaya ma zan zageshi ni da nake farin cikin zai rabani da ƙaya”.
Sake baki Sulaiman yayi ya kasa cewa komai yana sauraron Mahmoud dake ci gaba da ce masa.
“Ni dama auren nan bai ɗauruba a wurina, yanzu kuma tunda munzo nan wani ya yaba zai aurenta, Wlh ni zan bashi ita kai kuma kayi mata walicci dan yace min shi ɗan Gombe ne, sai an ɗaura auren kafin in gayawa su Abba ni na saketa, kuma na aurar da ita ga Sa'ad ɗin dan naga da gaske yake gashi da naci kamar maye”.
Ajiyan zuciya mai ƙarfi Sulaiman ya sauƙe tare da cewa.
“Ni na isa ayi haka dani, tab ai bani da wannan karfin zuciya da tsaurin idon wannan sai kai Oga Mahmoud”.
Cikin sauri yace.
"Ai dole zakayi kuma bance ka faɗawa kowa tsarina ba, har wannan surutaccen Salim kasan ba kaine dashi ba zai iya zuwa ya faɗawa Abba”. Cikin natsuwa Sulaiman yace. “Faɗa kam ba wanda zan faɗawa, to ta inama zan fara faɗar wannan SAƘAR MAKAFI da kake son saƙawa, amman yi dai kam yaseen bada niba”.
Cikin tabbatar wa yace.
"Zafa kayi Sulaiman wlh sai mun ɗaura mata aure, mu biyu ko bata so sai na aura mata shi, bare ma itace fa da kanta ta bashi number Yah Amin”.
Sulaiman yace.
“Nifa tsoro kake bani Mahmoud anya akwai wani abu wai shi tsoro a zuciyarka kuwa? Shin wai dama har ƙiyayyar da kakeyiwa Fariyda ta kai haka ne, matarkafa kake son tayi zance da wani kuma har kake ƙoƙarin ɗaura mata aure to wai ma ina makomar aurenku”.
Cikin faÉ—a yace.
"In ka ƙara ce mata matata wlh ubanka zanci, ai nace maka zan saketa ko”.
Ita kuwa Fariyda Jiki na rawa ta fara cikin Cookies da suka kawo mata kafin su dafa mata abincin data zaɓan.
Ci take yi tana share ƙwalla da yaƙi tsaya mata.
Shi kuwa Mahmoud a takaice yake cewa Sulaiman daya tambaye shi kana ina yanzu.
“Bar ƴan iska daki ɗaya suka bamu, da naje wai ai ni na zaɓa kuma wannan ne side ɗin ma'aurata masu yara, wai kuma ma kwanan nan zasuyi taron Asian Children Pediatrician, hotels ɗin a cike yake, na duba wasuma duk kusan baƙi sun cika garin, shiyasa duk a takure nake”.
Murmushi Sulaiman yayi yace. "To dan Allah me a ciki dan ka zauna da ita ɗaki ɗaya kace ma room and Parlour ne ai ba takura kuma ko dan su Zaid ai gwara ka kasance kusa dasu dan kasan halin da yake ciki”.
Haushin yadda Sulaiman bai fahimci yadda ya tsani ganin ta bane ya sashi katse kiran.
A matsallacin dake cikin hotel ɗin yayi sallan la'asar tare da zama har magrib da isha saida yayi a ciki. Kana ya miƙe daga nan kitchen ɗin ya wuce. Tea kaɗai yasha ya amsawa su Zaid Custard da yasa aka dama musu.
Ido ya zuba wa wayar lokacin da ya shigo cikin parlour kiran Sa'ad na biyar ya kuma shiga, cilla mata wayar yayi gefenta, da sauri ta tashi zaune tare da kallonsa sai kuma ta kalli wayar.
"Akan me zaki bawa wancan mayen number Yah Amin, meyasa bazaki bashi number ki ba ku gama shirmenku in ya bada sadaki in ɗaura muku aure”.
Cikin wani irin kallon mai cike da mmki tace.
“Waye”. Yana ajiye flacks ɗin yace.
“Kiyi picking call ɗin ai zakiji wanda kika bawa number”. Da sauri ta ɗauki wayar tare da karawa a kunne, da sauri ta kallesa ganin ya jawo su Zaid yana basu Custard ɗin.
“Hello my princess kiyi mgna inji muryarki ko zan samu nitsuwar dana rasa tun bayan rabuwarmu”. Da sauri ta juyo tana kallonshi, tare da kallon wayar da ta tabbatar shima zai ɗanji me Sa'ad ke faɗa, cikin sanyi tace.
“Wake mgna”. Cikin tausasa murya yace.
“Mijinki ne in sha Allah, kin tuna Ethiopia wurin yin transit”.
Ido ta É—an lumshe tare da cewa.
“Afwan na tuna Sa'ad ko”.
Cikin jin dadi yace.
“Yess Baby ya kike ya Ahmedabad ɗin ya miki daɗi, ko bai mikiba inzo insa yayi miki daɗi”. Cikin sanyi tace.
"Hakama ya wadatar ai, iya jin muryarka ma zai sani duk wani jin daɗi da farin ciki”. da sauri ta kalli Mahmoud da ya...........

https://arewapen.com/u/garkuwa

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 33
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Ya miƙe hannunsa ya zaro tissue ya goge musu bakinsu, ba tare da ya kalli inda takeba.
Ya wuce bedroom riƙe da wata tattausar jallabiya a hannunsa.
A bedroom ɗin ya ɗan tsaya bayan ya fito wanka cikin shirin baccinsa wurin gadon su Zaid ɗin ya nufa tare da gyara musu tarkacen toy nasu dake baje ya saƙalasu inda akayi dominsu labulayen ya kuma ja ya killace wurin yayi lub-lub gudun Ac ya ɗan ƙara.
Yana fitowa parlour ana Knocking ya buÉ—e ya amshi blanket da yasa su kawo mishi, numfashi ya É—an fesar saboda gamsuwa da tsabtan komai na hotel É—in yayi masa É—ari bisa É—ari.
Har lau wayar takeyi.
Zaitoon ya fara É—auka ya kaita bedroom É—in kana ya dawo ya É—auki Zaid É—in ma, addu'a yayi musu ya shafa musu, sannan ya wore baby blanket É—in dake ninke gefen gadon nasu ya rufesu lib.
Labulayen ya kuma gyara musu yadda sanyin bazai damesu sosai ba.
Parlour ya dawo tare da tsayawa a gaban TV ya canza channel É—in da take kallo na Bollywood sai kuma ya kashe wutan parlour.
Gefenta ya É—an kalla fuska a tsuke ya nuna mata hanyar bedroom da É—an yatsarsa, kai ta É—an jujjuya cikin sanyin murya da baya jin me take faÉ—a dan bai maida hankali kantaba bai kuma daku da jin me take faÉ—an ba da kuma neman da wa take wayar da Sa'ad É—in ne ko da wani.
Da hannu ya sake nuna mata hanya yana mai zama, saboda kallon Wrestling dan da jaruminsa ake gobzawa.
Tsaki ta ɗan ja ta miƙewa tsaye tana mai lumshe idanunta ta nufi bedroom ɗin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.