Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 86

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 5
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set É—in kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set É—in hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
HaÉ—ine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.

Idan kin sayi kaya in dai set É—in kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuÉ—in Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.

0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

“Dan Allah Ummi ki yafe masa, kinsan wannan binkin da yake yi da kama mayafinki nemar yafiyarsa ce a haka bazai ce ki yafe ɗin da bakiba”.
Da sauri tace.
“Eh na sani, ai nasan shi ɗan iskane da yafi ƙarfin ya buɗi baki ya bamu haƙuri mu iyayen da muka haifesa ma tun yana yaro har yanzu da ya kamata ace yayi hankalin da badan ƙaddararsa ba da shima yana da mata da ƴa ko ɗa, Amman bai taɓa buɗar baki yace mu yafe masa ba dani da mahifinku sai dai yayi ta bibiyarmu kamar inuwa ai gskiyar Fariyda shi ɗin mai girman kaine!”.
Cikin sanyi da rauni da fargabar yasan shikenan wutar ƙiyayya da gaba tsakanin ƙaninsa da matarsa zai tumɓasa fiye da baya yace.
“Dan Allah Ummi ki daina faɗin haka, nima da nake yaya a garesa yaushe yayi min laifin bare ku iyayenmu, Mahmoud baya shiga harka wani baya son a shiga tasa.
Muyi mishi uzuri itama Fariyda bata kyautaba na hanata shiga maganar da duk tasan akwai sunan Mahmoud a ciki Amman taƙi bari”.
Juyawa tayi ta dawo parlour.
Da sauri ya kuma juyawa shima ya bita a baya gaban kujerar data zauna ya durƙusa, tare da yin ƙasa da idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir sai jijiyoyin kansa da suka taso sama sukayi ruɗu-ruɗu More Especially na goshinsa.

Goggo Dada ce ta miƙe cikin sanyi ta nufi Dinnin area.
Ruwan sanyi ta É—auko mata.
Amsar bottle water din Ummi tayi tare da balle marfin ta kai bakinta, sai da ta sha fiye da rabi kana ta ajiye, tana sauke numfashi jin zafin da ƙirjinta keyi ya ɗan ragu.
Sai kuma ta miƙe tsaye tare da buge hannunsa dake dafe da kujerar da sauri ta nufi bedroom ɗinta tare da faɗin.
“Wlh in ka biyoni sai na faɗawa Abbanku yayi min iyaka da kai.”
Dai-dai lokacin kuma Zaitoon dake kwance kan 3 seatter tana wutsulniya tayi kasa ihu data sakine ya maida hankalinsu kanta kuma shi ya dakatar da shi daka dukkan yunƙurin bin Ummui.
Da sauri ya ɗauketa tare da rungumeta ya miƙi tsaye yana shafa kanta fuska ɗauke da hargitsin yanayi.
Aunty Amina da Goggo Dada kuwa ido suka zuba mishi suna karantar tsananin son da yakeyiwa yaran É—an uwan nasa, wanda ke bayyane a fuskarsa duk da abinda ke faruwa.
Cikin lumshe ido Aminullah ya miƙawa Jidda hannu tare da cewa.
“Jidda kawo Zaid amshi Zaitoon ki kaita ayi feeding ɗinta”.
Sai lokacin Jidda dake jin tamkar ita aka mara tayi saurin miƙawa Aminullah ɗin Zaitoon sai kuma ta nufi gaban Mahmoud ɗin tare da miƙa mishi hannu.
Da sauri ta rumtse idonta saboda jin yadda ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari da bayan hannunsa kan ta dawo daga gigin zogin marin forkon ya kuma yarfa mata na biyu da cikin tafin hannunsa.
Tare da cewa.
“Ki haɗiye kukanki kamar yadda kika zauna kina kallon gulma, munafuka mai kan angulu maza amsheta”.
Cikin sanyi lips da murya na rawa tace.
“In dai haka zai sa kaji sanyin a zuciyarka na yarda Yah Mahmoud kayi ta marina har sai kaji zuciyar tayi sanyi ka huce”.
Ta dire mgnar tare da juya mai gefen damanta, tana mai amsar Zaitoon É—in kuma.
Da sauri Aminullah ya riƙe hannunsa ganin ya ɗago hannun zai kuma watsa mata wani marin.
Goggo Dada ce ta kalli Jidda cikin son fahimtar matsayin Mahmoud É—in a zuciyar Æ´ar É—an uwanta tace.
“Maza Jidda jeki, kinga Zaitoon na kuka”.
Hawaye na zubo mata murya na cike da rauni da so mai zafi tace.
“Goggo Dada kiyi haƙuri bari in tsaya ya mareni duk iya adadin da yake so, saboda hucewar zuciyarsa.
Ya mareni kawai zaifin jin sauƙin zogin da nakeji a zuciyata akan marin da Ummi tayi mishi, wlh da ina da dama ko kuda bazan bari ta taɓa Yah Mahmoud ba bare mari, to amman hannun da yafi ko wanne hannu darajane a garemu ne ya mareshi.
Ni kuwa in ya rama a kaina da hannunsa tamkar nasarace a rayuwata”.
Da sauri Aunty Amina ta shiga tsakaninsu dan ganin yadda ya yinƙuro zai mata shaƙar mutuwa”.
Goggo Dada kuwa kai ta jinjina fahimtar tsananin son da Jidda keyiwa Mahmoud ɗin ne yasata jin mutuwar jiki, da ace ba ƙaddarar Mahmoud da sunyi farin ciki da wannan haɗin, jiki a sanyaye ta koma ta zauna.
Aminullah kuwa hanya ya nunawa Jidda wanda hakan yasa ta nufi part É—in sa.

Hafiz kuwa tunda yayi ƙasa da kansa bai ɗagoba sai yanzu da yabi Jidda da kallon fahimtar zazzafar ƙaunar da takewa Uncle ɗin nasa a kalamanta.
Aunty Amina kuwa hannun Mahmoud É—in taja ta zaunar dashi.

Shi kuwa Aminullah bayan Jidda yabi da Zaid da shima ya fara kuka.

Wunin ranar dai haka ya kaya ba daÉ—i.

Washe gari da asuba.
A hankali Ummi ta tura ƙofar bedroom ɗinta kasan cewar a turakan Abba ta kwana.
Zaune ta sameshi bisa sallaya da alamun nafilar bayan fitowar rana yake yi. Juyawa tayi ta wuce parlour inda ta jiyo Motsin Fariyda da Samira a kitchen.
“Barka da safiya Ummi”.
Fariyda ta faɗi tana ƙasa da kanta cikin girmamawa mai haɗe da son uwar mijin nata so na gaskya.
A hankali Ummi ta matso kusa da ita hannu tasa ta tallabo haɓarta tare da zubawa fuskantar ido.
“Me Aminullah yayi Miki?”.
Da sauri ta fara girgiza kanta murya cike da biyayya tace.
“A'a Ummi ba abinda yayi min”. Tana kallon fuskarta da manyan idanunta da sukayi lub-lub alamun tayi kuka tace.
“To meyasaki kuka?”.
Tana ɗan murmushi tace. “Allah kuwa Ummi ba abinda ya min, kin san Yah Amin me zai min, kawai dai ya bani tausayi ne, ya kasa bacci yana jaddada min irin son da yake wa Mahmoud kawai dai yace min ban kyauta masaba.
Ni kuwa ganin yadda ransa ya ɓacine yasa na kasa tsaida hawayena amman nayi ta bashi haƙuri.
Kuma dan Allah Ummi kema kiyi haƙuri ki yafen min in sha Allah bazan sake shiga zabgar Mahmoud ba”.
Kai Ummi ta jujjuya mata tare da cewa.
“Ni baki min komaiba Fariyda ai ke zan bawa haƙuri, in kuma roƙeki da girman Allah kada ki gayawa iyayenmu abinda Mahmoud yayi miki, sannan kuma dole kiyi mgna a kan Mahmoud tunda matsayin ƙani yake a gareki”.
Cikin sauri tace.
“In sha Allah Ummi bazan gayawa iyayena ba, ai wannan sirrin gidanane kuma ni baki min komai ba, ki yafe min Yah Amin yace min tun suna yara ke ba uwace mai dukaba sabida suma ba yare kwaramniya ba, amman a kaina jiya kin mari Mahmoud shine abinda ya hanasa bacci, Dan Allah Ummi ki tayani bawa Yah Amin haƙuri dan Allah ya yafe min, bana son yayi fushi dani”.
Shafa kanta Ummi tayi tace.
“Allah yayi miki al'barka ƴata, kada ki damu Aminullah bazaiyi fushi da keba zuciyarsa mai taushice da saurin yafiya”.
Cikin farin cikin son da uwar mijin nata keyi mata, ta amsa da Amin tare da haÉ—a mata tray É—in kayan tea É—in Abba da cups biyar dan tasan duk bayan sallan asuba tare suka shan tea a parlour Abba da Ummi Goggo Dada da Aminullah da shi Ayagi Sarkin rashin mutuncin in yana nan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.