Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 45 of 86

Ƙarfe shida dai-dai ya fito office ɗin bayan yayi alwalar magrib
Wayarsa dake Vibrate ya zaro daga aljihu ganin Abba ne yasashi yin picking call.
“Barka da yamma Abba”.
Abba yace.
“Barka dai. Da safen ka biya ka duba surkin naka da jikin?”.
Ɗan jim yayi har Saida Abba ya kuma masa tambayar cikin rashin mafita yace.
“A'a Abba amman yanzu in nayi magrib da isha zan biya in dubashi”.
Cikin bada umarni yace.
“Kada ka dawo gida har sai ka biya ka dubashi”.

Bayan sallan isha Baba Malam ne ya zubawa himilin kayan masarufi nasu na masu ciwon suger da Mahmoud ɗin yazo dashi ya bawa Sadiq car key ɗinsa suka rinƙa shigo dashi kama daga.
Pure Basmati rice semolina macaroni, indomie manyan gongonayen madarar da sugan masu cutar sugar da break ɗinsu sai drinks ɗinsu katon biyar.
Baba Malam yace.
“Wannan hidima ai tayi yawa Mahmoud”.
Kai ya ɗan sunkuyar cikin girmamawa yace...

*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo Evidence ɗin ki 09097853276. Mutanen kasar Niger 1000cfa +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAƘAR MAKAFI*
Page 18
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

“Malam asa min al'barka”.
Murmushi yayi tare da cewa.
"To Allah yayi maka al'barka ya tsare gabanka da bayanka ya baka zuriya ɗayyiba da zaman lfy cike da arziƙi ya raya musu yaranku”.
A hankali ya amsa da Amin dan addu'a akwai wanda yaji daɗinsu.
Baba Malam ya kuma cewa.
“Ya business ɗin naku dai, zuwa yanzu dai ai ka gama dai-daita komai ko”. Mahmoud yace.
“Eh Alhamdulillah”.
Yana mai kallon yadda yake nitse a gabansa tare da bashi amsa cikin girmamawa yace.
“Abbanka yace min zaka je Egypt yaushe ne tafiyar”.
Ba tare da ya ɗago kansa ba yace.
“In sha Allah ranar Thursday zan tafi abuja da safe, da yamma zamu wuce”.
Malam yace.
“Yau saura kwana huɗu kenan tafiyar”.
Kai ya gyaɗa masa
“Allah ya bada Sa'a ya kaiku lfy ya dawo daku lfy”. Da Amin Ya amsa.
Shi kuwa Malam,
Ido ya zuba wa su Adda Nana da Hadiza da Fariyda da Raihana da suka shigo yi masa Saida safe.
Bayan sun gaisa da Mahmoud ne suka yiwa Baba Malam Allah ƙara lfy da saida safe.
Zaid dake hannun Hadiza ne ya zame tare da zuwa wurinsa rungumesa yayi yana dariya da tafi.
Zaitoon dake bacci gefen Malam ɗin ne ta buɗe ido da sauri ta tashi zaune, ba tare da baccin ya gama saketaba ta rarrafa zuwa gaban shi ta kwanta kan Mahmoud murmushi sukayi dukansu ganin shaƙuwar ta musamman ce.
“Fariyda maza ɗauki ɗaya ku tafi kada dare yayi tsawo”. Cewar Baba Malam. Hadiza ne ta miƙe tare da cewa.
“Adda Nana mu tafi ko kice Adam ba sai yazo ɗaukarkiba zamu kaiki gida”.
Da sauri duk suka miƙe tare da cewa saida safe.
Shi kuwa Malam Fariyda dake durƙushe har yanzu yace.
"Tashi maza ku tafi”. A hankali tace
“Malam jakata da takalman su Zaid suna cikin gida”.
Baba yace.
“Raihana tashi ki ɗauko musu shi”.
Da sauri Raihana ta fita.
Shi kuwa Mahmoud so yake ya miƙe ya tafi amman tunanin yadda zai maida laifin kanta yake shiyasa bai tashi ba. Dawowar Raihana ne yasa ya miƙe.
Rungume dasu Zaitoon duka biyu.
Itama Fariyda miƙewa tayi dan jin yadda Malam yace maza tashi.
A bakin ƙofa suka haɗu da Mamy wacce yau itace a wurin Malam ɗin cikin ɗan girmamawa yace.
“Sai da safe”.
Mamy tace.
“To Mahmoud Allah ya bamu alkhairi a gaida gida”.
Tayi magnar tana shafa kan Zaitoon tana kallon Fariyda da ta fito ido kamar zai zubda ƙwalla tace.
“Kuje dare yayi fa”.
A hankali tabi bayansa ganin Mamy taƙi shiga ta tsaya kallonsu.
Sai da suka fita daga side ɗin kewayen Baba Malam ɗin ta shiga parlournsa.

Front seat ya buɗe tare da ajiye su kan kujerar.
Kana ya maida marfin ya rufe tare da zagayawa ta gaban motar ya buɗe driver seat ya shiga.

A hankali ta buɗe back seat ta shiga tare da maida marfin gib ta rufe da a hankali kamar munafuka tayi ƙasa da kanta.
Zamansa ya gyara tare da kunna haske cikin gaban motar ya ɗan haska musu.
Da sauri suka rarrafo kansa kansu ya shafa tare da fara kissing Cheek dinsu
Sai kuma ya ɗan lakaci hancin su.
Baki ta ɗan tura ganin yaƙi ya tada motar kuma ko juyowa ya kalli inda take baiyiba bare yace mata ƙala.
Dariya sosai su Zaid keyi suna wasa da abubuwan gaban motar.
Ɗan gajeren tsaki taja lokacin da ta duba time a wayarta a ƙalla sun kai 16 minute a zaune.
Cikin sanyi tace.
“Mutafi”. Tsaki mai wasali yaja tare da tsuke fuska murya a dake yace.
"Sai ki nemo wanda ya kawoki yazo ya ɗaukeki, ko an gaya miki mota ta ta shigar ko wanne tarkacene, fice min da gani kar in fasa bakin rashin kunyar”.
Da sauri ta fice tare da maida ƙotar ta rufe gib, ta juya ta nufi cikin gida, shi kuwa tana rufe kofar yasa wa su Zaid seat belt.
Saida ya tabbatar ta isa cikin gidan.
Ya figi motarsa ya bar gidan.

“Ya dai”. Raihana ta faɗa tare da zuba mata ido ganin shigowarta da maida ƙofar ɗakinsu ta rufe duk a tare.
Ido ta zuba mata ganin ta ajiye hand bag ɗinta tare da ninke gyalenta ta ajiye kan bang ɗin nata.
“Lfy dai kam”.
Baki ta taɓe tare da shigewa bathroom ta
Wanka tayi da alwalar kwanciya.
Ido Raihana ta kuma zura mata ganin ta zaro rigar bacci cikin kayanta, da ido tai ta binta har ta gama shiryawa ta zauna bakin gadon.
Numfashi mai sanyi ta shaƙa da ƙamshi turrenta tace.
“Wai meke faruwa ne? Ba kun tafi ba”.
Fuska ta kwaɓe cikin takaici tace.
“Sun tafi dai, haka kawai dan an sali dole na shiga motarsa shine zai min wulaƙancin, motar nan dai nima ina da ita Malam ne ya hanani driving tunda Yah Amin ya saya min, kuma har yau tana zaune key ɗinta ma na hannuna, in ba don Malam shima yasan bazan kula motarshi da yake jinta kamar ransa ba, motace ba mutum ba sai dokoƙintsiya da ƙa'ida an wani cikata da masifar ƙamshi kamar shagon saida turare”.
Raihana tace.
“To ina su Zaid?”. Tana zaro wayarta tace.
“Waya san masa, inaga ya tafi dasu”.
Da sauri tace.
“Bazasuyi kuka ba”.
Cikin takaici tace.
“Suma ɗaya da suke wani sonshi in suna tare dashi kamar sun samu ubansu, koni basa kulani, bare kuma dama in dai sunyi bacci ko sau ɗaya basa tashi sai har kusan 6 to 7 duk yabi ya kalallamemin yara dan mugun nufin rabani dasu, yaje mu gani zuwa safe dai dole zasu buƙaci ni ai”.
Cikin natsuwa Raihana tace.
“To Amman meyasa kika fito bayan har kin shiga motar”.
Kai ta gauda tace.
"Ƙin tada motar yayi fa, mukayi ta zama ya wani manna min hauka, shidasu Zaid suna ta harkarsu da nace to mu tafi mana shine yace min in fice msa daga mota in nemi wanda ya kawoni ya maidani”.
A hankali tace.
“Kenan bada izininsa ba kika zo”. Harara ta watsa mata cikin faɗa tace.
“Wlh yayi kaɗan”.
Daga nan ta kwanta tare da kashe wayarta.
A can gidan kuwa Ummi tace.
“Fariyda har yanzu shiru”. Goggo Dada tace.
"Dama ai cemin tayi kwana zatayi”.
Ummi tace.
“Ayyah to Allah ya kaimu gobe lfy, da yau da gobe ai duk ɗaya ne.”
Washe gari da asuba, da wuri ya dawo masallaci, da ɗan sassarfa ya hausara sama, yana buɗe ƙofar suna buɗe ido a tare.
Da sauri ya ƙarasa wurinsu,
Ɗaukarsu yayi ya saɓa a kafaɗa kana ya juya ya fito.
Tura ƙofar parlour yayi yana kutsa kai ciki. Alamun Maman Samira ta shigo dan fara aikin breakfast.
Shiru parlour ba kowa, haka yasa ya wuce ɗakin Goggo Dada.
Da sauri ta juyo tare da amsa sallamarsa, sai kuma ta miƙe tsaye tare da fara ninke hijabin sallanta tana faɗin.
“A'a daga ina haka, yaushe suka dawo”.
Kan kujera ya zauna bayan ta karɓi Zaitoon.
“Yaushe suka dawo”. Ta kuma tambaya ganin bai bata amsa ba sai gaisuwa daya ɗaga mata, kai ya ɗan kauda daga ganin kallon tambaya da take masa.
“Tare na dawo dasu jiya da dare”.
Tana zama gefen gado tace. “To Fariyda fa”.
Mikewa tsaye yayi tare da miƙa mata Zaid yace.
“Tana gidansu, Goggo Dada ayi musu wanka a basu Cerelac ɗinsu, ko indomie duk da abinda sukeso”.
Tana kallonsa cike da mmki tace.
“Tana gidansu kuma ka dawo dasu Zaid, ta ya akayi haka”.
Fuska ya ɗan ya mutsa tare da cewa.
" I don't know ta dai ce bazata dawoba ta barmin yaran”.
Daga nan ya fice.
Baki ta saki tare da rakasa da ido.
Eh lallai akwai aiki babba a wannan zaman auren, yess ta san tabbas Fariyda zata iya faɗin hakan tunda ba ƙaunarsa takeba shima kuma zai iya tata mata rashin mutunci”.
Ganin nazarin ba sama mata bakin zaren zayi bane ta miƙe ta fara yi musu wanka tare da kimtsasu sukayi ras dasu sai ƙamshi da sheƙi sukeyi.
Ta fito dasu parlour tare da amsar Cerelac ɗin da tasa Maman Samira ta dama musu kafin tai musu wanka, a gabansu ta ajiyesu tare da fara basu ɗaya bayan ɗaya in ta bawa wannan ta bawa wannan a haka har suka shanye fes.
Gyatsan da sukayi ne yasa bata kuma ƙara masu wani abun ba, daga nan kuma suka fara harkokinsu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.