Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 24 of 86
A can gidan Baba Malam kuwa tuni Raihana da Salma sun gama shiryawa Fariyda komai nata a bedroom ɗin dake gefen na Mamynta inda nan Raihana take kwana tunda tazo Hajja inna ma nan ta sauƙa inda tayi kwana biyar ta koma Gembu jiya.
Koda suka dawo nan ma sai gidan ya zama salam saboda ba wani farin ciki sosai a cikinsa.
Haka dai rayuwa tai-ta tafiya.
Har yau da akayi kwanaki arba'in cib da rasuwar Aminullah.
Zaune yake a parlour Baba Malam rungume dasu Zaitoon da suke ta maƙale wuyanshi suna zagayesa, sunanta dariya da Balankwace.
Yayinda Hafiz ke ta shigo da kayayyakin da suka yiwa su Zaid shopping.
Ido Baba Malam ya zuba musu ya gaza janye idonsa daga ganin shi da yaran É—an uwan nashi.
Mamaki yake yadda yaran ke tsananin shiga farin ciki in sun ga Mahmoud É—in.
Numfashi ya É—an fesar tare da kallon kayan masarufi da Hafiz ya gama jibgesu.
Kama daga madarar Naan Sugar Custard Cerelac Pampas and tissues omo sabulu set É—in baby shampoo and conditioner baby oil. Sai kuma cartons É—in Bobo indomie da pasta sai buhun shinkafa É—anye da gumi, kana da manyan gongonayen madara, da kuma set É—in rigunan sanyi na yara kusan kala biyar-biyar.
Cikin sauƙe numfashi Baba Malam ya fara girgiza kai.
“Mahmoudâ€.
Ya kirasa cikin kulawa cikin girmamawa ya amsa tare da zuba mishi ido. “Duk wannan kayan na menene haka? Hidimar tayi yawa, du-du yaushe ka turo Hafiz ya kawo kaya kamar haka, abin ko wata É—aya bai cikaba, sannan yanzuma ka kuma libgo kaya haka kada abin ya zama almabazzaranci fa, sannan kuma meyasa zaka rinÆ™a haÉ—owa da shinkafa yaranda iya karsu indomie sai abubuwan shansu da suka bawa mahimmanciâ€.
Cikin yin ƙasa da kanshi yana shafa fuskar Zaitoon yace.
“Baba Malam ai haƙƙin nane in kula da duk wasu buÆ™atarsu, bana son su buÆ™aci wani abu su rasa shi yasaâ€.
Da sauri yace.
“Ai duk abinda suka buÆ™ata zamuyi musuâ€.
Cikin sanyi yace.
“Bana son kowa yayi musu wani abu dan bana son su tashi su jisu kamar marayu, Malam tunda suna dani ba bukatar kowa ya taimaka musu a rayuwar nan.â€
Kai ya gyaÉ—a mishi cike da raunin da yasa idonsa na cikowa da hawaye.
Hafiz ne ya amshi Zaid dake ƙoƙarin tahowa wurinsa.
Zaman awa É—aya yayi da yaran da tunda suka dawo baizo ya gansuba sai yau sai dai duk ranar juma'a zaisa Hafiz ya É—aukosu suzo gida su wuni tare sai dare yake maidasu, bayan sun tafine.
Baba Malam ya kalli Mamyn Fariyda dake mamakin kayan da Mahmoud É—in ya kuma libgowa.
“Malam da dai an hanshi wannan hidimar tunda ba shi zai rinÆ™a ciyar da gidan nanba dan su Zaitoon na gidanâ€.
Kanta ta É—ago ta kalli mijin nata jin shiru bai tanka mata ba.
Idonsa da taga cike da hawaye ne yasa tace.
“Malam to kaima kenan yanzu in Fariyda ta iso ta samu kana Æ™walla ita kuma tayi yaya kenan?â€.
Murya cike da kamala yace.
“Wlh ina jin tausayin Aminina mahaifinsu Mahmoud yana bani tausayi ya rasa ɗansa, gashi Mahmoud kuma bashi da damar cike musu gurbin Aminullah.
Wlh da ace Mahmoud zai iya aure da tabbas zan aura masa Raihana taje ta riÆ™e Æ´aÆ´an yar uwarta, dan nasan Mahmoud bazai taÉ“a bar mana yaran nan ba, kuma suma iyayen nasa bazasu barin ba, dan yaran ne farin cikinsuâ€.
Kai ta jinjina cike da tausayawa tace.
“To ya zamuyi haka Allah ya tsara, ni kaina na tuna haka da ace Mahmoud zai yi aure da yaran Fariyda bazasuyi maraiciba Raihana zamu bashi ya aura su riÆ™e ya'yan tayunsu.â€
A can gida zaune gaban Abba yake yayi ƙasa da kansa.
Da sauri ya É—ago kansa ya kalli Mahmafin nasa jin yana faÉ—in.
“...
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta nan 09097853276, mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050 zakuyiwa magna.
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 9
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Assalamu alaikum jama'a ta jama'ar arziƙi fatan muna lfy ya gida da yaranmu.
Matan alkhairi mata masu duniya, akwai garaɓasa fa ta musamman da na watannan na maulud promo haɗine na musamman kashi da ban da ban, akwai naku na manyan mata, da kuma amare bazaaawara ko budurwa, da masu joge ɗanyen jego ko barden jego.
08069423567 gata inda zaku yi min magna ta WhatsApp,
Set É—in kayana mataki biyu ne.
Na forƙo daga 40k ne zuwa ƙasa shine ƙananan 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k Akwai Maganin Infection sadidan yar uwa ba haufi, shi kuma set 10k.
Sai kuma manyan set É—in hajia taho kiji daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k 120k 130k 140k sa sha kundum uban makiya 150k ne yar uwa.
HaÉ—ine na musamman.
Kana akwai kayayyakin turaren wuta dasu Humra da kulacca suma haka farashinsu yake.
Idan kin sayi kaya in dai set É—in kayanki yakai daga 50k 60k 70k 80k zan biya miki rabin kuÉ—in Delivery, daga 90k 100k 120k 130k 140k 150k to free delivery ne, Ni zan biya Miki.
0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.
Da sauri ya amsheta daga jikin mahaifiyar tasu, cikin abin bai gaza 3 minute ba ta farfaɗo ta hanyar bata numfashinsa cikin ƙwarwarsu ta likitoci.
Sai kuma ya kalli Amina da dake kuka tamkar zata shiÉ—e.
Cikin sanyi Yah kalli Barrister da yayi gyaran murya tare da fara maimaita.
Allahummma gafirlahu warahamhu.
Da ƙarfi-ƙarfi cikin ikon Allah duk sai suka kama.
Shiru parlour ya É—an nitsu.
Sai ajiyan zuciya da ake sauƙewa.
Dai-dai lokacin kuma Baba Malam ya shigo tare da bappa Lawan
Ahmad dake gefenshi yacewa.
“Ɗauko min ruwan sanyiâ€.
Yana sharce hawaye ya É—auko masa gorunan ruwan sanyi.
Da kanshi ya bawa Fariyda da ta fara wani irin numfashi.
Amsa tayi tasha kurɓa uku. Amina ya bawa, sai kuma ya miƙawa Ummi.
Idonshi ya zuwa Mahmoud da bai amshi goran da yake miƙa masaba kuma baice masa komaiba illa addu'a da yaketayiwa ɗan uwansa.
Sunkuyar da kai Baba Malam yayi murya na rawa ido na zubda Æ™walla yace. “Kuyi haÆ™uri Mahmoud muyi haÆ™uri, Allah ya jiÆ™an Aminullah yasa mutuwa hutune a garesa.â€
Dai-dai lokacin kuma Mama da Jidda suka shigo.
Suna shiga Jidda ta rungume Aunty Amina tare da fashewa da kuka. Da sauri Baba Malam ya miƙe ya kamo hannun Mahmoud tare da jawoshi suka fito. Bayan Goggo Dada ta amshi su Zaitoon.
A hankali Dr Nasir da Barrister da Ahmad suka mara masu baya.
Suna fita, Baba Malam ya ajiye shi kusa da Barrister, kana Ahmad da Nasir suka zauna gefenshi.
Cikin sanyi Baba Malam yace.
“Lawan muje ayiwa gawar sutura koâ€.
Ido na zubda ƙwalla shina ya miƙe suka fita.
Bayan an gamawa gasar duk abinda ya dace kamar yadda shariya ta tsara.
Aka ajiye ta a wurin ajiyar gawa na cikin masallacin.
“Ko zamu kai gawar Mahaifiyarsa da matarsa su kalleshiâ€.
Bappa Lawan ya faɗa yana kallon time ƙarfe ɗaya da kwata.
Kai Baba Malam ya jujjuya tare da cewa.
“Kai gawar cikin gidan zai Æ™ara hargitsasu gashi maÆ™ota da yan uwa sun cika gidanâ€.
Da sauri Malam liman ya gyaÉ—a kai tare da cewa.
“Gaskiya kam zasu rikiceâ€.
Sai kuma duk suka kalli cikin Masallacin jin man ladan ya kira sallan azahar.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.