Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 74 of 86

Kano
Abba ne ya zuwa Ummi ido har saida ta kai ƙarshen mgnar, cikin sanyi yace. “Kada ki sake yi mishi fatan haƙƙin Fariyda ya kamashi, kiyi mishi addu'a da fatan shirya, ni kaina yanzu na fara tunanin munyi ganganci na fara nadamar haɗa auren Mahmoud da Fariyda dan na lura bazasu taɓa son juna ba, na sani tunda yace ta kira suna mgnarsa tabbas hakanne tunda itama ba sonshi take ba. Na fara jin a raina bazamu ci nasarar komai ba a haɗa auren”.
Goggo Dada ne ta É—an kalli Ummi dake ta huci tare da cewa.
“Kiyi haƙuri ki cire abin a ranka nasan zai ja mata targaɗen ai shima ya iya ko kin manta Huzaifan Amina ma da ya targaɗe shi ya ja masa, da Haris ɗan Barrister ai kusan sau uku shi ke ja masa”.
Cikin takaici Ummi tace.
"Bazaku gane bane Mahmoud fa kamar baida tausayi”. Cikin sauƙe numfashi Abba yace.
“Ba komai zanyi magna dashi”.

Ahmedabad.
Wani irin kallo mai wuyar fassarawa takeyi masa lokaci da ya ture ta daga jikinsa ya miƙe tsaye ido a rufe yaja dogon tsaki murya a daƙile yace.
“Yesss ai yanzu kin tabbatar min da maitarki ta a fili, taci mutum ido da idone, na lura dama kaɗan kike jiran ki cinyeni ɗanye”.
Kanta ta maida ta kwantar jikin kujerar tare da ci gaba da sauƙe numfashi da baccin.
Kallon takaici ya watsa mata kana ya bar wurin.
Kano
Bayan sallan isha.
Baba Malam ne ya kalli Dr Nasir dake cewa.
“Nima na kirata bata picking call ɗina, yau kwana uku kenan bamuyi mgna ba”.
Mamy tace.
“To Malam ka kira Mahmoud ɗin mana, muji ko wani rashin kunyar tai masa ya ƙwace wayar”.
Baba Malam na gyara zamansa yace.
“Sai gobe da safe zan kirashi in sha Allah”.
Kai Dr Nasir ya jinjina kana yayi musu sallama ya tafi.

Ahmedabad
Tray abincin da yasa aka kawo mata, ya É—an kalla ganin ta ture shi gefe ba tare da taci komai ba.
A fakaice ya ɗan kalleta, wayarsa ya ɗan ja tare da yin rubutu kaɗan ya tura saƙon, sannan yaci gaba da bawa su Zaid indomei da aka dafa musu.
Hannun ta ɗan ɗago a hankali ta ɗan jujjuyashi ta rufe tafin hannunta sai kuma ta buɗesu a hankali, ajiyan zuciya ta sauƙe cikin gamsuwar dai-daita ƙasusuwan sai dai bashi da ƙarfi bazata iya cin abinci da shiba.
Ido ta zuba mishi cikin sanyi da rauni tace. “Bazan iya cin abinci da hannun ba”.
Yana gogewa Zaitoon baki yace.
“Kici da hagu”. Ido na zubda ƙwallan rauni da yunwar tace.
"Bana iya ci da hagu ba”. Baki ya taɓe yace.
“Zauna kar kici”.
Zaid da ya bawa ruwa yasha ne ya koma ya zauna ya fara wasansa da tab É—in haka yasa itama Zaitoon tayi wurinsa.
ÆŠago kansa ya kalleta sosai tayi raunin da ya bayyana a jiki da fuskantar, ga yunwa a fili kana gani.
Miƙewa yayi ya nufi bedroom.
Bathroom ya wuce yayi wanka ya ƙimtsawa cikin tattausar jallabiya.

A tsakiyar parlour ya tsaya ya zuba mata ido, ganinta zaune a ƙasa ta kifa kai jikin kujera, mug ɗin dake gabanta ya kalla da alamun Custard da yasa a dama mata ne aka kawo mata, matsowa yayi kusa, eh ta shanye shi fes tissue dake gefe a ƙalla guda uku wanda ta goge gefen bakinta data ɗan bata ya kalla kana ya ɗan zuba mata ido bisa alamu fa tuni tayi bacci a wurin a zaune, su Zaitoon ya kalla da suke ta wasansu.
Remote ya ɗauka ya sauya channel zuwa na boxing zama yayi ya miƙe sawunsa kan Centre table ɗin ya jingina da jikin kujerar.

Sa'ad ne zaune yasa waya a gaba video call suke yi da Mom É—insa.
“Mom in dai nayi mgna da ita in yayanta ya yarda kawai zanje Ahmedabad ɗin”.
Da sauri tace. “Yes my Son Wannan shine hanya mafi sauƙi, kuma nima ka turo min number yayan nata, zan bawa Abbanka in yadawo suyi mgna dashi, dan yayan nata zaifi ɗaukar mgnar da mahimmancin in yaji maza sun shiga, in ma zasu bamu damane muje wurin iyayensu anan a gama magna duk ba matsala sai Abbanka yaje ya nema maka izinin fara zuwa zancen”.
Cikin gamsuwa da hakan yace.
“Nama tura miki number bari yanzuma in ƙara gwada kiran layin.”
Ya ƙare maganar da katse kiran kayin ya Amin ɗim ya kuma kira.

Parlour sit tamkar babu mai rai a ciki, dan duk sunyi bacci, a yadda yake a zaunen yayi bacci, itama Fariyda a zaunen tayi bacci daga jiran ya fito wanka itama ta shiga, baccin da bata samu tayi shi kwana É—aya da wuni biyu ba ya kwasheta, su Zaid ma daga wasa sukayi baccin sai TV da ake ta boxing, wanda shi ya hanasu jin ringing Alam É—in wayar tasiri a kunnensu.
A hankali ya buɗe idonsa tare da miƙewa tsaye yana mai kallon time jikin ƙasan TV ɗin.
“Yah Salam 4:30 Am. Lokacin sallama yayi ai”.
Kanshi ya ɗan juya ya kalle su Zaid dake kwance a ƙasan carpert ɗin, sai kuma ya ɗan kalleta har lau bacci take mai nauyi sai dai yanzu ta zame ta kwanta a ƙasa kanta na dab dana Zaitoon.
Zaid dake duƙunƙune ya ɗauka ya kaishi kan gadonsu ya dawo ya sunkuya kansu Zaitoon ya ɗaga ya juyawa yayi ciki da ita, a hankali ta sauƙe numfashi tare da ɗan buɗe ido ta ɗan kalleshi sai kuma ta maida kai taci gaba da baccinta.

Sautin karatun Alqur'ani da yake na raka'ar forko ne ya tada ita daga baccin haka yasa ta miƙe tare da jujjuya hannunta.
Kai tsaye bathroom ta nufa.
Wanka tayi mai rai da lfy tare da goge bakinta, bayan ta fitone ta kimtsa cikin tattausan riga mai sulɓi da ƙelli numfashi mai sanyi ta shaƙa tare da lumshe idanunta sabida ni'imtaccen ƙamshin da take bazawa, ga daɗin jikinta da takeji.
A bakin gadon ta zauna tare da fara yin Azkarul Sabah da tasbihanta.
9:12 Am ta kwanta kan gadon da aka gyarashi fes bayan ta tafi da su Zaitoon Dannin area É—insu.
Koda ta dawo a parlour ta barsu wurin Mahmoud.
Kwanciya tayi tana lumshe ido taja duvet É—in ta rufe jikinta har zuwa wuya.

Zaid dake kan cikinsa ya gyarawa kwanciya Zaitoon kuwa kwance take kan 2 seatter da alamu bacci ta fara.
A hankali ya ƙara zame Zaid gefe, zip ɗin rigar jikinsa ya zuge yayi ƙasa dashi, kanshi ya ɗan ɗago tare da sunkuyowa yana leƙa kan nimple ɗinsa da yake ta mishi zogi zut-zut da mamaki yake kallon wurin saboda ganin yadda yayi jazir, iskan bakinsa ya ɗan hura a kan nimple ɗin tare da ƙarasa zuge zip ɗin duka dan ya samu sanyin AC ya ratsashi ko zogin zai bari.
Wayarsa ya ɗaga saƙon da asbitin Dr Imran Patel ya tura masa ta email ya kalla na gayyatar taron da za suyi na Pediatrician Asia baki daya a babban holl ɗin dake cikin hotel ɗin da suke ciki.
Kai ya É—an jinnina saboda tuno mgnar da sukayi jiya na sheida masa aikin Zaid sai nan da kwana uku saboda sakamakon gwaje-gwajen da sukayi da ya nuna musu da sauran haÉ—ewar ciwon wuri É—aya.
Wayar ya maida zai ajiye sai kuma yayi saurin É—ago wayar.
Da sauri ya tashi zaune tare da kwantar da Zaid, kiran Baba Malam da ya kusan katsewar ne ya amsa tare da kai wayar kunne cikin girmamawa da tausasa murya yayi sallama ya É—orawa da gaisuwa.
“Lfy lau Alhamdulillah Mahmoud ya iyalin naka”.
Yana mai yin ƙasa da kai yace.
"Alhamdulillah Malam yasu Mamy”.
Baba Malam yace.
“Duk suna lfy, ya Zaid da jikin nasa yaune aikinko”. Cikin girmamawa
Mahmoud yace.
“A'a Abba sun ɗaga sai ranar Friday da dare za'ayi”.
Baba Malam yace.
“To Allah yasa hakan shi yafi alkhairi ina Mamana tana lfy ko”.
Da sauri yace.
“Tana lfy”. Cikin girma Baba Malam yace.
“To bata waya”. Da sauri ya miƙe tsaye saboda girman dottinjon tare da kamalar rashin masa ƙorafin ana kiranta bata ɗagawa yace.
“To Malam yanzu zan kai mata, tana ciki ina Parlour ne”.
Ya ƙare maganar yana tura ƙofar bedroom ɗin.
Baba Malam yace.
“Eh ba matsala akai mata”.
Sassayan numfashi yaja lokacin daya shiga bedroom É—in.
Bakin gadon ya nufa yana mai ɗan ƙara fidda idonsa saboda babu wadataccen haske a ɗakin.
A hankali ya sunkuyo kan gadon yana faÉ—in.
"Malam bacci takeyi”.
Baba Malam yace.
“Kada ka damu tasheta ina son jin muryarta ne”.
A hankali ya ƙara sunkuyowa kanta tare da ɗan motsa lips ɗinshi a hankali karo na farko a rayuwarsa da yaji ya ambaci sunanta da bai ma gama tantance harufan ba.
“Farriyyha ya kira sunan cikin da sigar da yasa Baba Malam yin shiru tare da ƙara maimaita luggar sunan a zuciyarsa yace Farriyyha kuma. shi kuwa Mahmoud
“Farriyyha”. Ya kuma kiranta a karo na biyu.
Har lau kuma wayar na maƙale a kafaɗarsa ganin ko motsi batayi bane yasashi kuma kiranta a karo na uku *Farriyyha* har lau shiru bata amsa ba bata kuma motsaba sai sassayan numfashi da taja tare da fesa masa a fuskar.
“Tana lfy kuwa Mahmoud”. Baba Malam ya tambaya cikin kaɗuwa.
Da sauri yace.
“Ba komai Malam lafiyarta ƙalau”. Ya ƙare maganar tare da sa hannunsa kan duvet ɗin da ke kan ƙirjinta, yatsunsa biyu yasa ma nuniya da babbar yatsarsa ya kamo duvet ɗin da take rufe dashi, cikin mayen bacci ta buɗe kasalallun idonta ta zuba shi cikin nasa idon da ta gansu ras na Yah Amin ɗinta lumshe idonta tayi tare da kai hannunta kan lips ɗinsa sabida jin yadda ya haɗe
kan caɓɓullenta cikin yatsunsa.........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.