Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 21 of 86

Da sauri suka nufi bakin gate ɗin
Inda Barrister keyin parking a gefe.
Suna isa Mahmoud na fitowa, da sauri Barrister yabi bayansa.
Goggo Dada ne ta taimakawa Ummi da jikinta yake ta karkarwa, ta fito hango Fariyda da tayi a tsaye tamkar an dasatane, ya bata damar fashewa da wani irin maraitaccen kuka mai karya zuciyar duk mai sauraro.

Shi kuwa Mahmoud da sauri yasa hannunsa ya amshi Zaid dake hannun Maman Samira,
Sai kuma ya miƙa hannunsa ɗaya ya amshi Zaitoon dake hannun Samira.
Idanunsa da sukayi masifar ja mai bada tsoro ya rumtse da ƙarfi lokacin da ya haɗe yaran ya rungumesu a ƙirjinsa.
Ahmad kuwa kanshi ya kife a jikin motar tare da sakin wani sabon kuka.

Cikin tsananin rauni gigita da tashin hankali mai ruɗarwa Ummi ta nufi inda Fariyda ke tsaye tana faɗin.
“Na rasa ɗana Fariyda kin rasa mijinki, Yaranki zasu rayu cikin maraicin uba Aminullah na ya rasu Mahmoud na ya rasa ɗan uwa.”

Wani irin zazzafan numfashi Fariyda ta fizgo da ƙarfi tare da rumtse idonta da sukayi masifar fitowa waje tamkar zasu faɗo.
Da sauri Goggo Dada tayi kan Fariyda data yaken jiki ta faɗi.
“innalillahi wa innalillahi rajiun, ta suma fa”.
Jin abinda Goggo Dada tace ne, yasa Maman Samira shiga part ɗin Ummi da gudu ruwan sanyi ta ɗauko.
Amsa Goggo Dada tayi ta fara yayyafa mata, Amman ina shiru bata motsa ba.

Barrister ne yace.
“Ku kamata ku kaita ciki”.
Jin haka ne yasa Maman Samira da Samira suka ɗagata sukayi parlour Ummi.

A parlour suka samu Mahmoud zaune rungume dasu Zaitoon.

Gaban Fariyda da suka kwantar bisa 3 sitter Ummieta zauna tare da kife kanta gefen kan Fariyda.
Ahmad da Barrister a tare suka shigo.

Sai kuma akaci gaba da yayyafa mata ruwan.
Cikin ikon Allah ta farfaɗo.
Ido ta zuwa Ahmad da Barrister dake tsaye gefe, sai kuma ta kalli Ummi murya can ƙasa tace.
“Ummi da gaske Yah Amin ya ras?”.
Sai ta kuma sume wa.
Yah Salam shine Abinda Goggo Dada ta faɗa tana zubda ƙwalla.
Ruwan aka kuma fesa mata a karo na uku aka samu ta kuma farfaɗowa da wani irin gigitaccen kuka, kukan tan ne yasa Ummi fashewa da wani sabon kuka.
Kukan Samira da mamanta dasu Ummi da Goggo Dada ne, yasa Barrister zama tare da farayi musu nasiha tare da tausar zuƙatansu yana mai jaddada musu kalmar innalillahi wa innalillahi rajiun.

Shi kuwa Mahmoud tun da ya riƙe addu'ar Allahummma gafirlahu warahamhu, bai kuma faɗin ko wacce kalmaba bayan ita, ji yake a rashi dama shine yake suman da yaji daɗi , dan ji yake suman yafi mishi sauƙi akan yanayin azabtar da zuciyarsa da brain ɗinsa da yakeji tamkar ya zauce.

A can harabar gidan kuwa Baba idi ne ya zame ya zauna ƙasa dirsham tamkar wanda baida laka a jikinsa, tsoron Allah da imani da firgicine duk suka haɗe masa lokaci ɗaya shiyasa ko gate ɗin bai samu ya rufe ba.
Ganin mota ya tinkaro shigowa gidan ne, ya fara yunƙurin tashi tsaye, Amman sai ji yayi ya gaza, so ya yake ya tashi ya bawa motar hanyar shigowa Amman ya kasa miƙewa, hakan ne ya sashi fara rarrafe ya samu ya matsa gefe. Dr
Nasir yayan Fariyda ne dake jan motar yayinda Baba Malam ke gefe, Mamynsu da Aunty Amarya tare da Hajja Inna wacce jiya tazo daga Gembu membila a baya.
Suna yin parking Baba Malam ya fito.
Yana kallon Baba idi da ya samu ya miƙe tsaye.
Kai Baba Malam ɗin ya sunkuyar hango motar Abba dake shigowa da ta Baba Lawan a baya.

A hankali baba idi ya maida gata ɗin zai rufe, sai kuma yayi saurin tsayawa ganin Motar Daddy su Hafiz da Amina gefe sai su Hafiz a baya.

Hannu Abba ya miƙawa Baba Malam yana mai kallon motar su Amina, da sauri ta fito cikin motar ta nufi mahaifin nata.

Su Mamy kuwa tuni sunyi cikin gidan.

Da sauri Bappa Lawan ya kamo hannun Amina tare da cewa.
“Mamana tafi a hankali”.
Cikin sauri ta kalli ƙanin Mahafin m'nata murya a hargitse tace.
“Bappa meke faruwa ne? Daddyn Hafiz yace, muzo gida yanzu kuma naga gidan a cike, Bappa meke faruwa ne, ina Ummi na? Ina Yah Amin?”
Sai kuma tayi maza ta juya ta kalli Abba da sauri ta isa wurinsa ganin Bappa Lawan ɗin yayi ƙasa da kai yaƙi ce mata komai.
“Abba kuyi min mgna ma, ina Mahmoud?”.
Cikin sanyi Abba ya ɗan kalleta a fizge a hankali yace.
“Amina ki shiga cikin duk suna ciki”.
Jin haka ne yasa ta fara bin idonsu da kallo.
Baba Malam ne yayi saurin yin ƙasa da kansa domin shi ya gaza danne zuciyarsa rauninsa yayi ƙarfin da bazai iya hana idonshi zubda ƙwalla ba, Dr Nasir ta kalla yayan Fariyda wanda yake faɗin.
“Malam mu isa ciki wurin Fariyda”.
Jin haka ne kuma yasa tayi saurin cewa.
“innalillahi me ya samu Aunty Fariyda”.
Sai kuma tayi maza ta juya da gudu ta nufi part ɗin Umminta.
Da sauri Hafiza ta mara mata baya.

Dai-dai lokacin kuma. Fariyda ta hango Mahaifiyarta da step mom ɗin nata da kuma kakarta mahaifiyar uwa,
Ido ta rumtse da ƙarfi tare da miƙawa mahaifiyar tata hannu, cikin wata iriyar murya mafi ƙololiwar rauni tace.
“Mamy Yah Amin dina ya rasu ya barni, Yah zanyi da rain”.
Dai-dai lokacin Amina kuwa ta kutso kai cikin falon kalmar Yah Amin dina Yah rasu ya barni ne sukayi welcoming ɗinta.

A can wajen kuwa Bappa Lawan ne ya bawa Baba idi umarnin ya shinfiɗa taburmai a babban barandar masallacin dake harabar gidan.

Sai kuma ya juyo ya kalli Baba Malam dake cewa.
“Ina gawar take?”.
Da sauri Hafiz ya zazzaro ido waje cikin ɗaga murya yace.
“Abba gawa kuwa? Gawar waye? Innalillahi wa innalillahi rajiun”.
Da sauri Mahaifinsa ya kama hannunsa cikin tausaya wa yace.
“Kayi haƙuri Hafiz Ubangijin daya bamu Aminullah ya fimu sonshi kuma bamu da hurumin cewa ina dalilin ɗaukarsa da yayi”.
Ya salam shine Abinda Abba ya faɗa ganin wani irin kuka mai birkitaccen sauti da Hafiz ɗin yakeyi.
Da sauri Daddynsa ya jawosa jikinsa.
Shi kuwa Abba ji yake yi bazai iya hana kowa kukaba, shima da zai samu kukan zai yi Amman ina hakan bai samu ba.

A can parlour kuwa.
Wani irin runguma mai tafe da gigita Fariyda tayiwa Mahmoud da su Zaitoon duk ta haɗa su a ƙirjinta, kuka mai raunataccen sauti ta saki tamkar ranta zai fita.

Yayinda Fariyda kuwa tuni ta kuma sume wa.
Shi kuwa Mahmoud ido ya zuba wa yar uwar tasa ya kasa ce mata ko ƙala sai.
“Allahumma gafirlahu warahamhu”.
Da yake ta mai maitawa.
Wanda tunda yaji rasuwar bai kuma wata kalma bayan taba.
Ummi ce ta kalli Mamyn Fariyda cikin rawan murya tace.
“Suma tayi fa”.
Jin haka ne yasa Aunty Amarya saurin miƙewa ta fita, ta kira Dr Nasir ɗin da ya fita.

A nan wajen kuwa tuni Baba idi ya shinfiɗa taburmai.
Bappa Lawan ne ya kalli Baba Malam tare da cewa.
“Gawar tana nan masallacin.
Yanzu zamuje ayiwa gawar sutura.
In sha Allah in anyi sallan azahar za'a kashi makwancinsa”.
Cikin sanyi ido na zubda ƙwalla yace.
“To muje ayi mishi sutura.
Sai kuma ya ƙare maganar yana kallon Aunty Amarya dake sanarwa Nasir Fariyda ta suma fa.
Da sauri yabi bayanta...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.