Sakar Makafi Littafi Na 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 49 of 86
*Littafin SAƘAR MAKAFI na kuɗin 1k ne 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo Evidence ɗin ki ta nan 09097853276 mutanen Niger 1000cfa ne +22790440050 Hannatou zakuyiwa magna*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 20
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Ƙarfe shida da kwata ya shigo gidan daga Masallaci, tun daga baki bakin gate ɗin ya fara jiyo kukan Zaid tamkar zai shiɗe, da sassarfa ya ƙarasa cikin parlour. Ummi na riƙe dashi tana hura mai kunnen Amman a banza, Goggo Dada da ke zaune cikin sauri tace.
“Yauwa kawo shi mu tafi asbitin”.
Da sauri ta bata shi suka fita.
Mahmoud ɗin na cewa Hafiz da ke ƙoƙarin shiga ya ɗauko Zaitoon.
Ummi da Zaitoon ɗin ke riƙe da yatsarta suna tafiya ne tace.
“A'a ku barta kawai”.
Da sauri ya buɗewa Goggo Dada front seat tana shiga ya maida marfin ya rufe kana ya shiga mazauninsa, tare da figar motar suka tafi.
Ummi kuwa kitchen ta shiga ita da Maman Samira da ta shigo yanzu.
Ƙarfe takwas dai-dai Salim ya tashi daga gaban mahafin nasa cike da farin ciki ya fita dan tafiya gidan Abban.
Yana fita Mama ta kalli Bappa Lawan ɗin cikin tunasarwa da tabbatarwa da kuma ƙarfafawa tace.
“Naji dai kayi shiru batun Jidda da Mahmoud kaga yanzu tunda Salim ya samu wacce yakeso har kace yaje ya isar da mgna a wurin Abbansu, ya kamata ace ka samu ɗan uwanka da batun Mahmoud da Jidda, ko dan mu samu nitsuwar Jidda ma tunda taƙi kula kowa tace ita ɗan uwanta takeso.”.
Shiru yayi ya zuba mata ido cikin ƙiyasta ta sameshi da magnar Jidda da Mahmoud yafi sau biyar, ganin tana zubda ƙwallan tausayin yarta gami da faɗin.
“Wallahi da kai Jidda ke sawa a gaba tana maka kukan da take min da ka tausaya mata, tun ina ƙin kulata har na gaji na aminta da burinta ko dan gudun kada ta cutu”.
Kai ya gyaɗa mata alamar to..............
Ƙarfe tara dai-dai ta farka daga baccin daya saceta bisa sallayan. A firgice ta miƙe jin kamar kukan Zaid ɗin da sauri ta fito parlour.
Sai kuma ta sauƙo Downstairs ɗin da sassarfa, cikin hanzarin ta buɗe ƙofar parlour.
Murmushi tayi ganinsa zaune gaban Goggo Dada da tarin kwalaɓen magungunan, gefenta ta zauna tace.
“Har kunje asibitin ne”.
Kai ta gyaɗa mata da cewa gashi kuwa har maganin ya fara aiki.
Hannu ta miƙa masa.
“Zaid zo”.
Murmushi tayi ganin ya miƙe tsaye kan cinyarta ya zauna ya mai manna kansa a ƙirjinta.
Sai kuma ta kalli Ummi data shigo Zaitoon na biye da ita a baya tace.
“Har kin tashi”. Kai ta gyaɗa tace.
“Eh ashe har sunje asibitin, wai menene yake damunsa”.
Goggo Dada data miƙe kan 3 sitter ne tace.
“To sun dai ce akwai ciwon ciki, kuma sunce bayan kwana uku mu koma suyi masa gojin jijiya”.
Da sauri tace.
“Menene kuma gwajin jiniya”.
Goggo Dada tace.
“Sunce wai menene ma sunan abun wai alamun hainiya ne, dama wasu haifarsu akeyi dashi sai anyi tiyata an cire musu, amman dai basu tabbatar ba sai an gama gwaje-gwajen nasu”.
Cikin sanyi tace.
“Allah yasa ba shi bane”.
Amin sukace dukansu.
Ummi tace.
“Kawoshi kici abinci. Samira kawo mata abinci”.
Karɓansa tayi ta tafi tafiya parlour Abba dashi.
Samira data ajiye mata tray abin karin tane ta kalla tace.
“Wai dan Allah ni kam Samira ke zaman me kikeyi ne a gida, har yau baki ci gaba da karatunki ba tunda kika gama Secondary school, shima a makare kika gamashi tunda gashi Hafiz da Hafiza yanzu har sun tafi level 3 ke kuma sai bana kika gama Secondary ɗin”.
Goggo Dada tace.
“Tab shima da ya aka samu Babanta ya yarda aka sakata, saida Aminullah ya dage da naci ya haɗasa da Abbansu ma yayi masa magna, saida sukayi shekaru uku suna binsa kafin ya yarda, ai da itama tare take dasu Hafiz, to yanzu kuma yace ba wani ci gaba karatun ya isa haka sai dai ta fidda miji ayi mata aure, in Kuma bata fidda ba zai haɗata da ɗan ƙanwarsa na can Agadaz”.
Numfashi mai sanyi ta fesar tare da kallon Samira da tayi ƙasa da kanta cikin sanyi tace.
“Aunty Fariyda nima ina son karatu Amman Babana yaƙi”.
Tana gyarawa Zaitoon ribbons ɗin kanta da yake sulewa sabida santsin gashinta tace.
“Ba damuwa in sha Allah zai yarda kici gaba, ke dai muyi ta addu'a, kuma zan mishi magana a madadin Yah Amin wata ƙil in munyi sa'a sai ya yarda”.
Cikin sauri Goggo Dada tace.
“Kin kuwa kawo shawarafa Allah yasa haka”. Amin sukace.
Washe gari da safe. Salim ne zaune gaban Abba cikin alamun kunya yace.
“Abba dama Baba ne yace in Zo in sameka”. Sai kuma yayi shiru cikin nazari Abba yace.
“Aha ina jinka”. Ɗan sunyi mgnar da ɗan uwan nasa so yake yaji a bakin Salim din me yasa a turoshi.
Mahmoud dake gefensa ya kalla cikin irin salon nan na ka tayani mana, hararansa yayi tya ci gaba da danna wayarsa.
“Eh Abba dama akwai wata yarinya ce da na ganta a auren Mahmoud da Fariyda”.
Shiru yayi saboda wani irin kallo da Mahmoud ɗin ya watsa masa akan me zai wani ce aurensa dana Fariyda.
“Me sunanta yar waye ce”.
Yana gyara zama yace.
“Na nunawa Fariyda hotonta tace min sunanta Salma kuma yar ƙanin Malam ce Uncle Sani”. Murmushi mai cike da jin dadi Abba yayi kana yace.
“Ba matsala, amman kayi mgna da itane”.
Kai ya ɗan sosa yace.
“A'a ina jira dai sai in manya sunyi mgna in an bani izinin fara zuwa, dan ko mgna ma ban mataba”.
Abba yace.
“Kayi abinda ya dace Muhammad Salim Allah yayi maka al'barka, duk yadda nayi dasu zaka jini”.
Cikin jin daɗi yace.
“To Abba Allah ya ƙara girma”.
Amin Mahmoud yace tare da riga Salim ɗin miƙewa sai kuma ya koma ya zauna jin Abba na cewa.
“Ya batun tafiyar kane kam Mahmoud”.
Kai a sunkuye yace.
“Gobe da safe ai zan wuce Lagos”.
Abba yace “To Allah ya kai mu ba kaika lfy”.
Amin yace suka fita a tare.
Da yamma gab magrib ya shigo parlour da alama al'wala yayi.
“Goggo Dada ya jikin da sauƙi ko bai ƙara kukan bako”.
Tana bashi Custard tace.
“Ai lfy Lau sai ci, wata ƙil dama ciwon ke hanasa ci sosai”.
Kansa ya shafa kana ya fita.
Washe gari da safe, tsaye yake cikin Black jeans sai black blue shirt Salim dake gefensa ne yace.
“Lokacinfa na tafiya”.
Hafiz ne da ke riƙe da boronsa ya juya ya fita yana faɗin.
Uncle Salim ni zan jamu.
Ummi dake jera masa addu'a ne yake ta amsawa da amin bayan ya gama kwasar na Abba.
Rungume su Zaitoon ɗin yayi yana kiss kuma tunansu”.
Goggo Dada kada ku manta da komawa asbiti ni zanyi mgna da Dr Fadil, my Happiness Allah ya baka lfy”.
Dariya suke su duka biyu da kyar Ummi ta mashesu.
9:00 am jirginsu ya ɗaga Kano to Lagos.
Sai biyar na yamma kuwa suka tashi Lagos to Italy.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.